Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Ballagaza: Karuwanci Da Rayuwar Karuwai A Legas

Published

on


Daga Bello Hamza

Agatha Chukwuma budurwa ce da ta bar mahaifarta zuwa garin Legas domin neman hanyar da za ta mallaki abin duniya, saboda gari ne da ya shahara wajen gudanar da harkokin kasuwanci iri daban-daban.

Ta zauna tsawon wata shida a hannun wani kawunta ɗan yankin Orlu da ke cikin Jihar Imo.  Bayan ya sa ta a wata makaranta da ake ji da ita, a duk faɗin ƙasar nan, sai ta yi dabarar koyon sana’ar gyaran gashi, kusa da gidan da take zaune a wata unguwa da ake kira Fadeyi, a garin Legas.Ta kasance kullum tana da abin yi.

A makon da ya gabata ne, sai ta yi tunanin ta kai wa wata babarta Nneka da ke zaune a Ɓictoria Island ziyara, bayan ta daɗe tana ce mata za ta je, amma abin ya gagara.

Ta ce, tana jin labarin duk mutanen da ke zaune a wannan unguwa, mutane ne masu kuɗi, saboda mafi yawansu ma’aikatan banki ne ko kuma wani babban kamfani. Ganin yadda Nneka ke zuwa da motoci iri daban-daban lokacin da take kawo musu ziyara a Fadeyi, daga nan sai Chukwuma ta fara sha’awar irin wanna rayuwar. Saboda haka, kai wa Nneka ziyarar da ta yi, sai ya sa idonta ya ƙara  buɗe wa, inda ta ga wata sabuwar rayuwar da ba ta taɓa tuninta ba lokacin da take zaune a gida ba.

“Gidan da suke zaune da wasu ƙawayenta su biyu, gida ne mai kyau, babu shakka kai da ganin wannan gida ka san waɗanda ke cikinsa suna aiki a wani babban kamfani ne da ke wannan Unguwa,”  Yarinyar yar shekara 22, wadda ta iya sana’ar gyran gashi, ta gaya wa wakilinmu lokacin da suke tattauna wa a cikin wannan makon cewa, “Ina ganin Nneka ta daɗe tana zaman kanta, kuma ta san manyan mutane,” inji Chukwuma.

Ana amfani da kalmar zaman kanta ne, maimakon a ce karuwa, waɗanda kawalai ke kawo musu mazaje ko kuma su nemo da kansu ta hanyar tuntuɓa kai-tsaye ko ta hanyar kafar sadarwa ta zamani. Ana iya gane irin waɗannan mata ta hanyar sa kaya masu tsada da yawan gyaran gashi da riƙe waya mai tsada. Ra’ayinsu kullum shi ne su hole a rayuwa watau, “In kina da shi, ki ji daɗi”.

Chukwuma ta girgiza matuƙa lokacin da gane cewa babar nan tata da take sha’awar ta zama kamarta ashe karuwa ce, ta bayyana wannan alhinin nata ne lokacin da take zanta wa da majiyarmu.

Ta ce, zaman da ta yi na kwana biyu a Ɓictoria Island ya canza mata tunani kwata-kwata. Domin ta fahimci cewa, Nneka da ƙawayenta duk karuwai ne, kuma duk sun mallaki motocin hawa, suna yawan gyara jikinsu da sa kaya masu tsada, kuma suna yawan gyara gashinsu, kamar ba karuwai ba. Sai dai na fahimci wani abu, tsawon zaman da na yi da su a lokacin hutun mako, ban ga maza na zuwa wajen su ba, sai dai su yi wanka su shiga mota su fita, can zuwa wani lokaci kuma da daddare su dawo. A irin wannan fitar ce, wata rana, Nneka sun fita da ƙawayenta, ba su dawo ba sai da gari ya waye. Zuwa can sai ta kira ni ta ce da ni kada  in damu, za mu haɗu da safe domin yanzu tana tare da wani saurayinta ne. Dagan an ta fara ba ni labarin yadda ta samu kuɗi, hard a buɗe wasu shagunan sayar da kayayyaki a Legas.

“Na yi matuƙar gigiza da jin wannan labari kuma na yi mamamki ƙwarai yadda karuwa ke mallakar irin wannan maƙudan kuɗin da take juya wa a hannunta da kuma irin harkokin da take yi, daga nan ni ma sai na fara sha’awar in tsoma ƙafata cikin wanna harka, ko ni ma na fara kece raini cikn jama’a, In ji Chukwuma. Kamar  Nneka, sai wata ƙawarta Liz wadda ke kan ganiyarta a harkar karuwanci a garin Legas ta kira ta, ta nuna mata cewa, in dai tana buƙatar kuɗi, na kece raini, hanya ma fi sauƙi da za su same su, a matsayinsu na mata, shi ne, su baje hajarsu ga mabuƙata, wanda in masu kwaɗayi suka hango za su bumbunto, daga nan ke ma za ki fara cin duniyarki da tsinke.

Binciken da LEADERSHIP A Yau ta gudanar ya nuna cewa, yarinyar ‘yar asalin jihar Ondo ce kuma a halin yanzu tana daga cikin masu shanawa a harkar karuwanci, domin kuwa ta kai ga mallakar motoci na alfarma kamar su; Toyota Corrolla (Sport) da Leɗus RƊ330 sports waɗanda aka kiyasta kuɗinsu a kan sama da naira milyan 4, Elizabeth wanda shi ne asalin sunanta, tana zaune a wani babban gida mai ciki da falo guda uku a unguwar Lekki, wanda biyan kuɗin hayar da ya kai kimanin naira milyan biyu a shekara ba ya zame mata tashin hankali. “Gidan da nake zaune gida ne mai tsada wanda duk wanda ya zo wajena ya san ya zo wajen babbar mace” Liz ke gaya wa wakilinmu wanda ya same ta a wajen wani sheƙe aya  da ake kira Ƙuiloɗ. Wakilin namu ya yi shigar-burtu wanda ya nuna mata cewa, zai haɗata da wani saurayi da ke zaune ƙasar Turai, wanda kuma yake shirin zuwa Legas don ya zo ya ƙaddamar da waƙoƙinsa da kuma fina-finansa, da sigar cewa, an ɗora masa nauyin samo ’yan matan da zai kasance tare da su har zuwa lokacin da zai koma Turai bayan ya gama hidimarsa a Nijeriya.

Ya ce mata, “Mawaƙin zai zo da yaransa guda takwas dukkansu daga Turai”.  Jin haka ita kuma sai ta ce,  “Bayo dama ya gaya mini, saboda haka, ni yanzu a shirye nake duk lokacin da suka shigo, duk kwanan da za mu yi da su, kowane mutum ɗaya zai ba ni naira dubu ɗari da hamsin (N150, 000).Daga nan sai ta tambayi ranar da za su zo wannan ƙasar, saboda ta nemi ɗaki a otal ɗin da za su zauna tun kafin su zo, wadda ta ce, in sun zo za su kama wani danƙareren  otal da ke Ɓictoria Island, na tsawon kwanakin da za su yi. Ta gaya wa wakilinmu cewa, duk sai sun biya kuɗin da za ta caje su, kafin ma ta yarda su fara wata harka da su, Bayo kuma ya tabbatar wad a wakilinmu cewa, Liz da ƙawayenta ba abin ji ba ne, domin za su biya buƙatar da ake nema fiye da yadda ake tsammani. Za kuma ta ba kawalin nata hakkinsa na dukkan ɗawainiyar da ya yi wajen tabbatar wannan al’amari, yadda zai yi farin ciki. Daga nan sai ta ci gaba da bayyana sunayen kawalan da suka yi hulɗa da su wadda ta ce, bayan gama hulɗar sun samu alheri mai kauri a gurinta, saboda ƙoƙarin da suka yi wajen ƙulla hulɗar.

Bayan da ya rage saura kwana biyu wanna mawaƙi da tawagarsa su iso Nijeriya, sai wakilinmu ya kira shi, don ya tabbatar da zuwansa, wanda shi kuma ya ce, “An ɗaga ƙaddamar da wannan waƙa, har sai baba-ta-gani, saboda rashin samun kammaluwar aikin da kuma rashin samun biza a kan lokaci, amma ka yi haƙuri saboda, ban sanar maka da wannan matsala ba a kan lokaci ba”. Ya gaya wa Bayo, ya ce, ya gaya wa Liz, ta yi haƙuri da zarar waɗannan mutanen sun tuntuɓe shi, zai gaya masa.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI