Matan Chibok 15 Kacal Ke Raye A Hannun Boko Haram –Salkida — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Matan Chibok 15 Kacal Ke Raye A Hannun Boko Haram –Salkida

Published

on


Ahmad Salkida, dan jarida ne wanda yakan shiga tsakani a kokarin kawo sulhu tsakanin gwamnatin Nijeriya da kuma kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram, ya fadi cewa, kawo yanzun cikin yara mata ‘yan makarantar Chibok, 113 da suka saura a hannun ‘yan Boko Haram din, 15  ne kadai suka saura da ransu.

A cikin wasu tattaunawa da ya rika sakowa a shafinsa na, ‘Twita,’ Salkida, ya kara da cewa, su ma 15 din da suka saura duk an rigaya an aurar da su, an kuma shigar da su cikin kungiyar ‘yan ta’addan ta Boko Haram, da wuya ma su so dawowa wajen iyayensu a halin yanzun.

Ya shawarci gwamnati kan tattaunawar da ta ce tana yi don a sako sauran 15 din, da ta bukaci a nu na mata tabbacin su a raye kafin ta ci gaba da tattaunawar.

“Shekaru hudu da suka wuce, wani matsakaicin Kwamanda na kungiyar ta Boko Haram, ya jagoranci wasu gomomin maharan kungiyar ta Boko Haram, inda suka fito neman abinci da sauaran ababen bukatu na yau da kullum, a kauyan na Chibok. Zuwan da suka yi ne kuma sai suka ga sararin su sace ‘yan matan makarantar ta Chibok, wadanda suke makarantar a lokacin domin su rubuta jarabawarsu.

“Maharan sam ba su sami wata tirjiya ko kalubale ba a duk tsawon lokacin da suka kwashe a makarantar suna sace yaran, inda suka lula da yaran da suka kamo can cikin dajin Alagarno, watau Shalkwatar kungiyar ta Boko Haram ta farko, wacce suke kiran ta da Timbuktu. A nan inda suke kira da Timbuktu din ne suke shirya duk wasu hare-haren da suke kaiwa.

“A daren, wasu daga cikin ‘Yan matan sun sami nasarar tserewa kafin su isa Timbuktu din, kasantuwan ‘yan ta’addan da ke masu rakiyar ba su da yawan da za su iya kulawa da daukacin yaran da suka haura 200. Da farko, su kansu ‘yan Boko Haram din ba su ma san me za su yi da ‘yan matan ba, akalla a watan farko da suka saci yaran.

“Wani abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, a sati biyun fakon lokacin da aka sace ‘yan matan, gwamnatin tsohon Shugaban kasa Jonathan, ta tuntube ni kan neman hanyar lalaman da za a bi domin a sako ‘yan matan. Duk da a lokacin ina gudun hijira a wajen kasarnan, sakamakon matsin lamban da ita dai gwamnatin ta Jonathan ke yi mani.

“Duk da hakan, sai na nemi izini daga wajen da nake dan taba leburanci na a can Daular Larabawa ta tsakiya, (UAE), (duk da ina aikin a can, ina kuma kawo rahotannin ‘yan ta’addan) domin na zo na gana da Shugaban kasan na wancan lokacin, ganarwar da, Aliyu Gebi, da kuma Labaran Maku, suka shirya ta, a ranar 3 ga watan Mayu, ina kan hanya ta daga Abuja zuwa Madagali, Marwa har dai na isa matsugunin na ‘Yan Boko Haram. Na kawo ma Shugaban kasan, hujjojin da suka tabbatar masa da cewa, ‘yan matan suna nan a raye, na kuma baiwa manema labarai wata shaidar, domin kila ko ba zan sami dawowa da raina ba.

“A lokacin, fansar da ‘yan Boko Haram din ke nema ba mai wahala ce ba. So kawai suke a kai ‘yan’uwansu da aka tsare Damaturu, su kuma za su kai ‘yan matan Bunu Yadi, domin a yi musanya a wajajen. Sam ba su ambaci kudi ba ma. Sai aka ba ni cikakkiyar rakiya da Jami’an Sojoji, daga Abuja zuwa Damaturu.

