Connect with us

WASANNI

Mun Shirya Fuskantar Kalubalen PSG -Zidane

Published

on

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa tuni kungiyarsa ta shirya fuskantar kalubalen kasar Faransa a wasan da zasu fafata a filin wasa na Parc de France a gobe Talata.

Real Madrid dai za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta PSG a wasa na biyu na gasar zakarun turai bayan da kungiyar ta Real Madrid ta doke PSG din a wasa na farko da suka fafata a filin wasa na Santiago dake kasar sipaniya wasan da Madrid din suka samu nasara daci 3-1

PSG dai rabon da tayi rashin nasara a gida tun a watan Maris din shekara ta 2016 wanda hakan yasa kungiyar take da karfin gwuiwar samun nasara a wasan.

Zidane yace zasu buga wasan batare da tsoro ba ko kuma damuwa domin yan wasan kungiyar sun saba samun kansu a irin wannan yanayi kuma sunada yan wasan da zasu jure duk wani yanayi da zasu samu kansu.

Real Madrid dai za ta tafi wasan ne da karfin gwuiwa bayan tasamu nasara a wasan laliga da kungiyar Getafe a ranar Asabar din data gabata.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: