Connect with us

WASANNI

Ba Na Son Barcelona Su Dawo Firimiya- WENGER

Published

on


Mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana ra’ayinsa na cewar baya goyon bayan raɗe-raɗin da akeyi na cewar, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta koma gasar Firimiya ta ƙasar Ingila, in har dai yankin Cataloniya ya ɓalle daga ƙasar Sifen.

Yankin na Cataloniya dai yana neman ɓallewa ne daga ƙasar Sifen, domin yakoma cin gashin kansa, yayinda a kwanakin baya aka yi ƙoƙarin kaɗa ƙuri’ar raba gardama, domin ba yankin damar ɓallewa.

Ministan wasanni na ƙasar ta Sifen ya bayyana cewar idan har yankin na Cataloniya ya ɓalle daga ƙasar Sifen, to ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta iya komawa gasar Firimiya domin taci gaba  da taka leda.

Akwai ruɗani dai akan idan ƙungiyoyin da suke yankin na Cataloniya zasu koma buga wasa domin ƙungiyoyi uku ne kawai a yankin waɗanda suka haɗa da Barcelona, Espanyol, da kuma Girona.

Sai dai Mista wenger ya ce akwai ruɗani a lamarin domin idan har aka lalata yanayin zirga zirgar ƙasa da ƙasa, abin bazaiyi dadi ba.

Ya ƙara da cewar idan hakane ai yakamata yai kawai a dawo da Celtic ko Rangers, tunda sune yan ‘yankin Birtaniya, amma idan har Barcelona ne za su koma Firimiya yana ganin abin bazaiyi tsari ba.

Bugu da ƙari ya ƙara da cewar magoya baya zasu sha wahala wajen zuwa kallon wasa, inda yace yana fatan za’a sasanta lamarin a siyasan ce tunda ai magana ce ta siyasa bata ƙwallon ƙafa ba.

A ƙarshe wenger yayi fatan cewa maganar bazatayi nisa ba, kuma Barcelona zasuyi zaman su a ƙasar Sifen.

Ɗan wasan Barcelona dai, Gerard Pique ya na ɗaya daga cikin masu goyon bayan ɓallewar yankin na Cataloniya daga Sifen, saboda ko a kwanakin baya sai da magoya bayan, ƙasar Sifen suka yiwa ɗan wasan ihu a filin ɗaukar horo da kuma lokacin da ƙasar take buga wasa.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI