Gobara Ta Lashe Matsugunin Fulani A Kebbi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Gobara Ta Lashe Matsugunin Fulani A Kebbi

Published

on


A jiya ne gobara ta lashe matsugunin falanin da ke garin bawada a karkashin gudumar kambaza karamar hukumar mulkin Gwandu a jihar kebbi a jiya.

Watar gobarar ta tashi ne da misalain karfe 1 na daren jiya sanadiyar iskan guguwa daya tashi a cikin dare da tunanin cewa za’ayi ruwan Sama a ruggar ta Fulanin na garin bawada da ke cikin yakin kambaza a hukumar Gwandu a jihar ta kebbi.

Hakazalika bukokin uku da kuma dukiyoyinsu da zasu kai kimani miliyan daya da kuma daruruwa sun halaka sanadiyar gobarar da ta tashi a cikin dare a ruggar ta falanin a jiya.

Da ya ke bayyana yadda tashin gobarar ya auku a ruggar ta Fulanin garin bawada a jihar ta kebbi, Malam Umaru Ja’eh yace” wannan gobarar ta tashine da misalin karfe daya na dare bayan muna barci sai muka gan hayaki ya tashi a cikin bukokin mu gudu uku bayan tashin guguwa inda muke tsammanin cewa ruwan sama ne sai sauko”. Ganin cewa ba ruwan sama bane sai na nemi dauken jama’ar da ke kusa da mu domin kashe watar.

Har ila yau ya ce, “kafin mu samu ruwan da zamu kashe watar ta lashe dukiyoyin kayan mu da ke kimanin Naira Miliyan Daya da wasu daruruwa a cikin bukokin uku a ruggar ta fulanin garin bawada.”

Hakazalika Umar Ja’eh yace “ rashin bamu da ma’aikatan kashin gobara yasa mun samu asarar kayan mu da kuma bukokin mu”.

Bugu da kari yace “ babu asarar rayuwa ta mutanen ko ta dabbobi sai dai asarar kayan mu da kuma bukokin uku.

Daga karshe yayi kira ga gwamantin jihar kebbi da kuma hukumar da abin ya shafa domin taimaka muna da gudumawa na tallafi kan asarar da mukayi ta dukiyoyinmu na Kaya da kuma matsugunin.

Tijjani Baba Gamawa Ya Nemi A Inganta Rayuwar Talaka A Hukunta Masu Laifi A Nijeriya

An bayyana rashin inganta rayuwar talaka ta hanyar samar musu da walwala a fannoni dabam dabam na rayuwa a matsayin wata hanya da za ta cigaba da haifar da matsaloli a Nijeriya, musamman ganin yadda ake cigaba kama wadanda ke haddasa fitina a Nijeriya ba tare da ana hukunta masu laifi ba.

Tsohon mai ba gwamna shawara na musamman a Jihar Bauchi Air Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya shine ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilin mu a Bauchi, inda ya kara da cewa abin takaici ne yadda a kullum ake samun tashe tashen hankula a Nijeriya da kuma aikata laifuka ta hanyar mu’amala da manyan makamai, amma har zuwa wannan lokaci lamurran kara ta’azzara su ke yi madadin a samu dakile su, don a samu ci gaban zaman lafiya da walwalar jama’a a Nijeriya.

Air Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya ya ce abubuwan da ke faruwa a Nijeriya ba su da dadi kuma kowa yasan abin da ke faruwa dole ya nuna damuwa, duk da cewa gwamnati na iya kokarinta dole ta yi wa mutane adalci ta rike gaskiya a rike amana a tabbatar kowa ya rike gaskiya kuma mutanen kasa da shugabanni dole a fadawa juna gaskiya a fuskanci gaskiya don a samu ci gaban lamurra.

Ya ce abubuwa da dama sun faru kamar wasa musamman game da harkar da ta shafi tsaro, amma an wayi gari lamurra na nuna kamar za su fi karfin gwamnati, don haka ya zamo wajibi a tashi tsaye a magance irin lamurran da ke faruwa don a samu ci gaban zaman lafiya, ta hanyar neman shawarar masana don yin abin da ya dace saboda a daina zubar da jinin bayin Allah.

Ya ce abin mamaki ne wuta na tashi nan na tashi can dole mutane su marawa gwamnati baya kowa ya yi kokarinsa a ba jami’an tsaro bayanai game da abubuwan da ke faruwa cikin al’umma don ba za su iya yin komai su kadai ba dole sai sarakuna da mutane kowa ya ba da gudummowar sa kafin a cimma nasara.

Ya ganin irin halin da ake ciki game da yadda a ka tozarta wassu al’ummomi wasu aka raba su da rayukan su, gwamnati dole ta hukunta mai laifi kuma wanda aka cutar a mayar masa hakkinsa a ba shi hakuri. Amma idan aka wayi gari mutane na haifar da husuma tare da kashe mutane a kowane wuri ba tare da an hukunta masu laifi ba to dole za a ci gaba da samun matsaloli a kasar nan da rashin daidaito ko yafewa juna tsakanin kabilu da aka jima ana zaune tare.

