Connect with us

RAHOTANNI

RAHOTO: Ko A Nan Gwamnatin Buhari Ta Tsaya, Ta Samu Nasara – Ambasada Bature

Published

on


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Dawo da martabar tattalin arzikin kasar nan ne kadai zai iya dawo da martabar kasar nan. Jigo a jam’iyyar APC, Ambasada James Bature ne ya fadi hakan a tattaunawarsa da manema labaru a Minna kan cikar Gwamnatin Shugaba Buhari shekaru biyu a kan karagar mulki.

Sai dai kuma James Bature ya ce yadda hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ke aiki akwai bukatar gyara a kai, “lallai yadda ake aiki dole ne ‘yan adawa su koka akan cewar su kadai ake yiwa bita da kulli, amma da za a gyara duk wani tsohon shugaba ko Gwamna a binciki ayyukan da ya yi a baya da yadda ya kashe kudaden kasa da jama’a za su kara amincewa wannan aikin da gaskiya ake yinsa.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya ta ka rawar gani sosai wajen dakile zagon kasar da ake yiwa kasar nan, amma akwai bukatar hukumomin da aka dorawa alhakin kwato hakkokan jama’a a hannun shugabanni da su tabbatar sun yi aiki yadda ya kamata dan kauce wa zarge-zargen jama’a”.

“Wannan aikin bai kamata ya tsaya a kan shugabannin da suka rike da mulki ba, har shugabannin da suke jagorantar mutane a bangaren addini akwai rawar da suke takawa, ya kamata su ma a ja masu layi kuma duk wanda aka samu da laifin zarmiya da zagon kasa a fito da shi a hukunta shi, domin rikicin addini da tsanar da ake cusawa a tsakanin mabiya addini bai rasa nasaba da anfanin da suke samu idan hakan ya faru wanda hakan ma na daya daga cikin hanyoyin da ake bi wajen zama bisa kujerar jagoranci na din-din-din”.

Wakazalika, Ambasada James ya jawo hankalin ‘Yan Nijeriya da su kara jurewa da hakuri da yadda abubuwa ke tafiya, domin a cewarsa “ba a gyara rana daya, barna shi ke zuwa lokaci daya amma gyara sai an bi a hankali. Bai yiwu wa a dade ana barna sannan a yi tunanin gyara lokaci daya, shugabannin da suka

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI