Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sojoji Sun Ceto Mata Da Yara 1,000 Daga Boko Haram A Borno

Published

on

A cikin wani bayanin da Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Nijeriya, Birgediya Janar, Tedas Chukwu ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa rundunar tasu ta yi nasarar tseratar da sama da mutane 1000 daga hannun mayakan Boko Haram.

Har wa yau kuma, ya ce, sun kubutar da wadannan jama’ar ne; wadanda  mayakan ke garkuwa dasu, a lokacin wani samame da rundunar su ta Lafiya Dole ta 22-Brigade, ta gudanar a arewa maso-gabas.

Bugu da kari kuma, Birgediya Janar Chukwu ya ce, wannan samamen an aiwatar dashi ne ta hadin gwiwa da rundunar tsoron kasa da kasa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF).

Ya shaidar da cewa, sun ceto wadannan mutanen ne a kauyukan Malamkari, Amchaka, Walasa da Gora, wadanda ke cikin karamar hukumar Bama a jihar Borno.

“Sannan kuma mafi yawan wadanda aka yi garkuwar dasu mata ne da kananan yara tare da matasa, wadanda yan kungiyar ke tilasta wa shiga kungiyar mayakan Boko Haram”. Inji shi.

“Kamar yadda daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa gyadar dogo, kuma daga  cikin wadanda aka ceto din, Alhaji Gambo Gulumba dan asalin kauyen Amchaka, ya yaba matuka bisa kokarin sojan Nijeriya dangane da yadda suka nuna musu halin jinkai tare da haba-haba da suka samu daga wajen su”. Kamar yadda yake a cikin bayanin.

Janar Chukwu ya sake bayyana cewa sojan Nijeriya suna aiki tukuru wajen ganin sun tsabtace yankin dama a kasa baki daya daga ayyukan tayar da kayar bayan mayakan Boko Haram, kana da fadi tashin yanto duk mutanen da mayakan ke garkuwa dasu.

Har wa yau, ya shawarci jama’a da su baiwa jami’an tsaro hadin gwiwa wajen tsegunta duk wani motsin da basu gamsu da shi ba, zuwa ga rundunar domin daukar mataki cikin gaggawa.

Haka zalika kuma, mai magana da rundunar sojan Nijeriyar ya bayyana cewa an kula da wadanda aka tseratar din a cibiyar kiwon lafiya dake barikin sojojin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: