Connect with us

MANYAN LABARAI

Baru Ya Mayar Wa Da Kachikwu Martani

Published

on


Daga  Idris Aliyu Daudawa

Babban jami’in gudanarwa na Hukumar kula da albarkatun mai ta ƙasa NNPC, ya  fasa ƙwai akan zargin da ake mashi na, ƙin bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa wajen bada kwangiloli.

Idan dai ba a manta ba makon da ya gabata ne, ƙaramin Ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya rubuta wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wata takarda, inda ya yi zargin Baru bai bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa yadda ya dace wajen bada kwangiloli ba.

A wata doguwar takarda da aka fitar ranar Litinin ta hannu mai magana da yawun Hukumar albarkatun mai ta ƙasa, mai suna Ndu Ughamadu ya,kare wanda ake yi ma zargin ya ce shi zargin da ake bai da wata makama bare kuma ace tushe, bugu da ƙari kuma duk lokacin da za a bada wata kwangila, a na bin yadda doka ta ce a yi.

Ya ce, idan banda ayyukan Ajaokuta, Kaduna da kuma Kano, duk sauran abubuwan ba a wani ambaci maganar kwangilolin sayen wasu kayayyaki ba.

Maganar kwangilar da aka bada ta NPDC wannan an bi ƙa’ida, kazalika AKK  ita ma majalisar zartaswa ta ƙasa, ba a kai ga lokacin da za a bada kwangilar ba.

Ya ƙara da cewam da yake an buga yadda ake zargin ba a bi ƙa’ida ba, wajen bada kwangilolin NNPC a jaridu, sai shugaban ƙasa ya buƙaci babban jami’in gudanarwa na NNPC shi da ‘yan tawagarsa, da cewar su kare kansu, akan zarge-zargen da ake yi masu. Ita dai takardar da ƙaramin ministan mai ya miƙa a ranar 30 ga Agustar 2017, ta nuna cewa yawancin kwangilolin da aka bayar, ko kuma ba a sake fasalinsu ba, ba wanda ya taɓa tattaunawa da shi.

Babban abin da aka fi su kuma mai muhimmanci shi ne, tun daga farko, ba sai an sake fasalin kwangila ba, ko kuma a tattauna da ƙaramin minista, ko kuma su ɓangaren da ke amincewa da al’amuran da suka shafi kwangilar NNPC. Abu mai muhimmanci shi ne, shugaban ƙasa a matsayin shi na ministan albarkatun mai.

Da akwai wani lokaci da za a iya shiga wanda duk abin da ake so bai wuce amincewar mambobin ɓangaren bada kwangilar NNPC ba, Sai kuma ta wani ɓangaren, wannan kuma ya dace ne da yadda kwangilar ta ke, wannan ana buƙatar amincewrar shugaban ƙasa, kamar yadda ita wasiƙar kwangilar ta fayyace, ko kuma su majalisar zartarwa su amince da bada kwangila.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI