Al’ummar ƙauyen Birnin Tudu da ke Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara sun ce sun kashe ’yan bindiga sama da 30 cikin kwanaki uku da suka yi suna fafatawa bayan wasu ’yan bindiga sun kai musu hari.
Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun zo ne a kan babura ranar Talata, inda suka riƙa harbe-harbe, shiga shaguna ta ƙarfi tare da satar kayayyaki.
An ce an kashe mutane uku daga cikin mazauna ƙauyen, yayin da wasu suka ji raunuka.
Al’ummar sun ce sun yi artabu da maharan har suka samu nasarar korar su.
Sai dai ’yan bindigar sun yi nasarar sace shanu daga wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su.
Kwamandan ’yan sa-kai na ƙauyen, Bello Abubakar, ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su samar musu da ƙarin jami’an tsaro, makamai da motar yaƙi domin kare ƙauyen daga harin ramuwar gayya.
Wani tsohon jami’in soja, Bello Muhammad Bakyasuwa Maradun, shi ma ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro a yankin.
Rundunar ’yansandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta ƙara matakan tsaro domin kare rayukan mazauna yankin.












