Connect with us

LABARAI

Zuba Jarin Naira Biliyan 100 Na Sukuk: An Yaba Wa Gwamnatin Tarayya

Published

on


Daga  Abdulrazak Yahuza Jere, Abuja

Masu zuba jari a bangaren harkokin kudi da ke sassan kasar nan sun yaba wa Gwamnatin Tarayya kan shirin da ta bullo da shi na zuba jarin Naira bilyan 100 daga hannun ‘yan kasuwa a karkashin Ofishin Bin Diddigin Basussuka.

Daraktar ofishin, Misis Patience Oniha, tare da jami’an Ma’aikatar Lantarki da Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, sun shaida wa masu ruwa da tsaki a bangaren a Legas, da Fatakwal da Abuja cewa kudin Naira bilyan 100 za a zuba ne a bangaren gina muhimman hanyoyi a kasar nan.

Shirin mai lakabin “Sukuk” da babu ruwa a ciki, wani tsari ne na zuba jari da za a rika biyan kason riba kamar yadda ake biyan kudin haya a shekara-shekara, kana daga bisani a biya babbar jumillar kudin da aka zuba a karshen shekara bakwai na zubi.

A yayin da take bayani a wuraren da suka ratse daban-daban a kan hanyoyi yayin kaddamarwar farko, Oniha ta tabbatar wa masu zuba jari cewa shirin na “Sukuk” ya samu cikakken goyon baya daga Gwamnatin Tarayya kuma ya kasance daya daga cikin hanyoyin da za a samar da kudade domin gudanar da manyan ayyuka.

“Wannan daya ne daga cikin yunkurin da ake ta faman yi wajen ganin an samar da kudin aiwatar da wasu kebantattun ayyuka kuma abin ya samu cikakken goyon baya daga Gwamnatin Tarayya. Tsari ne da za a rika biya kamar yadda ake biyan haya wanda aka bullo da shi don al’ummar da ke muradin hakan su ci gajiyarsa”, in ji ta.

Mataimakin Daraktan Tsare-Tsare da Cigaba na Ma’aikatar Lantarki, Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, Mista Danlele Yila, ya lissafto ayyukan hanyoyi guda 25 da aka rarraba a sassan manyan shiyyoyin siyasa shida na kasar nan da za a yi amfani da kudin Sukuk wajen aiwatarwa.

Daga cikin ayyukan sun hada da gina gadar Loko Oweto, tagwaita hanyar Abuja zuwa Lokoja, tagwaita hanyar Suleja zuwa Minna da kuma ta Kano zuwa Maiduguri.

Sauran sun hada da tagwaita hanyar Kano zuwa Katsina (Ohase 1), gyara babbar hanyar Onaca zuwa Enugu, hanyar Enugu zuwa Fatakwal (section 1-3) da kuma tagwaita hanyar Ibadan zuwa Ilori (section 2).

Daya daga cikin wakilan shirin, Tunde Adama na bankin Citibank, wanda ya zanta da wakilinmu bayan taron farko, ya ce akwai kyakkyawan yakini a kan shirin na Sukuk.

“Wannan sabon shiri ne wanda yake nufin bude sabon babin cigaba ga masu muradi, sabuwar hanya ce ta zuba jari. Ina da yakinin cewa shirin zai kai ga gaci kamar yadda sauran tsarin basussuka da Ofishin Bin Diddigin Basussuka ke bullo da su.”

Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya, reshen Jihar Ribas, Hajia Maimuna Bello, ta bayyana shirin a matsayin babban yunkurin cimma muhimman muradu na kasa, sai dai ta bukaci ofishin ya kara himma wajen wayar da kai game da shirin.

A Abuja kuwa, tsohon babban daraktan Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Ibrahim Waziri, wanda ya yi marhabin da shirin ya yi fatan cewa za a kashe kudin da za a tara a shirin wurin aiwatar da ayyukan da aka lissafa, kana ya jaddada cewa saboda kyakkyawan tsarin da aka yi wa shirin, masu zuba jari za su rika samun kasonsu na riba a kan kari.

Daga cikin alfanun shirin na Sukuk kamar yadda ofishin DMO ya bayyana, akwai kiyaye amanar ajiya, samun kudin shiga a kai-a kai ba tare da an cire haraji ko makalewar kudi ba, kasancewar za a rika tallatawa a Kasuwar Hannun Jari ta Kasa da makamancinta na FMDK OTC.

Ana iya amfani da shirin a matsayin abin jingina wajen karbar bashi daga bankuna.

Shirin zuba jari na Sukuk shiri ne na Naira bilyan 100 mai kimanin tsawon shekara bakwai kuma ya samu aminci daga Majalisar Kwararru Masu Ba da Shawarwari Kan Sha’anin Hada-Hadar Kudi na Babban Bankin Nijeriya.

Za a sanya shirin tare da tallata shi a Kasuwar Hannun Jari ta Kasa da makamancinta na FMDK OTC tare da fara amfani da shi a ranar 14 ga Satumba.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI