Connect with us

KUNGIYOYI

Kungiyoyi Da Kulob-Kulob: Bunkasa Kasuwanci: ‘Yan Kasuwar ‘SCC Jere Junction’ Sun Bayyana Kudurinsu

Published

on


Kungiyar ‘Yan Kasuwar Mahadar Hanyar Abuja da Jere (SCC Junction) ta bayyana kudurinta na kara habaka hada-hadar kasuwancin kayan miya da na marmari a kasuwar domin jin dadin masu saye.

A cewar kungiyar, kasancewar kasuwar ta fi kusa da Babban Birnin Tarayya Abuja a kan daukacin yankunan da Jihar Kaduna ta yi iyaka da babban birnin, akwai damammaki birjik na samun budewar kofofin arziki da Jihar Kaduna za ta amfana da su idan aka bunkasa kasuwar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Musa Jere ya yi tsokaci kan harkokin kasuwar da ci gabanta.

“Kasuwar ta kunshi sashen masu sayar da kayan gwari irin su dankalin turawa, fruits (kayan marmari) su kankana, lemo da sauran su. Akwai kuma masu sayar da kaji wanda idan mutum ya saya a take za a gyara masa kuma ba tare da ha’incin komai ba, mun yi fice a kan haka. Muna kasuwanci ta yadda kowa da ka gani a kasuwar yana gudanar da harkokin kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali da lumana sannan muna samun ci gaba daidai gwargwado mun gode wa Allah. Ta ko ina muna samun baki ‘yan kasuwa da ke kafa rumfuna kuma su ma daga baya sai su ja ‘yan’uwansu su zo saboda sun ji dadin kasuwanci a nan.

“Masu sayen kaya a wurinmu kuma muna kara yi musu lale marhabin, muna tabbatar musu da cewa za su ci gaba da samun kayan abincin da suke so masu inganci cikin rahusa”.

Sakataren Kungiyar, Alhaji Ja’afar Adamu Jere, ya yi tsokaci kan kokarin da kungiyarsu ta ‘Yan Kasuwar SCC Junction ke yi na kiyaye hakkokin masu sayayya a kasuwar.

“Kasuwa ce da aka fara sayar da kayan miya da doya da kaji, daga bisani sai masu sayar da shanu suka zo suka bude sashinsu. Akwai kuma masu kawo nono mai kyau da manshanu da abincin sayarwa, Alhamdulillahi ci gaba na kara samuwa ta kowane sashe. Muna fata Allah ya kara bunkasa mana ita. Domin ta hakan gwamnati musamman ta Jihar Kaduna za ta amfana da kudin shiga musamman idan aka kawo mana abubuwa na ci gaban kasuwanci a zamanance.

“Mu ‘yan kasuwan da ke kasuwanci a wannan kasuwar, mutane ne masu son zaman lafiya da kiyaye martabar manya da kananan mutane. Muna jinjina wa Gwamna Malam Nasir el-Rufa’i saboda tsayuwar dakar da ya yi na tabbatar da tsaro a wannan hanya ta Jere zuwa Abuja. Jami’an tsaro na yin bakin kokarinsu a duk lokacin da wani abu ya taso.

“Babban abin da muka sa a gaba shi ne me za mu yi a wannan kasuwar don mu samu ci gaba, ita ma karamar hukumarmu ta Kagarko haka, sannan jiharmu ta Kaduna ita ma ta samu har ma Gwamnatin Tarayya baki daya”.

Sakataren ya kuma yi roko na musamman ga Gwamna Malam Nasir el-Rufa’i ya kawo wa kasuwar dauki kamar yadda yake yi wa kasuwanni daban-daban a sassan Jihar Kaduna.

“Muna kira ga maigirma Gwamna Malam Nasir el-Rufa’i ya kawo mana ci gaban da muke jin labarin yana samar wa a kasuwanni don bunkasa kasuwanci. Sannan gwamnatinsa ta agaza mana da jari, yanayin tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi ya sa wasu sun rasa jarinsu. Wasu da dama a da suna sana’a a kasuwar nan, suna samun na rufin asiri, su ciyar da iyalansu da ‘yan’uwansu ba tare da sun dogara da kowa ba amma yanzu abin ya gagara, ba su da jari. Don Allah gwamnati ta dube mu da idon rahama kan wannan.

“Garinmu na Jere gari ne mai daraja da kima da mutunci tun a tarihin kafuwarsa, kuma a duk kewayen nan babu garin da ya kai Jere ci gaba ta kowane bangare musamman kasuwanci da noma. Akwai manya-manyan mutanen da a baya sunansu kawai muke ji amma yanzu sun zo sun bude gonakai a Jere suna noman rani da damina cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar da wasu tsofaffin gwamnoni da ministoci. Wannan cigaba ne da aka samu a yankin Jere musamman ga matasanmu da ke samun aiki. Wurin da muke da nakasu shi ne yadda za a bunkasa wannan kasuwa ya zama abin da ake nomawa a yankin nan namu an fara kasuwancinsa a ciki ba kawai a rika lodawa ana fita da shi muna kallo ba. Gwamnatin jiha ta taimaka da abubuwan ci gaba a wannan kasuwa, akwai babban alheri da za ta samu idan ta yi haka”. In ji shi.

Kasuwar ta SCC Junction dai ta yi makotaka da tashar jirgin kasa ta Jere wadda babbar dama ce ta habaka kasuwanci a wurin.

Tare da: Abdulrazak Yahuza Jere

08039216372

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI