Connect with us

ADON GARI

MIYAR KAYAN LAMBU

Published

on


Kayan Hadi

1-Naman Kaza

2-Kabeji

3-Karas

4-Koren Wake

5-Peas

6-Attaruhu

7-Red pepper

8-Yellow pepper

9-Grean pepper

10-Sinadarin girki

11-Gishiri

12-Corry

13-Thyme

14-Mai

15-Courn flour

 

Yadda A Ke Hadawa

Uwargida da zarar kin wanke kazar ki kin tsabtace ta sai ki dora a wuta ki tafasa sai ki sauke ki soya ta ki kwashe ki ajiye a gefe. Sai ki dauko duk kayan lambunnan ha su tattasan duk ki wanke su ki yanyankasu. Kowanne ki yi masa mazubinsa daban, ki ajiye su a gefe. Sai ki zuba mai a wuta in ya yi dan zafi sai ki dauko thyme ki zuba a man ki dsoya thyme din za ki ji kamshi Na tashi sai ki zuba peas,karas,koren wake,ki rage wuta kasa kasa. Ki barsu su Dan nuna kadan. Sai ki zuba ruwan tafasar naman dan kadan saboda duk kayan lambun suma ruwa ne Sai ki zuba sinadarin dandano gishiri curry dede dandano. Sai ki barshi ya dan muna sai ki zuba red pepper, green pepper da kuma yellow pepper. In suka dan dahu sai ki zuba kabejin. Sai ki barshi ya dahu, ruwan jikin sa ya gama fitowa. Sai ki dama courn flour kadan da dan kauri ki zuba Dede kaurin miya. Sai a barshi ya dan dahu. Sai a sauke A ci da shinkafa ko kuskus. Wajen dahuwar shinkafar ko kuskus din sai a yanyankata karot yadda ake so a dafa su fare.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI