Yunwa Ta Hallaka Yara 150 Cikin Shekara Daya A Gombe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yunwa Ta Hallaka Yara 150 Cikin Shekara Daya A Gombe

Published

on


Rashin samun isasshen abinci ya kashe Yara akalla 150 a Jihar Gombe a cikin shekarar da ta gabata wato 2017.

Wannan al’amari ya faru ne a ya yin da ake aikin kula da lafiyar Yaran a cibiyar kula da masu cutar yunwa dake kananan hukumomi hudu na jihar.

Wani babban Jami’i mai kula da wannan sashen na Jihar ne mai suna Suleiman Mamman ya bayyanawa majiyarmu hakan a makon jiya.

Mamman ya bayyana cewa a cikin shekarar 2017, Yara dubu sha hudu da dari da arba’in da uku (14,143) ne suke fama da wannan cuta a cikin Jihar a tsakanin cibiyoyin kula da masu cutar yunwa a kananan hukumomin Gombe da Nafada da Dukku da kuma Kaltungo.

Ya ce cikin wannan adadin, Yara 13, 069 ne an ci nasarar kula da lafiyarsu inda a karshe aka sallame su. Sai dai ya ce; Yara 710 kuwa ba a iya cimma nasarar kula da su ba sakamakon daina zuwa da su da iyayensu suka yi wanda su kadai suka san dalilin haka.

Ya ce; Yara 150 kuwa, ajalinsu ya cika ne a ya yin da ake nema musu lafiya. Sannan Yara 214 ba a iya cimma nasarar kula da lafiyarsu ba sakamakon wasu dalilai masu karfi da suka sha karfinsu.

Ya ci gaba da cewa; Yaran da ba su warke ba, an ba su kulawa ta akalla wata takwas amma duk da haka babu wata ci gaba da aka samu.

Masanin ya daura da cewamafi yawansu suna da cutar kanjamau, a wannan dalili ya sa an tura su wasu asibitocin daban-daban a cikin jihar domin kula da su.

Hakazalika, Kwamishinan lafiya na Jihar Gomben, Kennedy Ishaya ya bayyana cewa; “jihar Gombe tana daya daga cikin jihohi takwas a kasar nan da aka ba su bashi a Bankin duniya domin su kawo karshen matsalar cutar yunwa.”

Ya kara da cewa; “gwamnatin jiha ta kammala dukkan shirye-shirye domin ganin mun sabunta dukkanin cibiyoyi da asibitocin da suke kula da wannan al’amarin a jihar, inda muka fara da asibitin jiha na musamman wanda yake bukatar da ga darajarsa.”

Kwamishinan ya bayyana cewa; sakamakon yadda ake kara samun hauhawar masu wannan cutar a kasarnan musamman ganin yadda ake samun tashe-tashen hankula a arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, wannan ya nuna cewa akwai hadarin gaske wajen samun karancin abinci a shekara mai zuwa in dai ba a gabatar da wannan matsalar ba domin ganin an kawo karshenta.

A zancensa ya ce; tuni aka samar da wani Ofishi wanda za a samar masa da mai gudanar da shi wanda ba da jimawa za a bayyana ayyana shi.

Ishaya ya ce; kalubalen a Nijeriya ba wai saboda rashin abinci bane, illa rashin sanin me ya kamata a rika samarwa na abinci a kasar.

Ya tabbatar da cewa; hukumarsa zata duba wannan lamarin domin ganin sun hada hannu da karfe da wasu hukumomi da kungiyoyi domin ganin sun kawo karshen yunwa a Jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!