Bahaushe Mai Ban Sha’awa (2) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Bahaushe Mai Ban Sha’awa (2)

Published

on


Ra’in fushin huce haushi (Frustration-Agression Hypothesis)

08065533969

saboahamad@gmail.com

A fagen kari magana, akwai wata Karin maganar da Bahaushe ya yi, wadda yake cewa ‘Kumburi gadoki, sakiya ga jaki’, ko kuma ya ce, ‘Ba ni na kashe zoman ba, rataya aka ba ni’ wadannan karin maganganu duk ma’anarsu daya ce, kuma sun yi daidai da ra’in malaman halin dan’adam, ra’in da suka lakaba wa suna ‘Frustration-aggression hypothesis’ ko ‘scape-goat theory’, wanda za mu iya fassara shi da ra’in fushin huce haushi.

Bahaushe yana yin daya daga cikin wadannan karin maganganu a lokacin da ya fahimci cewa, ga hakikanin mai laifi amma sai aka kyale shi aka yi hukunci ga wanda ba shi ya aikata laifin ba, saboda ko dai ana jin tsoro wancan mai laifin, ko kuma, an raina marar laifin. Misali, hakikanin mai kumburi a kafa shi ne doki, wanda shi ya kamata a yi wa sakiya, amma saboda darajar da doki ke da ita, sai aka yi wa jaki sakiyar, saboda raini, alhali ba shi ke da kumburi a kafar ba.

Malaman halin dan’adam sun yi bincike mai tarin yawa a kan irin wannan halin na dan’adam. Akwai binciken da suka yi a kan beraye wadanda suka tsare su a cikin keji, suna zuba masu abinci lokaci-lokaci. To, ran nan sai suka bar su da yunwa, suka ki sa masu abinci kamar yadda aka saba. Maimakon a saka masu abincin sai aka saka masu dutse. Ganin an sanya masu wani abin da ba abinci ba, sai berayen nan, suka fusata, suka kama cizon dutsen, suna tunkurinsa da kai, suna fatali da shi. A nan, hakikanin mai laifi shi ne wanda ya ki sa wa berayen nan abinci, amma saboda ba yadda za su huce hushinsu a kansa, sai suka huce a kan dutse, wanda ba shi ne mai laifi ba.

Shi ma Mukharjee, ya bayyana cewa, ana samun fushin huce haushi a lokacin da ake wasan kwallo tsakanin tim biyu. Idan aka ci wani tim. Sai ka ga magoya bayan tim din da aka ci sun kama karya kujerun da suka zauna, suna farfasa gilasan motar da duk suka ci karo da ita a kan hanyarsu ta komawa gida. Saboda haka, Bahaushe ya zama mai ban sha’awa, ganin yadda in ya yi karin magana, sai ta yi daidai da ta Maluman Birnin Zazzau wato daidai da ta Malaman Kimiya wadanda suka nazarci abin a kimiyance shekara da shekaru.

 

Ra’in ja ni-mu je (Stimulus-Response Theory)

A wani labarin baka na Bahaushe akwai labarin wata matar da ta je wajen wani malamin, da nufin ya tamake ta, ya ba ta asirin da za ta mallake mijinta ta yadda duk abin da ta ce masa zai aikata. Da matar ta je gun malam, sai ya ce mata, ta je cikin daji, ta samo nonon bauna. Kowa ya san yadda bauna take da fada, musamman in ta ga mutum kusa da ita sai ta sa kaho to soke shi ta jefar da shi gefe daya, ta bi shi, ta tattaka har sai ta ga ya mutu.

Da malam ya dage a kan cewa lalle sai ta samo nonon nan, sai matar ta yi kuru, ta yi ta maza, a inda ta samo dusa ta zuba a kwarya ta je cikin dajin da ake samun bauna ta ajiye kwaryar dusa a kan hanyar da bauna ke bi, ita kuma, ta tafi gida abinta. Haka ta ci gaba da yi, wata da watanni. Kullum matar nan ta je sai ta iske bauna ta cinye dusa. Ana nan ran nan, sai ta ajiye kwaryar dusa, ta koma nesa da inda Baunar take. Ana haka, kullum matar nan na matsawa kusa da bauna, a lokacin da Baunar ke cin dusa har dai wata rana ta kai tana shafar bauna, Bauna na cin dusa, ba ta yi wa matar nan komai ba, saboda ta san ita ce ke kawo mata abinci.

A haka, har ran nan, matar ta tatsi nonon bauna, ta kawo wa malam. Da malam ya ga tabbas nonon bauna ne, sai ya ce wa matar, da ma, ba wani magani zai hada mata da nonon ba. Ya yi haka don ya nuna mata cewa, yadda ta hanyar lalama, da rarrashi, da lallaba, da nuna so da kauna, har ta sa bauna ta amince da ita, har ta bari ta tatsi nononta, to, in, ta yi wa mijinta haka, za ta mallake shi. Zai mata duk abin da take bukata daga gare shi.

Wannan labarin baka na Bahaushe, ya yi daidai da ra’in masana halin dan’adam na ‘Stimular-Response Theory’ wanda za mu iya fassara shi da Ra’in ja ni-mu je. Masana halin dan’adam, sun yin bincike iri daban-daban da beraye da kyanwa,  inda suka gano cewa, za a iya jan halin dabba, har ma da mutum zuwa ga aikata wani aiki, idan akwai wata biyan bukata. Wato, in akwai wani alfanu na abinci, ko kuma abin da dabba ko mutum ke so, to zai iya yin abin da ake so ya yi.

A bincike-bincike malaman, sun sa kyanwa a cikin keji, wanda a cikinsa akwai wani dan mabudi wanda in aka danna shi wani sashe na kofar kejin zai bude, a sami nama a jiye. To, kullum sai su ajiye nama a sashe guda na kejin ita kuma kyanwa,da ta ga nama, sai ta kama tsalle-tsalle da karce-karce, har dai a karshe, ta kai ga taba  dan mabucin da ke bude sashen da naman yake ajiye ta ci abinta ta koshi. A haka har a hankali ta gane cewa, ba sai ta bata lokacinta tana tsalle-tsalle, ko karce karce, kafin ta kai ga abincinta ba. Abu daya da ta yi, na taba wancan mabudin. Shi ke nan, da an sa mata nama, sai kawai ta taba mabudi, sai kofa ta bude, ta ci namanta.

Masana halin dan’adam irin su Pablor, Thornduk, Guthrie, Hull da Skinner, su ne masanan da suka shahara a duniya wajen ra’in ja ni-mu je, kuma duk sun tabbatar da wannan batu na jan hankalin dan’adam da dabba wajen koyon abubuwa, ko sa su aikata wani aiki.

Labarin mata da malam, ya nuna mana cewa, shi ma Bahaushe, tsohon masanin ra’in ja ni-mu je ne. akwai ma wasu karin maganganu da Bahaushe ke yi, wadanda suke kara tabbatar da wannan ra’i, inda yake cewa, ‘sabo turken wawa’ . Akwai kuma ta, ‘yaro da gari abokin tafiyar manya’. Wato. In ka saba wa mutum da wani abin da yake so, za ka turke shi, ka rika sarrafa shi yadda kake so. Haka ma Bahaushe ke nufi, a inda ya nuna cewa, in yaro yana da abin hannunsa, kuma yana sakin abin hannu yana ba da kudi, ko abinci, ko dai abin da manyan mutane ke so, sai yaron ya zama abokin tafiyarsu duk da kasancewarsa yaro. Bahaushe mai ban sha’awa

 

Kammalawa

Bayanan da suka gabata sun tabbatar mana cewa, Bahaushe tsohon masanin kimiyar halin dan’adam ne ganin yadda in ya karin magana, ko ya sa wata magana cikin kirari,ko adon magana sai abin da ya ce ya yi daidai da na malaman kimiya. Bahaushe yana yin wadannan maganganu don su zama jagora, don fadakarwa bisa ga halin rayuwa ta yau da kullum. Misali, ta Ra’in ja ni- mu je na Bahuashe yana son ya nuna wa jama’arsa cewa, nuna so da kauna ga matashi, su ne muhimman abubuwan da ya kamata a rika yin la’akari da  su, fiye da nuna tilasci, ko yin kankanci.

Bahaushe yana nuna wa jama’arsa cewa lokacin kuruciya, lokaci ne mai hadari ga ‘ya’ yanmu mazansu da matansu, saboda haka, sai an rika yin taka-tsanstan wajen tafiyar da lamarinsu. Wajibi ne a rika sama wa matasa aikin yi, inda a nan za su yi amfani da karfinsu da basirarsu da ke ginuwa. Rashin yin haka, shi ke sa su fada cikin tarzoma da tayar da hankalin jama’a. Mutanenmu na dauri, sun fi fahimtar hadarin kuruciya, saboda haka, da sun ga yaro ya balaga, sai a fara yi masa tanadin sana’a wadda iyayensa ke yi, ko kuma wadda mutanen garinsu ke yi. Saboda haka ne a da, ba matashi mai zuman banza. Za ka sami matashi yana kira ko rini ko gani ko dinkin hannu, ko aikin lambu, ko dai wani abu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai