Connect with us

WASANNI

Courtois Ya Na Son Komawa Real Madrid

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada

Mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, Thaibo Courtios yana son komawa kulob din real Madrid bayan dayaƙi sake sabon kwantaragi da Chelsea kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Courtios  yana jin dadin zama a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea tun bayan daya koma ƙungiyar ashekara ta 2014  inda ya lashe gasar firimiya guda biyu acikin wasanni 118 da yayiwa ƙungiyar.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa dan wasan yana son komawa real Madrid ne sakamakon yayi zaman garin lokacin da ya zauna a ƙungiyar Atletico Madrid a lokacin da Chelsea ta kaishi aro.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta real Madrid dai ta dade tana neman mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united sai dai har yanzu bata samu nasarar daukar mai tsaron ragar ba, daɓid de gea.

Courtois dai yanajin dadin zaman birnin landan tare da Chelsea sai dai an bayyana cewa wasu dalilai ne zasu sakashi barin ƙungiyar wadanda suka shafi rayuwar iyalinsa.

Saura dai shekaru biyu kwantaragin mai tsaron ragar yaƙare, sai dai tuni ƙungiyar ta Chelsea ta gayyaceshi domin a fara tattaunawa dashi akan sabuwar yarjejeniyar inda kuma akace mai tsaron ragar yana jan ƙafa akan zaman.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI