Connect with us

LABARAI

Ku Biya Ma’aikatan Ku Albashi, Su Na Cikin Tsanani, Cewar Buhari

Published

on


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin jahohin da ma’aikatansu ke bin bashin albashi da fansho, da su biya ma’aikatan wandanda kacokam sun dogara ne akan albashin na su.

Shugaban ya damu da yadda gwamnonin suka gaza biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya na daga fansho da garatuti duk da an dawo da kudin rance na ‘Paris club’ kuma an raba su ga jihohin Kasar.

‘akwai yan Nijeriya da ba a basu albashinsu na watanni shida ba, da wadanda ma ba a biyasu hakkokin ritaya ba, don haka na umarci gwamnonin kasar nan da su biya ma’aikata  hakkokinsu saboda mafiya yawansu da shi suka dogara don gudanar da bukatun rayuwarsu.’ Inji Shugaban Kasa Buhari


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI