Connect with us

WASANNI

Konte Ya Ji Ciwo A Wasan Faransa

Published

on


Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, ɗan ƙasar faransa, N’Golo  yasamu rauni a wasan da ƙasar faransa  ta buga da ƙasar Bulgeria a wasan da ƙasashen suka fafata a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, wanda za’ayi a ƙasar Rasha a shekarar 2018 .

Ɗan wasan,  wanda a shekarar data gabata shi ne ɗan wasan dayafi kowane ɗan wasa ƙoƙari a kakar wasan data gabata a gasar Firimiya ta ƙasar ingila, yasamu rauni ne a daidai minti na 34 da fara wasan inda ɗan wasan Adrien Rabiot ya canje shi.

Ɗan wasan dai an bayyana cewa ba zai buga wasan ƙasar Faransa ba, wanda zata buga da ƙasar Belarus a ranar Talatar nan.

Idan ciwon bai warke ba har zuwa sati mai zuwa, wataKila ɗan wasan bazai buga wasan da Chelsea zata buga ba da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace da kuma wasan Zakarun Turai da zasu buga da Roma tsakiyar sati.

Chelsea dai tana a matsayi na shida akan teburin Firimiya kuma ƙungiyoyin Manchester City da United, su ne a matsayi na ɗaya dana biyu inda suka ba Chelsea ratar maki shida.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI