Sakarwa Kananan Hukumomi Mara Zai Taimaka Wa Habbakar Yankunan Karkara –Kwamared Adamu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Sakarwa Kananan Hukumomi Mara Zai Taimaka Wa Habbakar Yankunan Karkara –Kwamared Adamu

Published

on


Sakarwa Kananan Hukumomi Mara Zai Taimaka Wa Habbakar Yankunan Karkara –Kwamared Adamu

Kwamared Zakari Y. Adamu Kontagora, shi ne shugaban kungiyar ‘A Taimaki Al’umma’ reshen Jihar Neja, kuma mataimaki na musamman akan kafafen sadarwa da yada labarai ga dan majalisar jiha mai wakiltar Kontagora ta biyu. A tattaunawarsa da wakilin mu Muhammad Awwal Umar, ya yi karin haske ga fahimtarsa na ba kananan hukumomi ‘yanci don su ci gashin kan su. Ga yadda hirar ta kasance:

Akwai wasu kudurori da shugaban Jam’iyyar APC ta kasa ya fitar a matsayin abubuwan da ya kamata a gabatar don samun daidaito ga halin da kasar nan ke ciki, kuma maganar ba kananan hukumomi daman cin gashin kansu na ciki, ganin talaka yafi kusa da karamar hukuma. Shin me ka fahimta da cin gashin kan kananan hukumomi?

A fahimta ta idan ana maganar ‘yancin gashin kai ana nufin ‘yan tawa, ma’ana cikakkiyar ‘yancin gudanar da abu. Wato karamar hukuma ta rika samun kudaden ta kai tsaye daga gwamnatin tarayya tare da cikakkiyar ‘yancin gudanar da al’amuran ta na mulki ba tare da gwamnatin jiha ta yi mata katsalandan ba, maganar bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kan su tabbas abu ne mai matukar muhimmanci a tsari na dimokradiyya, a kowace kasa ta duniya musamman irin kasar mu Nijeriya da dimokradiyyar ta take jaririya, duba da irin rawar da kananan hukumomin ke takawa ta fannin cigaban kasa da al’umma akwai bukatar su kasance masu cikakkiyar ‘yancin gashin kansu  kamar yadda gwamnatocin jihohi da na tarayya suke da shi, domin karamar hukuma itace gwamnati mafi kusa da al’umma musamman talakawa saboda kafin gwamnatin Jiha ko na tarayya ta ji koke guda na talaka  karamar hukuma ta ji uku, kenan ka ga idan suna da ‘yancin gashin kansu za suyi kokarin sharewa talakawan su hawaye ba tare da jiran tallafin Jiha ko gwamnatin tarayya ba.

Sannan irin ayyukan raya kasa da karamar hukuma ke yi kamar samar da hanyoyi a cikin unguwanni da yankunan karkara da samar da wutan lantarki ga al’umma zai karu, ilimi a matakin farko zai inganta, ruwan sha mai tsafta zai wadata a cikin al’umma, samar da ayyukan yi ga matasa zai karu, zaman kashe wando zai ragu, za a samu sauyi sosai a rayuwar ‘yan kasa, ka ga kenan an ragewa gwamnatin jiha da ta tarayya wani dawainiyar da ke bisa kansu. Hakan kuma zai taimaka matuka wurin ciyar da wannan kasa gaba a dan kankanin lokaci.

Ana ta maganar cin gashin kan kananan hukumomi, a farkon 1999 da aka faro zubin siyasar kananan hukumomi na mallakar kudadensu kaitsaye, amma duba da yadda aka mayar da aljihun kananan hukumomi kamar ramin bera yasa gwamnoni da majalisa kirkiro dokokin yau su kanananan hukumomin suke kokawa akan su yanzu, ba ka ganin idan an sake ba su damar ‘yar gidan jiya za a sake komawa?

Eh zamu iya cewa hakan ne, sai dai wani abu da ya kamata mu yi la’akari dashi a nan shi ne ba a taru aka zama daya ba, don wasu shugabannin kananan hukumomi a baya sunyi kuruciyar bera da watanda da baitilmalin kananan hukumominsu, ba shi zai sa mu ce za a cigaba da tsarin handame kudaden talakawa ba kamar yadda ya faru a baya ba, idan sun samu ‘yancin gashin kan nasu a wannan lokaci, domin ko a halin yanzu da muke ciki akwai shugabannin kananan hukumomin da suka taka rawar gani ta fannin yiwa al’ummar su ayyukan cigaba da ‘yan kudaden da ake basu duk da mun san akwai baragurbi daga cikin su wadanda tunda suka hau karagar mulki ba abin da suka tsinanawa al’ummarsu ta fannin ayyukan cigaba , misali a Jihar mu ta Neja akwai shugabanin kananan hukumomin da na san sun yiwa al’ummar su ayyukan da ko gwamna ya yi su a jin-jina masa hakan yasa uwar jam’iyyar su ta  APC na Jiha da sauran kungiyoyin cigaban al’umma na kasa suka ba su lambar yabo, to ina ga idan sun samu cikakkiyar ‘yancin gashin kai, ka ga ai sai abin da hali yayi wurin yiwa al’umma ayyukan raya kasa.

In haka ne wace hanya ya kamata a bi idan an bai wa kananan hukumomin cin gashin kan da suke koka wa ganin ba a koma ‘yar gidan jiya ba?

