Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Sojoji 4 Da Farar Hula 7 Da Laifin Fashi Da Makami

Published

on

Jami’an tsaron musamman masu yaki da ‘yan fashi da Makami ‘SARS’ sun yi nasarar cafke wasu Sojoji masu sanye da Kaki, wa’yanda ke aiki a Birged na 9 da ke cibiyar Sojoji na Ikeja, da kuma wani korarren Sojan sama guda 1, tare da wasu fararen hula bisa zargin aikata fashi da Makami.

Wa’yanda aka kaman, an ce jami’an tsaron da ke sanye da Kaki ne kan yi musu rakiyar kariya, inda suka gwanance wurin satan Farantan tattara hasken Rana, da kuma Injinan da ke adana hasken na Rana (Inberters). An dai kama su ne a ranar 5 ga Watan Satumba, yayin da gungun nasu suka farmaki Makarantar Sakandaren Okemegba da ke Mojoda Epe a Birnin Legos.

Majiyar mu ta hukumar ‘yansanda ta shaida mana cewa, Sojojin da ke sanye da Kakin, an kama su ne sanye da Kakin nasu na Soji, inda bayan kamun na su, aka damka su a hannun hukumar Soji da ke Birged na 9, a nan aka zartar musu da hukunci karkashin dokokin Sojoji, a take aka kore su daga aikin na Soja.

Majiyar ta mu ta cigaba da bayyana mana cewa, “mun damke Sojojin ne yayin da suke tsaka da aiwatar da aika-aikan nasu, inda ba mu yi wata-wata ba, muka damka su a hannun hukumar Sojoji, aka zartar musu da hukunci karkashin Kundin dokoki na Soja, aka kore su daga aiki, sannan aka sake maido da su hannun mu danb gurfanar da su a gaban Kotun farar Hula”.

“Mun gurfanar da su a gaban Kotun jiya tare da sauran fararen Hulan da muka kama su tare, sunayen Sojojin sun hada da tsohon PTE Busayo, da tsohon PTE Olalekan, da tsohon PTE Usman, yayin da shi kuma korarren Sojan saman sunan sa Odufoye”.

“Su kuma abokan aika-aikan nasu fararen hula sun hada da Ani, dan shekaru 30, da Omorede, da Emanuel, da Odufuye, da Chukwu, da kuma Nwekeoma”.

“Masu aikata laifin, sun farmaki wata Makaranta ne cikin wata Motar daukan kaya mai lamba LLD-61DK, dauke da Makamai, inda kai tsaye suka ballo Farantan tara hasken Rana da ke Makarantar, daga nan suka kutsa kai wurin da aka ajiye Injin da ke adana hasken na Rana, suka sato manyan Baturan Injin guda 2”.

“Dubun su ya cika ne yayin da masu gadi su ka gan su, nan da nan suka sanar da ‘yan banga, su kuma ba su yi wata-wata ba suka sanar da hukumar ‘yansanda”.

“Jami’an ‘yansandan sai suka shirya, suka datse hanyar da ke kaiwa zuwa Garin Epe, inda a nan ne aka yi nasarar cafke Sojojin guda 3, yayin da su kuma ragowar daga baya aka daddamko su a wurare daban-daban bayan da aka gabatar da bincike”.

“Jagoran gungun nasu ya amsa cewa, su ne suke da alhakin babballe Farantan tara hasken Rana da ke kan hanyar da ke zuwa Badagry, sauran wuraren da suka amsa sace Farantan tara hasken Ranar sun hada da, Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Badagry, Sito Tobethromies, Ajara, da kuma wasu wuraren da aka saka manyan Karafunan samar da sabis din Kamfanin Wayar MTN da ke kan hanyar zuwa Lekki, Ajah, Sangotedo, da kuma Eleran Igbe wanda ke kan hanyar Epe”.

Wani mai suna Maduka, wanda ke gudanar da harkokin kasuwancin sa a rukunin Shagunan Kasuwanci na Arena Shopping Compled ne dai ake tuhuma da sayan dukkanin kayayyakin da suka sato, kuma ma shi ake zargi yana daukar dawainiyar su, ta inda yake ba su gudunmawar Kudade.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!