Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yadda Aka Harbe Wata Mata Dake Zaman Makoki A Enugu

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta fara gudanar da bincike akan zargin  harba bindiga a makabar ta, inda hakan ya janyo mutuwar wata mata mai zaman makoki wani kuma ya samu rauni.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar  Ebere Amaraizu ya tabbatar da hakan a sanarwar da rundunar ta fitar a Enugu ranar Asabar din da ta gabata.

Amaraizu ya ce, lamarin ya auku ne a yankin Amanato Mburumbu dake karamar hukumar Nkanu East, inda ya ce, an samo bindigar da makeran gida suka kera a makabartar.

Amaraizu ya sanar da cewar, hadarin ya rutsa da mace da wadda take zaman makokin.

An ruwaito cewar, lamarin ya auku ne  a lokacin da wani mutum da ake kira Daniel Chukwu dake zaune a yankin ya shigo makabar tar a lokocin yana dauke da bindigar bayan bai ankare cewar bindigar take shirin tashi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: