Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Hatsari Ya Ci Rayuwar Dalibai Biyar Na Kwalejin ’Yan Sanda

Published

on

Daliban makarantar horar da ‘yan sanda da ke Wudil, a jihar Kano su biyar da wasu fasinjoji guda biyu ne suka rasa rayukansu a jiya Lahadi a sakamakon wata mummunar hatsarin mota da ta auku a kan babban hanyar Kano da Zariya.

Daliban wadanda suka fito daga makarantar tasu na ‘yan sanda, inda suke kan hanyar koma gidajensu domin hutun zango da suka samu.

Hatsarin ta auku ne da wata mota kirar Golf inda ta samu suka karawa da wata mota kirar J5 a lokacin da suke tsaka da tafiya a kan titin.

Wani ganau ya shaida mana cewar a bisa karawar da motocin suka yi wanda hakan ya janyo ita golf din ta yi daje ne ya janyo mutuwar, inda a cikin wadanda suka mutu har da daliban biyar.

Majiyarmu ta ci gaba da shaida mana cewar, hudu daga cikin dalibai maza ne, kuma dukkaninsu ‘yan Zariya ne, inda kuma mace daya ita ma dalibar kwalejin horar da ‘yan sandan, wacce ita kuma gidansu ke Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: