Farfaganda Ko Kama-karya: Da Me Masari Zai Nemi Tazarce A Jihar Katsina?                            — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Farfaganda Ko Kama-karya: Da Me Masari Zai Nemi Tazarce A Jihar Katsina?                           

Published

on


Tare da Maje El-Hajeej Hotoro 08038529660, 08038529660

A lokacin da marigayi Umaru Musa ‘Yar adua ya na Gwamnan jihar Katsina (Allah Ya jikansa), ban yi tsammanin gwamnan da zai gaje shi zai malala makamancin irin ayyukan ci-gaba da ya yi ba. Bayan ya zama shugaban kasar Najeriya Ibrahim Shehu Shema ya gaje kujerar, sai wani abokina ya tabbatar min cewa ya fi ‘Yar adua assasa ayyukan raya kasa a jihar Katsina. Ba tare da bata lokacin ba na kira wani abokina ya kuma tabbatar min da hakan. Watarana sai na samu damar tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin kasar jamhuriyar Nijar, don haka sai na mayar da jihar Katsina sansanin yadda zango a yayin tafiya ko dawowa. Wannan ne ya ba ni damar ganin ayyukan Shema, amma duk da haka sai na nemi wani abokina dan jarida na ce ya hada ni da wani ciakken dan adawa da zai yi wa Gwamnatin Shema alkalanci.

Makeken gida ne wanda aka narkarwa da mahaukatan kudade irin na wanda ya rike mukamin Gwamna ko wani babban mukami a gwamnatin tarayya. Waye wannan? Shine tambayar da na fara yi wa abokina kasancewar dan adawa na ke nema da zai fallasa badakalar Shema. “Wannan gidan Mustapha Inuwa ne da ake yi wa lakabi da Zakin Adawa, saboda yadda ya ke fatattakar gwamnatin Shema”. Mun gaisa na kuma gabatar masa da kaina a matsayin dan jarida da ya ke son ba shi damar bayyana abinda bas u gamsu da shi ba a wannan gwamnati. Ya kuma amine na kara masa abin daukar magana ya fadi a binda ya ke son fada. Bayan kammala hirar na yi mamakin yadda mutumin da ya rike mukamin kwamishinan ilimi da kuma sakataren gwamnati a jihar Katsina kuma lokacin Umaru Musa ‘Yar Adua zai mallaki mahaukacin gidan da Mustapha Inuwa ya mallaka. Kamar yadda ban yi tsammanin duk fadin jihar Kano akwai wanda ya rike mukami a jihar ba Gwamna ba ya gina makamancin wannan katafaren gida.

Ya ragargaji Shema ya bayyana shi a matsayin azzalumin mai mulki irin na Fir’auna, kana kuma ya kore masa imanin sa na Mususlunci ta hanyar alakanta shi da makamancin akidar addini daya da Jonathan. Kasancewar aikin jarida kamar kowane aiki na da sharudda da ka’idoji wasu zantukan ba za su iyu a wallafa ba. Na kuma cika masa alkawari na wallafa masa wannan hira a jaridar Leadership HAUSA, wanda aka yi wa kanun labari da zazzafan furuci akan Shema daga bakin Mustapha Inuwa. Wannan ya sa wasu suka ja hankalina da cewa, kalamansa cike suke da tsantsar bakar hassada fiye da adawa, domin ko ba komai gwamnatin da ta yi shekaru takwas tana mulkin jiha da wahala ta rasa wani alheri komai kankantar sa. Kuma akwai bukatar ba wa gwamnatin da aka soka damar kare kanta a matsayin albarkacin fadin albarkacin baki na aikin jarida.

Salisu Yusif Majigiri shine shugaban ma’aikata na gwamnatin Shema na riske shi a gidan gwamnatin jihar Katsina cikin ofishinsa. Bugun kirji yayi tare da cewa, idan na zagaya cikin jihar na samu aiki daya da ‘Yar Adua ya fara bas u kammala ba ko daidai da girman kujerar da na ke zaune a kai ne zai ba ni kyautar Naira Miliyan daya. Na kuma tabbatar da wannan furuci nasa daga bakin ‘yan jihar, lokacin guda ya ce shi ba zai fada min me suka yi ba biya ma zai yi mu sa a jaridar mu hotunan da ayyukan da gwamnatin su ta yi. Kuma wasu daga ciki ma sa wa yayi na zagaya da na’urar daukar hoto na dauki hotunan ayyukan da ake tsaka da gudanar da su. Ya kuma sayi shafuka a jaridar aka sanya ayyukan tare da kalubalantar wanda ya ce ba a yi ya zo ya karyata ya ce ba a yi ba.

Allah mai jujjuya al’amura yadda Ya so, yau an tsinci Masari ne gwamnan jihar Katsina. Kuma Zakin adawa Mustapha Inuwa shine Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina. Ban yi mamakin ganin tsohon Gwamna Shema a komar EFCC ba, doming a duk wanda ya taba zama daya da Mustapha Inuwa zai tabbatar da cewa, ba abinda zai hana idan suka samu dama su wulakanta Shema. Kazalika ban yi kasa a gwiwa ba na kara rankayawa jihar Katsina domin sake ba wa wani dan adawa dama ya yi wa gwamnatin Masari alkalanci kamar yadda suka yi wa Shema a baya. Muttaka Rabe Darma dan jam’iyyar PDP ne kuma tsohon shugaban hukumar albarkatun man fetur ta kasa (PDTF), na same shi mai matukar bambanci da Mustapha Inuwa. Ya na magana cike da ilimi gami da adalcin magana ta hanyar buga misali ba shaci-fadi ba. Bugu da kari ba wani gillin ramuwar gayya ko takaicin rasa kujerar jihar da ya sa shi kokarin yi wa Masari batanci.

A cewarsa farfaganda ita ce jigon gwamnatin Shema, domin kullum fadi suke (kamar yadda ya ji) ba don an sace kudi ba da sai sun mayar da Katsina kamar Landan. An zargi Shema da sace Naira Bilyan 52, kuma yanzu Masari ya karbi irin wannan Naira Bilyan 52 ya kais au takwas amma jihar Katsina ba ta koma birnin Landan ba. Babu abinda ya ke yi, kuma kudin da ya karba PDP ba ta taba ganin su ba. Sannan daga lokacin da suka karbi gwamnati zuwa yanzu sun karbi kudaden da ya ninnika kudaden da Shema ya karba a shekarunsa na karshe. Shema yayi aiki da kananan hukumomi ya sakar musu kudaden su amma a yanzu Masari ba ya aiki da kananan hukumomi. Duk kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya kai-tsaye asusun jihar ya ke zurarewa. Sannan idan mun karbi kudade muna sanar da mutane cewa ga abinda muka karba kuma ga abinda za mu yi da su.

A shekarar 2016 gwamnatin jihar Katsina ta karbi Naira Bilyan 82 daga gwamnatin tarayya, sannan a wannan shekarar gwamnatin jihar Katsina ta ciyo basussukan da sun kai Naira Bilyan 25. Sannan ga kudaden Paris Kulob wanda jihar Katsina ce jiha ta hudu da ta karbi kudade mafi tsoka inda ta karbi Naira Bilyan 15. Sannan a kalla ta na karbar haraji misali ya kai miliyan 500. Idan ka hada tun daga lokacin marigayi Musa ‘Yar Adua ya yi Gwamna tsawon shekara takwas zuwa Shema da ya yi shekara takwas ba wani Gwamna da ya karbi irin wadannan kudade da gwamnatin Masari ta karba a shekara kusan uku kacal. Idan kuma akwai mai tantama ya je ya dauko manazarci ya bincika ya sannan ya karyata wannan magana.

A baya abu ne mai sauki ka samu wani jigo a gwamnatin Shema yayin da ka so ba su damar kare kai akan wani zargi, amma abin mamaki Mustapha Inuwa da a baya kowane lokaci wayarsa a bude ta ke, yanzu ta yi wahala. Kowa ka taba tsoron su ya ke ji saboda fargabar za su hana shi takara a gaba ko kuma suna gaba da shi don wani dalili. A yanzu gwamnatin jihar Katsina ta zama ta ‘yan farfaganda da kama-karya. Duk abinda Gwamna ya fada ba mai musawa, an yi taron karrama wadanda suka yi mulkin jihar Katsina an cire sunan Shema da yayi Gwamna tsawon shekaru takwas. Duk kuwa da yayi muhimman ayyukan da zuwa yanzu dai Masari bai yi sub a, sannan cikin alfahari sun bayyana ayyukansu ga duniya, amma halin yanzu dan majalisar jiha ma fargabar sakataren gwamnatin ya ke ji kamar mulkin soja ba na siyasa ba. Saboda tsabar kama-karya shugabannin jam’iyyar APC na jihar sun fake da Buhari sun ba wa Masari tikitin takarar kai-tsaye ba tare da an ba wa ‘yan jam’iyyar damar gwada sa’ar su ba. Wanda duk duniya wannan ba dimokradiyya ba ne, wannan ya sa yanzu jam’iyyar ta dare gida biyu saboda fargabar ba za su samu adalci ba.

Advertisement
Click to comment

labarai