Jam’iyyar PDP Ta Yi Kyakkyawan Tanadi Don Mata (II) -Halima Kajuru — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Jam’iyyar PDP Ta Yi Kyakkyawan Tanadi Don Mata (II) -Halima Kajuru

Published

on


Wace riba kike ganin mata sun samu a gwamnatin PDP wacce kike ganin ba su same ta ba a wannan gwamnatin?

Mata sun taka mahimmiyar rawa a lokacin gwamnatin PDP, hakanan ita ma gwamnatin ta PDP ta taka masu mahimmiyar rawa. A wancan lokacin na mulkin Jam’iyyarmu ta PDP, kama daga kan Uwargidan Shugaban kasanmu har ya zuwa matan gwamnonin mu, duk sun bude ayyuka da kuma hanyoyi kala-kala wadanda matan suka ci gajiyar su. Mata a wancan lokacin sun karu ta misali a koya masu sana’a, a kuma ba su jari, an kuma ba su mukamai manya-manya har ma da kananan tamkar takwarorin su maza.

Misali a nan, ni a karamar hukuma ta da na fito, watau Kajuru, Mace mawuyaci ne a baya can ta iya zama kansila in ana zabe. sai muka sami matar gwamnan mu na PDP a wancan lokacin muka ce ma ta, to ko a mukaman nan na rikon kwarya da ake sanyawa, a daure a sanya mata mana. Muka ko yi sa’a, ta yi wa mijinta magana, ya kasance a duk karamar hukumar da aka nada kansiloli hudu sai da aka sanya mace guda. Don haka take a lokacin, sai da muka samu mata 23 a nan Jihar Kaduna sun yi kansila. A mataki na tarayya kuwa, Shugaban kasa ya baiwa akalla mata takwas mukaman Ministoci. An kuma baiwa matan mukaman shugabancin manyan ma’aikatun gwamnati da dama, ba kuma wata Majalisar da za ka je, in ka debe kamar irin su Kano haka, sabili da al’adunmu da kuma Addini, amma duk Majalisunmu akwai mata a cikin su. Amma hatta a nan Kaduna, a kan sami mata uku har ma hudu a Majalisa, amma yanzun fa? Ai ka ga babu mace ko da guda a cikin majalisa. Sam mata ba su da murya ba kuma su da wakilci a cikin majalisa, ba mace wacce ta san wane hali ne mata ke ciki ballantana ta taimake su, don haka matan ke shan wahala matuka a wannan gwamnatin. Ba wani abin da ake yi masu ko da kuwa da sunan tallafi ne, su dai suna nan a cikin gida kawai ajiye.

Sun ta fi sun bar mata a baya, amma dai mu a PDP muna nan tare da mata, hatta wannan zaben na kananan hukumomi da za a yi a Kaduna ranar 12 ga wannan watan, a shiyyan da na fito kadai, watau shiyya ta biyu, sai da muka yi kokari muka tabbatar da cewa mata har uku sun ci zaben fidda gwani a cikin Jam’iyyar mu, biyu a Chikun daya kuma a Kajuru, da kuma izinin Allah da karfin kuri’ar da za mu jefa masu za su lashe zabukan na su.

 

Yanzun wane fata ne matan ke da shi in har da Allah zai baiwa Jam’iyyar taku ta PDP sa’a ta sake dawowa kan karagun mulkin kasarnan da ma na Jihohi?

Da farko shawarar da zan baiwa mata ita ce, ya kamata mata su tsaya su natsu, duk in ka ji ana cewa sak, to tabbaci hakika in ka bi sak din kuwa sai ka yi nadama, kamar dai yadda muke gani a halin yanzun. Ita siyasa ka kan kalle ta ne, wa na sani, wane ne zai taimake ni? Duk inda ka tabbatar za ka karu, a gidanku za a karu, a garinku za a karu, Addininka zai karu, to sai ka fada a yi da kai. Amma matukar ba wannan, to babu amfanin yin ta. Don haka mu yi nazari mata, a duk duniya yanzun mata ne karfin kowane gida, mazaje da yawa an sallame su aiki, wasu an yi masu ritayan dole, wasu an karkashe su a wurare yakin nan da sauran fituntunin nan na yau da kullum. An bar matan da marayu, aikin da namijin zai yi, yanzun macen ne ke yin sa, don haka mata su zauna su natsu su yi nazari su yi dubi a cikin Jam’iyyun nan wacce ce ke tausaya wa mata, wace Jam’iyya ce tausayi da jin kan matan ke zuciyar su.?

Ni a matsayi na, na Shugabar matan Jam’iyyar PDP na wannan shiyya ta Arewa maso Yamma, duk dan takarar da na zauna da shi, sai na bayyana ma sa cewa, mun fa gaji da a zo ana raba mana injin yin taliya ko keken dinki da makamantan su. Duk abin da aka baiwa namiji, shi ne muke son a ba mu. In an baiwa namiji mota Tasi ce, mu ma a ba mu mota Tasi, in an ba shi Keke Napep ne, mu ma a ba mu Keke Napep, muna da ‘ya’ya a gida, za mu ba su su tuka su sami taro sisi, su na ci su na kawo mana. Amma mu na zaune da su a gida mun zauna, sun zauna, su na nema a wurin mu, muna nema a wajen su, sam ba ma son hakan.

Mata ku yi hakuri, Jam’iyyar PDP tana da kyakyawan tanadi a gare ku, za ku ga Canji, canji ba irin wannan ba, canji na ainihi irin wanda kuke bukata, ba na yaudara ba. Jam’iyyar mu ta san mata ta san wahalar da suke sha, ta san kuma mata su suke da kuri’a ma fi rinjaye.

A duk inda mace kuma ta tsaya ta tsayu kenan, don haka da wuya ka ga mace yau ta tsallaka ta koma wannan Jam’iyya, gobe kuma ta tsallaka ta koma waccan Jam’iyyar, mata su na da alkawari, saboda haka muna magana da dukkanin ‘yan takaranmu da su tabbatar sun sanya mana mata a gaba. Mata sun yi rawar gani, mata su suke taka mahimmiyar rawa a siyasar Nijeriya. Sannan kuma mata masu son zaman lafiya ne, mata ba sa son kowace irin fitina, mata su na da kokarin rike amana, don haka kake ganin namiji ya baro waje ya zo cikin gida wajen matar aure ya zuba kudin adashi a wajen mace, saboda ya san sisin kwabon sa ba zai yi ciwon kai ba, sun kuma yarda mace ta iya adana, ba kuma ta son aikata duk wani abu da sunanta zai fito a kira ta azzaluma. Ballantana har a nu na ta a Talabijin ana cewa ga ta nan, EFCC, su kama ta, kafin duk ka ji an kama mace biyu kan wani abu na rashin gaskiya, sai ka ji an ce an kama maza 100, in kuma an kama 100, za ka taras mata ba su wuce biyu ko uku ba, don suna takatsantsan wajen taba abin da ba halaliyar su ba.

Muna da tabbacin matukar mata suka sami shiga kamar yadda ya dace, za a ga sauyi mai ma’ana. Mace ba ta damu da ta gina katon gida ba, ba ta damu da ta sayi mota ta milyan 30 ko 50 ta wuce ana cewa ga ta can ba, sai dai in mijinta ne ya saya ya kawo, amma ba ita ta cire kudinta ta yi wannan ba. saboda ta san akwai abubuwan da suka fi wannan amfani a gabanta.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!