Connect with us

RA'AYINMU

Batun Gyaran Titunan Nijeriya

Published

on


A makon da ya gabata, aka fara tataburza kan wani batu da ya kunna kai na karin farashin man fetur da Majalisar Dattawa ke yunkurin yi; lamarin da ya jefa al’ummar kasar nan, musamman talakawa cikin zulumi da fargabar halin da za su iya tsintar kansu matukar aka cimma nasarar kara farashin litar man daga naira 145 zuwa 150.

Ba batun kara kudin alkalaminmu zai yi magana a kai ba – tun da Majalisar Dattawa ta fito fili karara tare da shelanta cewar an yi mata mummunar fahimta, kuma an murguda labarin yadda ‘yan kasa suka rika kallon sa a bai-bai – illa iyaka irin tsoro da fargabar da suka cika zukatan ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da maganar ta kunno kai.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, mai wakiltar Kano ta Kudu, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Titunan Nijeriya a Majalisar Dattawa, ya gabatar da kudurin yin doka kan Tsarin Farfado da titunan Nijeriya da yanzu haka suke cikin mummunan yanayi, wanda a dalilin haka kullum cikin kashe matafiya suke – talakawa wadanda ba za su iya biyan kudin jirgi ba.

Kabiru Gaya, wanda ya zagaya kusan dukkanin titunan da ke fadin Tarayya kasar nan, ya kuma ganewa idonsa halin da suke ciki, saboda haka ya nemi masu ruwa da tsaki a harkar Sufuri da su bullo da wata hanya wadda za ta bawa Gwamnati damar gyaran wadannan titununa cikin sauki – shi ya sa ya nemi a yi doka a Majalisa ta musamman da za ta rika tattauna halin da manyan hanyoyinmu suke ciki.

A irin wannan Kudiri da ya gabatar ne, Kwamitinsa ya gano akwai Naira biyar da ake cirewa (rara) daga kowane farashin lita guda tun da dadewa, domin hatta lokacin da farashin yake 87, akwai hakki da ya rataya a wuyan Hukumar Kula da Farashin Man Fetur ta kasa (PPPRA), na ta rika cire naira biyar tana mika shi ga Hukumar Gyaran Manyan Titunan Nijeriya (FERMA). Sai dai ga dukkan alamu, wadancan kudade ba a sanya su a asusun da ya dace, domin kwamitin Sanata Kabiru Gaya ya gano cewar akalla Naira Bilyan 160 ne PPPRA ba ta sanya a asusun FERMA ba.

A halin da ake ciki, hakika titunan kasar nan suna bukatar kyakkyawar kulawa. Akwai kunya matuka game da yanayin tsarin sufuri a Nijeriya. Manyan titunanmu da suka hada da Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma, Arewa Ta Tsakiya duk a lalace suke, titi daya ne tal, Abuja-Kaduna ya ci arzikin gyaran faci-faci sakamakon kwaskwarimar da aka yi wa Filin Jirgi na Abuja, amma daga Kaduna zuwa Kano, duk wanda ya kama hanya ransa idan ya yi dubu sai ya baci. Haka lamarin yake a manyan titunan da suka hada Arewa da Kudu, matafiya kullum cikin zulumin bin hanya suke saboda rashin kyawu. Duk da cewa kasar nan Allah ya yi mata arzikin da za ta iya mayar da titunanta tamkar na Dubai ko Saudiyya ba tare da an rika karbar naira biyar daga farashin litar mai ba.

Gwamnati mai ci a yanzu, watau ta APC, karkashin Shugabancin Muhammadu Buhari ta taka rawar ganin matuka wajen kwato makudan kudaden da wasu tsiraru suke kwashe (a yaki da cin hanci da rashawa), ire-iren wadannan kudade suna nan jibge, babu wanda ya san halin da suke ciki. Wasu ma marayu ne domin har yanzu ba a gama gano hakikanin mamallakansu ba, me zai hana a yi amfani da su wajen ci gaban kasa maimakon ajiye su a lalitar banza?

An dade ana gafara sa, amma ‘yan Nijreriya ba su hango kaho ba. A daidai wannan lokacin, mutane suna shan wahala, talauci da fatara kullum karuwa suke yi, mai ci sau uku a rana ya dawo sau biyu, wani ma da kyar yake samun ci sau daya.

Gyaran tituna abu ne mai kyau, amma za a iya yin sa ba tare da an tsauwalawa talakawa ba, Nijeriya kasa ce ma arziki, da za ta iya yin dukkan abinda ta ga dama matukar tana da bukatar hakan.

Matakin da Sanatoci suka dauka na cewar ba kudin man za a kara ba lallai abin yabawa ne, domin kara kudin man fetur ka iya zama silar karuwar farashin kayayyakin harkokin yau da kullum. Muna sane da cewar tun daga lokacin da aka janye tallafin man fetur, wanda ya janyo farashinsa karuwa da kashi 47%, dukkanin kayan amfanin yau da kullum sai da farashinsu ya ninka, domin man fetur na cikin manyan sinadaren da tashin farashinsu babbar illa ce ga rayuwar talaka.

Idan har da gaske gyaran titunan ake so a yi, akwai hanyoyi da yawa wadanda suka dace ba tare da an tsauwalawa talakawa ba, domin mun ga yadda aka gyara titin Abuja zuwa Kaduna cikin kwana 50 kacal, ba domin talaka ba, sai don kusoshin gwamnati da gyaran filin jirgin Abuja ya hana jiragensu sauka a Birnin Tarayya sai a Kaduna.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI