Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Wanda Ake Zargi Dan Boko Haram Da Ya Kashe Dan Sanda A Ekiti

Published

on

A karshen makon da ya gabata ne wani da ake kyautata zato dan kungiyar boko haram ne ya kashe dan sanda a jihar Ekiti.

Sai dai wanda ake zargin, dubunsa ta cika inda ya shiga hannun hukuma. A yanzu haka an aza keyarsa zuwa gidan maza da umarnin koto bisa wannan zargin da take yi masa na kashe Dan sanda a jihar.

Wannan dan Boko haram din ya bayyana sunansa a matsayin, Abdussalam Adinoye kuma bayan ya shiga hannu sai aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare dake Ado Ekiti hedikwatar gwamnatin jihar.

Kuma shi wanda ake zargi Abdussalam din yana da shekaru 36 aduniya ya kashe wannan dan sandan mai mukamin sajan  mai suna Gana alokacin da yake abakin aikinsa na dan sanda  acikin karamar hukumar Oye-Ekiti.

Akan wannan an baiwa alumman najeriya shawara su hada kai da hukumomin tsaro domin asamu akawo karshen fitinar Boko haram akasannan da dukkan masu aikata ta addanci kamar yadda Abdulganiyyu ya fada yace ‘’Dole ‘yan najeriya su gane ce wa gwamnati ita kadai ba za ta iya ta shawo kan matsalar ‘yan ta’adda akasan nanba sai da taimakon jama’a na ko wani bangaren kasannan inji shi’’.

A wani labara kuma daban ajihar Bayelsa wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun yi awon gaba da wani kusa na jamiyyar A.P.C . na jihar musta Robert Desmond sarkin yaki na  wata kungiyar jamiyyar ta A.P.C. a jihar kuma magoya bayan jamiyyar  sun ce suna kyautata tsammanin ‘yan bindigan sun rigaya sun hallaka shi musta Desmond .

Hukumar yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai kuma sun bukaci jama’a su taimaka musu da bayanan sirri da zai kai ga gano mabuyar wadannan masu miyagun ayyuka kuma rahutonni sun bayyana ce wa an sace Mista Desmond ne aranar asabar din makon jiya bayan halarsa wani taro da suka gudanar akaramar hukumar Nenbe dake cikin jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!