A yau, an bude dandalin tattaunawa kan inganta tsarin jagorancin duniya na shekarar 2026, a sabon yanki na Xiong’an na kasar Sin. Taken dandalin kuma shi ne “Sake samar da kwarin gwiwa da damar hadin gwiwa: Manyan sauye-sauyen da ake fuskanta da kuma batun inganta tsarin jagorancin duniya.”
Kafin haka, a watan Satumban bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da babbar shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO). Daga baya, a watan Mayu na bana, kasar Sin ta kira taron “Kungiyar abokai da suka amince da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya” a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York na kasar Amurka, kafin daga bisani a watan Yunin da ya gabata, kasar ta fitar da takardar bayani don bayyana ra’ayinta a fannin inganta tsarin jagorancin duniya.
Shin ko me ya sa kasar Sin ke mai da cikakken hankali kan batun inganta tsarin jagorancin duniya? Dalili shi ne tsarin jagorancin duniya yana cikin wani yanayi na matukar bukatar samun gyara. A duniyarmu, yadda dimbin kasashe masu tasowa ke samun ci gaba cikin sauri ya riga ya sauya fasalin tattalin arzikin duniya, amma har yanzu tsarin raba wakilci da ikon fada-a-ji ta fuskar jagorancin duniya bai canza sosai ba. A bisa wannan yanayi ne, gibin jagoranci yake bayyana a sabbin fannoni, kamarsu tinkarar sauyin yanayin duniya, da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da harkoki masu alaka da yanar gizo ta Intanet, da tsaron sararin samaniya, yayin da manufar damawa da bangarori daban-daban ke fama da mawuyacin hali, sakamakon yadda wasu kasashe ke yawan daukar matakan kashin kai da nuna salon daukar matsaya biyu.
To, ko ta yaya za a iya inganta jagorancin duniya? Dangane da wannan tambaya, amsar da kasar Sin ta gabatar ita ce babbar shawarar inganta tsarin jagorancin duniya, wadda manyan ka’idojinta su ne “Tabbatar da daidaiton mabambantan kasashe a fannin ikon mulkin kansu, da bin dokokin kasa da kasa, da aiwatar da manufar cudanyar sassa daban daban, da dora muhimmancin mutane a gaba da komai, da kuma kokarin daukar takamaiman matakai.” Wannan shawara tana da nufin sanya tsarin jagorancin duniya ya kara zama mai adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa mabambantan kasashe za su dauki nauyin tsarawa da kare ka’idojin duniya a hadin gwiwarsu. Tun lokacin da aka gabatar da shawarar, ta samu goyon baya daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su kusan 160. Wannan ya nuna cewa, shawarar nan da kasar Sin ta gabatar za ta iya biyan bukatar galibin kasashe, musamman ma wadanda ke kan hanyar tasowa.
A kan batun jagorancin duniya, kasar Sin da kasashen Afirka suna da matsaya iri daya. Saboda Sin da Afirka dukkansu sun yi kira da a yi wa Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin sulhu dake karkashin majalisar garambawul, don daidaita yanayin rashin adalci da kasashen Afirka ke fuskanta sakamakon wasu batutuwan tarihi, da kuma kara wakilcin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, a Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin sulhunta. Kana a fannin huldar kasa da kasa, Sin da Afirka sun nuna cikakken goyon baya ga ka‘idojin dangantakar kasa da kasa, wadanda aka tsara bisa tushen kundin Majalisar Dinkin Duniya, kuma suna adawa da mulkin danniya, da yunkurin raba kasashe zuwa rukunoni daban daban bisa ra’ayin mulki, gami da ta da rikici tsakanin rukunonin. A fannin tattalin arziki, Sin da Afirka suna goyon bayan dunkulewar duniya a fannin tattalin arziki a kokarin amfanin kowa, tare da bukatar yin gyare-gyare a hukumomin hada-hadar kudi na duniya, kamar su Bankin Duniya, da Asusun ba da lamuni na duniya, don habaka wakilcin kasashe masu tasowa a cikin wadannan hukumomi, da ba su ikon bayyana ra’ayoyinsu.
Dandalin tattaunawa kan inganta tsarin jagorancin duniya da aka kira a wannan karo ya kunshi kananan tarukan tattaunawa guda biyar, wadanda ke mai da hankali kan wasu batutuwa masu nasaba da jagorancin duniya da suka fi janyo hankalin mutanen duniya, wato su: “Aiwatar da manufar cudanyar sassa daban daban, da kare tsarin duniya mai daukaka matsayin Majalisar Dinkin Duniya”, da “Yayata ra’ayin yin hadin gwiwa gami da amfanar da juna, da neman cimma ra’ayi daya don kara saurin ci gaban tattalin arziki”, da “Tabbatar da daidaito da fa‘idar juna, da zurfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da na hada-hadar kudi”, da “Inganta jagoranci a wasu sabbin fannoni, kamarsu fasahar AI, da yanar gizo ko Intanet, da kuma sararin samaniya,” da kuma “Inganta musayar al’adu, don samar da damar yarda da juna da koyi da juna”. Babu shakka, kasar Sin da kasashen Afirka za su iya amfani da damar da wannan dandalin ya bayar don mai da burin da aka sanya ya zama tsarin hadin gwiwa, da daukar matakai bisa matsaya daya da aka cimma, tare da kokarin ba da gudummawa ga yunkurin gina tsarin jagorancin duniya mai adalci da gaskiya. (Bello Wang)













