CRI Hausa" />

A game da yadda Amurka ta kare aniyarta ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong a kwanakin baya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin madam Hua Chunying ta sanar a yau Litinin cewa, Sin za ta kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka don mayar da martani.

Madam Hua ta ce, abun da Amurka ta yi ya sabawa dokoki, gami da ka’idojin kasa da kasa, wanda kuma ya zama shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin. A don haka, gwamnatin Sin ta yanke shawarar daukar matakan sanyawa Amurka takunkumi, inda tun daga yau 2 ga wata, Sin za ta dakatar da duba rokon da jiragen yakin sojan Amurka suke gabatarwa na samun hutu a Hong Kong, da garkama takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka da ba na gwamnati ba, wadanda suka aikata munanan laifuka a rikicin Hong Kong, ciki hadda kungiyoyin NED, da NDI, da IRI, da HRW, da Freedom House da sauransu.

Madam Hua ta jaddada cewa, Sin ta bukaci Amurka ta gyara kuskuren da ta aikata, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar. Har wa yau, Sin za ta yi la’akari da halin da ake ciki, don kara daukar matakan da suka wajaba, na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da bunkasuwa a yankin Hong Kong, da kare ikon kasar na tsaro, gami da ci gabanta.

(Mai Fassara: Murtala Zhang, ma’aikacin sashin Hausa na CRI)

Exit mobile version