“An shirya cewa, gwamnati za ta tabbatar ta kai kamammun ‘yan Boko Haram din 70 Damaturu ne da zaran na isa can, domin na kuma sadu da wasu guda 30 a can din. sauran mutanan da muke aikin sasantawan da su duk suna Abuja, domin tabbatar da sun sako 70 din a cikin Jirgin sama kafin ma ni na isa Damaturun, sai dai shi Kwamandan Sojin da ke Damaturun, ba a sanar da shi abin da zai kawo ni ba. An dai shaida ma shi cewa, yana da babban bako ne kadai.

“A lokacin, har su ‘yan Boko Haram din, sun kai ‘yan matan can inda aka alkawarta, amma sai ba su ga an kawo mutanan na su ba da za a yi musayan da su, a kuma daidai wannan lokacin ne Kwamandan Dakarun tsaro na kasa, ya kira ni a waya, yana shaida mani, an fasa shirin. Amma daga bisani, Shugaban kasan ya shaida mani cewa, ba da yawunsa ne aka ce an fasan ba. Tabbas an sami daman kubutar da yaran a lokacin, sai dai ba a mayar da hankali ne ba kawai. Hakan ya sanya su ‘yan Boko Haram din suka fusata. Ni kuma na koma bakin aiki na a can UAE, amma na ci gaba da samun gayyata, ba daga waccan gwamnatin ba kadai, hatta wannan gwamnatin ma ta yanzun, wacce ta neme ni a kan shiga tsakani hudu daga cikin biyar din da na yi, sai mun yi kusa da cimma yarjejeniyar musayar, sai gwamnati a mafi yawan lokuta ta yi sakaci da lamarin, a duk lokacin da gwamnatin ta yi sakaci, sai shi kuma Shekau, ya canza salo.

“Na ci gaba da kawo rahotannin rikicin, a wasu lokutan, na kan sami tsangwama daga gwamnati da kuma Boko Haram din. ban damu ba, domin na san aiki na kawai nake yi, na mai bayar da rahotanni, da yawa daga Jami’an gwamnati sun dauke a matsayin wani abu na daban, mai bayyana abin da a zaton su kamata ya yi a yi shi a boye. Sai gwamnati ta fara neman wani ba ni ba, wanda zai karasa abin da ni na soma shi, a nan ne ‘yan sakona na baya suka shigo, inda suka kasance, sabbin masu shiga tsakanin.

“Ni hakan ma sai ya kasance sauki ne a gare ni, wani dalilin kuma shi ne, na dagewa na kan cewa, lallai a nan gida ne ya kamata mu warware lamarin. Sai na kasance kamar wata kaya a cikin jikin shugabanni na, saboda yadda in sun fito sun ce ga yanda abin yake, sai ni kuma na ce ba haka abin yake ba. Washegarin ranar da na saki wani faifan bidiyo na ‘yan matan, abin da na kan yi hakan a baya. Sai Sojojin da suka ba ni rakiya, na Sojoji da ma jiragen sama domin na je na aiwatar da aikin nawa, sai na yi mamakin wai sun shelanta nema na, daga baya sai na  yi mamakin ashe sharuddan da na gabatar masu ne tun da farko na sakin ‘yan matan bai yi ma wasun su dadi ba, kamar yadda wani aboki na ne ke cewa, ko da ka zo da mafita, masu cin moriyar yakin da kuma masu jin cewa sun san komai, sun gwammace su mutu, da su amshi wannan mafitar da talaka zai sami sauki.

“A yau din nan, binciken da na yi wanda sakamakon sa ba dadi, ya tabbatar mani da cewa, ‘yan kadan ne daga cikin ‘yan matan Chibok,  113 da suke hannun su suka saura da ransu. Yawancin ‘yan matan duk sun mace, sakamakon musayar wuta da kuma bamabaman da Jami’an tsaro suka rika jefa masu, wadanda ina da tabbacin, ba sun jefa masu ne domin su kashe ‘yan matan ba, sun jefa ne domin su ceci ‘yan matan. Ina mai bakin cikin shaida maku, yara 15 ne kacal daga cikin 113 nan suke da rai a halin yanzun, a bisa binciken da na yi, cikin watanni ukun nan da suka shude, mun kuma ga wasu daga cikin su a cikin faifan bidiyon, wanda ni na san yanda na samo shi, na kuma saka shi a shafin yanar gizo na Sahara.

“To yanzun a wane hali ne ma sauran 15 din suke ciki, kan tattaunawan da ake yi? Bincike na ya nu na mani cewa, su ma din yanzun ba suna karkashin ikon Shekau ne ba.

“Majiya ta, ta tabbatar mani duk an aurar da su, mazajen su ne kadai za su iya yanke hukunci kansu, sai dai in mazan na su sun sake su ne ko an kashe mazan na su ne Shekau zai iya wani abu a kansu. Amma a haka da kuma suka zama ‘ya’yan kungiyar, shugaban su ba shi da hurumin wata tattaunawa domin sakin su, ko da kuwa nawa ne za a biya, majiyoyi da yawa, sun ce bai dace ba a bayyana sunayen 15 din da suka saura a nan, hakan aikin gwamnati ne. a lokacin da ake yi da ni, kowane lokaci na kan zo da hujjan tabbatar da kasancewar su a raye.

“Gwamnati ta daina batun tattaunawa kan ‘yan mata masu yawa, wadanda duk ba su a raye. Kumbiya-kumbiyan da ke tattare da halin da ‘yan matan Chibok da ma na kwanan nan, ‘yan matan Dapchi, ke ciki, da wadanda ake shirin tattaunawar da su, shi ne dalilin da ya sanya mutane ire-ire na ba a yi da su. Gaskiyan magana ita ce, a wannan halin ba wata dama ta yin sulhu.

“Mafita guda ta wadannan ‘yan matan ita ce, ko dai a yi amfani da karfin Soja, ko kuma a tattauna da mazajen su, su sako matan na su, a bisa wata yarjejeniya, wanda hakan ke nufin in an kashe mazajen ne kadai, domin ‘yan ta’addan ganin ‘yan matan suke a matsayin wasu daga cikin su, wadanda ya zama tilas su ba su kariya.

“Ta ya zai kasance ba wani labarin da ake samu na ‘yan matan, sannan kuma iyayen su da masu fafutukar a sako su, duk ba su ma san halin da ake ciki ba? Dalili shi ne, gwamnati ba ta yarda da kawo rahotannin rikicin ba, yawancin hanyoyin kawo rahotannin, duk nata ne wadanda ta tsara su, sannan kuma ‘yan Nijeriya ba su shirya sauraron gaskiya ko bin gaskiyan ba. Kawo labaran wannan rikicin na tafkin Cadi, ba aiki na ne ni kadai ba, Borno Jiha ta ne, wannan rikicin ya shafe ni, shekaru 13 daga cikin shekaru 18 da na yi a aikin jarida, duk na yi su ne wajen kawo labaran wannan rikicin, abin da ba wani dan jarida ko mai binciken da ya aikata hakan, don haka bai kamata a yi watsi da abin da na fada a kan wannan rikicin ba. Na sadaukar da rayuwa ta, da ta iyalai na, a baya da ma yanzun, ba kawai wajen kawo labaran ba, har kasantuwa na mai shiga tsakani da kuma mai binciko gaskiyan lamarin.

“Amma a lokacin da gwamnatin tarayya ta sami wata hanyar ba ni ba, sai aka yi watsi da duk sadaukarwar da na yi, ana ma yi mani bita da kulli. Ba ni da wata boyayyar manufa da ta wuce ta ganin na shiga tsakani na kuma bayar da karin haske ga iyayen yaran nan.

“Bai kamata kasan nan ta hana ku ceto ‘ya’yanku ba, bai kuma kamata kasan nan ta kasa shaida maku gaskiyan lamari ba. Ina bakin ciki da taya iyayen yara kusan 100 da suka mutu ko kuma ba su dawo gida ba juyayi,. Tilas ku rika tuna cewa, ‘ya’yan naku sun fi da yawa daga cikin mu karfin hali, wanda ba abin da za su iya su kaucewa wannan azal din da ta fada ma su.”

 

Advertisement
Click to comment

labarai