Connect with us

WASIKU

‘Ina Jajanta Wa Al’ummar Taraba’

Published

on


Assalamu Alaikum. Editan LEADERSHIP HAUSA, da fatan kana Lafiya. Bayan haka ina amfani da wannan dama in jajanta wa mutanen da rikicin manoma da makiyaya ya rutsa da su a Jihar Taraba. Allah ya kare afkuwar hakan nan gaba.

Daga Nura Muhammad Gusau.

 

 • Kadan Ne A APC Mutanen Kirki

Kashi hudu cikin dari na ’ya’yan jam’iyyar APC ne mutanen kirki, ciki har da Shugaba Buhari, amma sauran kashi 96 duk bara-gurbin ’yan jam’iyya ne.

Hakika na yi matukar mamakin yadda wasu ’ya’yan jam’iyyar APC mai mulki a kasarmu Nigeriya ke son fin na jam’iyar PDP rashin mutunci a lokacin da suna mulki, yanzun ta kai dan jam’iyyar APC zai iya yi wa talaka rashin mutunci ko rashin kunya wai don su ne da mulki.

Abin kunya da mamaki shi ne yadda gwamnatin jihar Katsina ke kokarin daukar mata masu dafa abinci a makarantun Frimare, amman sai ga shi ’ya’yan jam’iyyar APC na daukar matansu maimakon su dauki matan wadanda suka rasa rayukansu kuma suka bar iyalai. A gaskiya mun kusan cewa kada Allah ya maimaita mana irin gwamnatin APC.

Daga Abba Sa’ad Mahuta, Dan Kungiyar Muryar Jama’a, reshen jihar Katsina, 0706 254 5272.

 

 • Ya Kamata A Tausaya Wa Jama’a A Sallar Nan

Assalamu Alaikum. Tabbas Bukukuwan Sallah wannan karon zai zo mana a wani irin hali na tsadar rayuwa da al’ummar Afrika suka tsinci kansu, musamman kasashenmu Nijeriya da Nijar.

Sai dai fatan kira ga mahukunta da masu hannu da shuni da su tashi tsaye wajen ganin taimaka wa mabukata da hanyoyin tufatarwa da ciyarwa a cikin wannan karshen wata da muke ciki, domin nuna jin kai da saukaka wa al’umma bukukuwan sallah.

Daga Hafizu Balarabe Gusau

 

 • Muna Fatan A Samu Sakamako Mai Kyau

ASSALAMU Alaikum. Edita, da fatan kuna cikin koshin lafiya. Hukumomin kasar mu Nijeriya da wasu kungiyoyin hawa kan taburin tattauna kan batun makamashi da ake sabuntawa da nufin shata wa kasar makoma a bangaren makamashi. Muna fatan samun matsaya mai kyau Amin.

Daga Arabiyyu Muhammad Gidan Madi, Dalibi a Kwalejin Shehu Shagari da ke Sokoto 0806 787 3852

 

 • An Yi Walkiya Mun Ganku

Assalamu Alaikum, tabbas yau kirana ga mahukunta a Nijeriya ne, ganin yadda gwamnatin tarayya ta sa wa kasafin kudin bana hannu. To al’ummar kasa sun zuba na mujiya su ga yadda za su amfana da shi, domin kuwa an dade ana ruwa kasa na shanyewa, sai dai talakawan kasa su ji maganar kasafin kudi a kafafen yada labarai sun ki gani a kasa, to ku sani fa komai nisan jifa kasa zai fado, an yi walkiya mun ganku.

Daga Shugaban Muryar Talaka Zamfara HAFIZU BALARABE GUSAU 07035304499

 

 • A Kara Kaimi A Harkar tsaro

Assalama  Alaikum.  Edita don Allah ka ba mu dama na yi kira ga Hukumomin Nijeriya da su kara  tsaurara matakan tsaro a hanyoyin dake fadin sassan Nijeriya Kudu da Arewa, Gabas da Yamma, Saboda ’yan fashi da makami sai karuwa suke masaman a wannan lokaci na gabatowar karamar  salla.

Daga Garba Sabiyola Gashua da Musa Baki Maidoya kasuwar  Gashua  0809 628 4154

 

 • Gara Kowa Ya San Matsayinsa

To Hausawa mazauna jihohin Igbo, mayar da martani kan wa’adin wata uku da matasan Arewacin Nijeriya suka ba ‘yan kabilar Igbo a kan su bar yankin, wannan ya yi, gara ma kowa ya san matsayinsa da mu da su.