Don haka ya bayyana cewa matukar ana son kasa ta zauna lafiya dole shugabanni su tsaya su jajirce wajen ganin an hukunta mutane da suke haifar da fitintinu a kasar nan don su zamo misali ga duk wanda ke da nufin yin abin da ya kauce wa dola, don gobe wani ba zai yi nufin aikata laifi ba.

Don haka ya ce dole shugabanni su jajirce su yiwa mutane adalci, kuma duk da kokarin da gwamnati ke yi dole a tashi kan matasa a tabbatar sun samu abin yi don lamarin akwai barazana yadda matasa ke zaune babu ayyukan yi basu san tudun dafawa ba.

Baba Gamawa ya kara da cewa ya zamo wajebi a yiwa kasa addu’ah don samun zaman lafiya da cigaba mai albarka, haka kuma ya nemi a hukunta masu laifi a duk inda suke don a dauki darasi daga wadanda aka kama da laifi kuma aka bayyana laifukan su aka tura su kotu ta musu hukunci.

Amma idan mutum ya yi laifi ana kallo aka kyale shi ba tare da an hukunta shi ba to wasu za su bi suma su ci gaba da haifar da matsala saboda sun san idan suna da farcen suka duk barnar da suka yi ba wani mummunan hukunci da za su fiskanta.

Ahmed Tijjani Baba Gamawa ya kara da cewa abubuwan da ke faruwa a kasar nan basu da dadi don haka dole a lura wajen ganin masu mulki sun daina tozarta mutane tare da kawar da masu gaskiya idan suna son a zauna lafiya. Idan kuma ba haka ba akwai lokacin da zai zo talakawa za su yanke hukunci wajen kin zabar duk wanda ya ki musu adalci da jagoranci na gari wajen nuna gaskiya da yin aikin da ya dace don ci gaban jama’a.

Saboda haka ya zamo wajibi shugabanni su fahimci cewa mutane suna cikin wahala kuma dole a duba halin da suke ciki don a inganta rayuwar su saboda suma mutane ne ba bayi ba kuma suna da bukatar rayuwa cikin walwala da ’yanci kamar kowa.

Hukumar Shige Da Fice Ta Damke Bakin Haure 67 A Mashigin Neja

A kokarinta na tabbatar da tsaron kan iyaka domin hana haramtattun baki silalowa cikin kasar nan, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta damke bakin haure 67 ‘Yan Nijer.

Dakarun hukumar na musamman masu sintiri a kan iyakar Nijeriya da Nijer suka damke bakin hauren ta mashigin Jihar Neja.

Sanarwar da jami’in yada labaran hukumar ta NIS, DCI Sunday James ya raba wa manema labaru, ta nunar da cewa Babbar Jami’ar Hukumar reshen Jihar Neja, Misis Hornby ta bayyana wadanda aka cafken.

Sanarwar ta ce nasarar da aka samu ta damke bakin hauren ta biyo bayan taron da shugaban hukumar, Muhammad Babandede, ya yi da shugabannin manyan shiyyoyi da jihohi da kuma sassan hukumar na kan iyakoki, filayen jirgin sama da kan iyakoki na ruwa ne inda ya hore su su kara matsa kaimi a bakin aikinsu domin tabbatar da cewa ba a bar duk wanda ba Dan Nijeriya ba ya jefa kuri’a ko tsayawa takarar zabe kamar yadda yake kunshe a tsarin mulkin kasa.

Har ila yau, nasarar ba za ta rasa nasaba da sabon yunkurin shugaban hukumar ba na tabbatar da shigar da al’ummomin da ke kan iyakokin kasa cikin sha’anin tsaron kan iyaka inda shugabannin al’ummomin ke taimaka wa jami’an hukumar da bayanai.

Damke bakin hauren ‘Yan Nijer 67 a kan mashigin Jihar Neja alama ce ta sabon yunkurin na Muhammad Babandede ya fara haifar da da mai ido.

Sanarwar ta ce tuni aka dauki bayanan bakin hauren kuma za a tasa keyarsu zuwa kasarsu.

Shugaban hukumar, Muhammad Babandede ya bukaci sauran shugabannin sassan hukumar su yi koyi da shugabar reshen Jihar Neja, CIS Hornby da jami’an sintirin kan iyakoki wadanda suke aiki tukuru tare da kara kaimi bayan Kwanturola Janar din ya ba su sababbin motocin sintiri a kwanan baya.

Idan za a iya tunawa dai, a kwanan baya Hukumar Shige da Ficen ta yi kawance da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) domin tabbatar da cewa babu wani bako daga waje da aka bari ya kada kuri’a a zaben 2019 da ke tafe idan Allah ya kai mu.

Advertisement
Click to comment

labarai