Babban hanyar farko dai shi ne al’umma su rika zaban mutanen kirki a matsayin shugabannin su masu gaskiya da rikon amana wadanda keda kishin cigaban kasa da al’umma a zukatan su, domin tun ran haihuwa ake barin kyau inji hausawa, saboda da daman shugabannin kananan hukumomin da za kaga basu tabaku wani abin azo agani ba tun farko ba al’ummar ce a gaban su ba, manufarsu kawai ya za su handame kudaden talakawa su rika siyan kadarori da su, saboda haka  akwai bukatar masu zabe wato talakawa su yi tsantsaini tare da karatun tanatsu wurin dora mutum a matsayin shugabansu, duk wanda ya fito takarar shugaban karamar hukumar su yi bincike akan halayyarsa wani irin gudunmuwa na cigaba ya bayar a baya a wannan karamar hukuma tasu, sannan su yi zama na fahimta da shi su ji manufofinsa da kudurce-kudurcensa idan sun gamsu da irin manufofinsa sai su rubuta takardan yarjejeniya a rubuce da shi akan idan ya hau ba zai zaude daga wadannan manufofi na shi ba.

Bayan haka akwai bukatar al’umma su rika bibiyar kudaden da ke shigowa kananan hukumominsu daga gwamnatin tarayya da kudaden shigan da ta ke samu a cikin gida da kuma irin aikace- aikacen da ake yi da kudaden na su, hakazalika kungiyoyin cigaban alumma su kara sanya ido akan al’amurran kananan hukumomin tare da bankado duk wani kitumurmura ko almundahana wanda ka iya cutar da rayuwar talakawa da suka ga ana kokarin yi a karamar hukumar.

Sannan akwai bukatar ita  kanta gwamnatin tarayya ta kafa hukuma na musamman da za ta rika kula tare da sanya ido ga al’amurran kananan hukumomin ta yadda za su kashe kudaden da ake ba su hakan zai sa a kwaucewa komawa ‘yar gidan jiya.

Amma ai su kan su kananan hukumomin, suna da hanyoyin samun kudaden shiga, idan an yi dubi da irin dalilan da yasa aka kirkiro su, ko akwai wata doka ne da ke hana su yin anfani da kudaden da suke samu a matsayin hanyar shiga daga yankunan kananan hukumomin su.

Duk da ni ba kwararran masanin doka ba ne amma dalibin shari’a ne, a iya sani na ba wata doka da ta hana karamar hukuma anfani da kudaden da ta ke samu na cikin gida, idan ma ka ga shugaban karamar hukuma ya ki ya yiwa al’umma ayyukan cigaba da kudaden da karamar hukumar ke samu daga cikin gida, to yayi hakan ne bisa radin kansa ba wai don doka ta hana ba, kuma da alama yana da wata boyayyar manufa ta zaluntar al’ummarsa wanda hakan bai dace b, domin duk kudaden da karamar hukuma ke karba daga al’umma, kudade ne da ake bukatar a yiwa al’umma ayyukan da za su anfani rayuwarsu da na iyalansu, hakazalika su kansu al’ummar na bukatar ganin anyi masu aiki da kudaden da ake karba daga hannunsu hakan zai sa a duk lokacin da Jami’an gwamnati masu karbar rabano da haraji suka zo karba ba za su ji kyashin bayarwa ba domin sun san abin da za ayi da kudaden nasu.

To me ke sanya a kowanne lokaci ba su son fitowa suna fadawa jama’a abin da suke samu kullum sai kokawa akan an ki sake masu mara.

Magana ta gaskiya duk shugaban karamar hukumar da ka ga yana noke -noke yana kin gayawa al’ummarsa gaskiyar kudaden da karamar hukumar ke samu to tabbata ba adalin shugaba ba ne kuma alamace ta ya shirya zaluntar al’ummar da suka zabe shi domin duk shugaban da ka ga yana boyewa al’ummarsa wani abu da ya kamata ace sun sani wannan ba shugaba nagari ba ne, kuma bai kamata ya zama shugaban al’umma ba domin shugabanci na bukatar gaskiya da rikon amana tare da yiwa al’umma adalci a kowanne hali.

Misali a iya sani na ga al’amuran wannan gwamnati na jihar mu ta Neja duk shugaban karamar hukumar da kaji yana fadar gwamnati ba ta bashi kudaden gudanar da harkokin karamar hukumarsa ba gaskiya ya fada ba, domin da zuwan wannan gwamnati maigirma gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello abin da ya fara yi na farko shi ne maganar yadda kananan hukumomi za su dogara da kansu kuma duk karshen wata kananan hukumomin jihar Neja 25 na samun kudaden su kamar yadda ya dace, saboda haka duk wani shugaban karamar hukumar da ka ga ya kiyiwa alu’mmarsa ayyukan cigaba ganin damarsa ne, ba don ba a ba shi kudade ba.

Wani abu ma dake kara daure mani kai ga wasu shugabannin kananan hukumomi hatta kansiloli da suke a matsayin wakilan al’ummar gundumomin su ba sa sanin hakikanin na wane karamar hukuma ke samu daga gwamnatin tarayya da kudaden shigarta na cikin gida, wanda wannan babban kuskure ne, ina kira ga duk wani shugaba da yasan yana irin wannan tafiyar da ya gaggauta canzawa, ya kuma mai da hankali wurin yiwa al’ummar da suka zabe shi ayyukan da zai anfani rayuwarsu.

Ina fatar wannan kuduri na bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kansu da shugaban jama’iyar APC na kasa ya yi magana akai zai samu sahalewar gwamnatin tarayya duk da na ga ‘yan majalisun tarayya sun taka rawar gani wurin tabbatar da wannan doka muna jin-jina masu akan wannan kokari da suka yi, ina fatan bangaren zartaswa ita ma za ta goyi bayan wannan doka, domin ina da yakinin alheri ne ga al’ummar kasar nan musamman ma talaka..

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!