Daga Arabiyyu Muhammad gidan Madi Sokoto

 

 • Kyautata Tasro A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Ya Yi Daidai

ASSALAM LEADERSHIP HAUSA. Matakin ba sani ba sabo da gwamnatin Nigeriya ta dauka akan tsaro, musamman a kan hanyar Kaduna Zuwa Abuja sakamakon matsalar satar mutanen da ta zaman ruwan dare a yankin ya yi daidai, domin ita ce tun yana danye ake tankwarashi, masu hauwa babur  da masu aceba a yankin sai a dauki hakuri a zuba wa sarautar Allah Ido, a kuma ba Jami’an tsaro hadin kai domin a gudu tare a tsira tare. Allah ya sa a dace.

Daga Alhaji Umaru Foreba Gashua 0810 800 3333

 

 • Allah Ya Ba Baba Buhari Lafiya

Assalamu Alaikum. Barka da wannan lokacin, da fatan kuna Lafiya, tare da sauran ma’aikatan kakwata! Ina amfani da wannan damar ta wannan wata mai Albarka, in yi addu’a ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Allah ya kara mai lafiya da nisan kwana, Allah ya sa ya dawo lafiya domin ya ya ci gaba daga inda ya tsaya. Kuma Allah yaba sauran musulmai da ba su da lafiya sauki a duk inda suke.

Daga Nura Muhammad Gusau,  dan kungiyar muryar talaka ta kasa, reshen jihar Zamfara

0813 337 6020

 

 • Assalamu Alaikum Edita.

Hakika umarnin da wata kungiyar matasanmu na Arewa su ka bawa yan kabilar Ibo da su bar yankin Arewa, sam bai zo mana da mamaki ba, ganin yadda suma matasan na kudun suke cin karensu babu babbaka, a ce har a cikin Arewa suna sanye da irin launin tutarsu wai don son neman fitina kawai, kuma Gwamnoninsu na Kudun sun kasa tsawatar musu, lallai ba zai yi wu ba, domin shiru-shiru ba domin ba tsoro ba ne.

Daga Shugaban Muryar Talaka Zamfara Hafizu Balarabe Gusau 07035304499

 

 • Wanda Bai San Bushiya ba, Shi Yake Dirka Mata Naushi

Salam Edita, na fara da wannan magana ne domin in yi tsokaci dangane kan yadda matasan kabilar Igbo ke ci gaba da kokarin kawo barazanar zaman rashin lafiya ga kasarmu Nijeriya ta hanyar  ganin yankin nasu ya zama kasa mai cin gashin kansa wato kasar ‘biafra’ wadda har ta kai ga suna yi wa alummar Arewacin Nijeriya da ke yankunansu barazanar su fice daga yankin kafin wani wa’adi da suka gindaya musu, wanda har hakan ya kawo alummar Matasan Arewacin Nigeria sun fusata, suma sun dauki wannnan mataki ga alummar Igbo dake Arewacin Nijeriya.

Ya kamata wadannan mutane dake kokarin kafa kasar biafra ku sani cewa wannan mataki da kuke shirin dauka dauka babu inda zai jefa ku sai da na sani da nadama. Idan aka yi la’akkari da yadda mutanenku dake zaune a Arewaci, sun ninka alummar Arewaci da ke zaune a yankunanku yawa nesa ba kusa ba. Amma idan hakan kuke ganin ya fi maku daidai, to ga fili ga maidoki. Ku ya kamata ku tambayi magabatanku irin wahalar da suka sha a baya, a lokacin da suka dauki wannan gurgun mataki. Hasalima dukkan wani arziki da kuke tunkaho da shi a wannan kasa, an gina shi ne da arzikin Arewa, don haka babu wata burga da za ku yi mana, domin kowa ya ga Balbela da farinta ya ganta.

Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia 08060353382

 

 • Babu Dalilin Raba Nijeriya A Yanzu

Salam Edita, na rubuto wannan wasika don in ja hankali kan a san cewa Nijeriya dai kasa guda ce kuma kowa nada hakkin zama a inda yake da ra’ayi a matsayinsa na dan kasa, don haka nake kira ga masu kiran yan wasu kabila su fice daga wani yankin Nijeriya a kudu yake zaune ko a Arewa su daina kuma bama goyon bayan kama kungiyoyin Matasan Arewa da Gwamnan Kaduna ya yi ikirari.

Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI