‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

‘Yan bindiga sun kashe ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Shinkafi a majalisar dokokin jihar Zamfar.

An kashe Muhammad Ahmad J. ne a daren Laraba a kan hanyarsa ta zuwa Kano bayan kammala taron shigar Gwamna Bello Matawalle jamiyyar APC da ’yan Majalisar Dokokin Jihar.

Babban Daraktan yada labarai na majalisar dokokin jihar Zamfara Mustapha Jafaru ya tabbatar da faruwar kisan ga manema labarai a Gusau.

Hon J.Ahmad kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.

Exit mobile version