Zagin Sanatoci: Ashe Malam Ba Malam Ba Ne? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Zagin Sanatoci: Ashe Malam Ba Malam Ba Ne?

Published

on


Kalmar Malam, bahaushe yana amfani da ita wurare da daban daban musamman wajan girmama na gaba da shi  ko kuma wanda ya koyar da shi wani ilimi ko dai na zamani wato boko ko kuma na Addini

Haka kuma ana amfani da wannan kalma domin dora abu a muhallinsa, wani lokaci ma tana da wahalar dauka saboda kas-kas da kai na Malam Bahaushe, duk mutumin da ya yi karatun addini yana ganin kalmar da girma, shi yasa ma wani lokaci idan ance Allah shi gafarta Malam, sai ya ce almajiri dai.

Sannan amfani wannan kalma ta Malam bai tsaya anan ba, a makarantun Boko inda mutun yana koyarwa saboda girmamawa ya zama Malam, ko yana so ko baya so, haka abin yake a makarantun addini da suka hada da islamiya da makarantun allo da na zaure duk ana kiran masu koyarwa Malamai.

Wani abin burgewa game da Malam Bahaushe shine, idan yana son yin magana da kai bai sanka, kalma mafi sauki da yake amfani da ita domin ya baka wani matsayi shine ya kiraka da suna malam ko Malama idan macce ce, a mafi yawan lukota mutane na jin dadi idan aka suffata da su wannan kalma ta Malam.

Kazalika duk mutumin da yasan matsayi da girman kalmar Malam zaka gan shi mutun ne mai saukin kai, mai sanin yakamata, mai kiyaye dokokin Allah, mai gudun duniya, mai son ya aikata daidai, mai tausayi da sanin ya kamata, wanda yasan darajar mutane.

Bincike ya nuna cewa duk wani mutun da ake kira da suna Malam ya zama wajibi ka rika kallonsa da suffofin da na ambata a sama, kuma wani ikon Allah inda ba ganganci aka yi ba wajan yi masa lakabi da Malam ba, dole sai ka ga wasu dabi’u da suka sha ban ban da na sauran jama’a da ba a kira da suna  Malam ko Malamai.

To haka abin yake a sauran kabilu da jinsina, ana girmama manya sannan a ba su wani matsayin na musamman ana yi masu wani kallo na daban, ana rage masu wuri, ana dauke masu nauyin wasu abubuwa na rayuwa, ana shiga cikin al’amarinsu ana yabansu da halayan kirki, ana ba su matsayi daidai gwargwado kuma yadda ya kamata.

Malam Nasiru El-Rufa’I wannan suna ya cika duniyar Malam Bahaushe ta fuskoki da dama, da suka hada da na siyasa da kasuwanci amma dai an fi saninsa a siyasa shi yasa ma wani lokaci ko sunansa na yanka ba a fada sai dai ka ji an ce Malam wanda yanzu jama’a ke ganin kamar sun yi kuskuran kiransa da suna Malam tun farko.

Bisa la’akari da irin abubuwan da na ambata a sama Malam Nasiru El-Rufa’I ya cancanci a kira shi da suna Malam? ba tare da tunanin zai kiyaye duk wani abu da Malamai suka kiyaye ba domin su tabbatar da sunan, ba haka kawai ake makalawa mutun shi ba.

Hanyoyin gane girma da matsayin sunan Malam a cikin tarihi da al’adun Malam Bahaushe shi ne, ba a radawa da suna Malam sai dai ana yi masa lakabi da suna Malam idan sunan asali na mutun yana da nasaba da wani babban mutun ko shehi da ba a son kiran sunansa kai tsaye, sai a rika kiransa da suna Malam.

Duk wani mutun da ya samu wannan lakabi da Malam indai ba wadannan hanyoyi aka biyo ba, to idan aka zuba ido za a ga yana yin wasu abubuwa da suka yi hannun riga da dabi’un mutanen kirki, za a rika ganin mutun yana tufka yana warwara, za a ga mutun bai san mutuncin mutane ba, za a ga mutun baya da tausayi da Imani za a ga mutun yana raina wayo da hankalin jama’a da sai sauran su.

Idan da za a yi tambaya ace wai a ina ne Nasiru Ahmed El-Rufa’I ya samu lakabin suann Malam? na tabbatar idan aka samu amsar zai yi wahala ta zama daya da hanya kwara daya kuma sahihiya wanda ake samun lakabin Malam acikin tarihin hausawa musamman na arewa.

Sannan idan muka duba da kyau ma’anar cewa Malam Nasiru El-Rufa’I ba Malam bane zata fito nan gaba kadan ta hanyar bayyana wasu ayyuka dabi’un sa jama’a suka yi shaidar gani da ido, saboda ya yi kaurin suna a fannoni daban daban.

Lokacin da sunan Malam Nasiru El-Rufa’I ya fara bayyana acikin al’umomi kuma a siyance, gaskiyar magana shi ne, matane sun shaidai shi a matsyin mutumin da baya da mutunci da raguwa da girmamawa da tausayawa da adalci irin na Malamai.

Wannan ina magana ne akan wasu halayansa da suka bayyana a aikace kafin mu zo akan irin maganganun da yake yi wanda kiransa da suna Malam tamkar zagi ne da cin mutunci wanda ya amsa sunansa Malam.

Zamansa a Abuja a lokacon mulkin shugaba Obasanjo Nasiru El-Rufa’I ya yi abin a zo a gani wanda har duniya ta nade ba za a iya mantawa da shi ba, ya jefa mutane cikin zullumi da rashin tabbas na rayuwa wanda har gobe sun kasa yafe masa wannan babban tabo da ya yi masu.

Kuma har gobe suna hake da shi tare da tunanin da zaran sun samu dama za a ga abinda zai biyo bayan abubuwan da ya yi da sunan  aikin gwamnatin wanda shi ya kare da kyar da fadin cewa azzalumai sun sanyo shi gaba, ya taba komawa abin tausayi kafin daga baya ya zama dan kunama.

A tarihi ba a taba samun wani da ke amsa sunan Malam ba, kuma ya rufe idanu ya aikata abubuwan da ba za a taba goge su daga zukatan jama’a ba, saboda munin su.

Duk mu ajiye wannan batu a gefe guda, bari mu zo akan batutuwan da suka faru kwanan nan, Nasiru El-Rufa’I ya shiga takun saka da sanatocin uku da suke wakiltar jama’a daga jihar Kaduna a majalisar dattawa wanda hakan ya zama wata sabuwar hanyar da ta tabbatar da cewa Nasiru El-Rufa’I ba Malam ne irin wanda aka sani tun asali ba kuma ya kamata adaina kiransa da suna Malam domin abin ya zama wani cin fuska a yanzu.

Saboda haka ya ja daga da wadannan sanatoci kuma ya kasa hakuri ya daidaita da su, ya kasa kai karar su wajan Malamansu saboda sun ganin darajar su, ya kasa bin mataki na hankali da shari’a a karshe ya yankewa kansu hukunci ta hanyar yin zagi a matsayin wani abin koyi da yake so mutane jihar Kaduna su rika yi kuma suna tunawa da shi duk lokacin da aka yi zagi ko aka zagi wani babban mutun.

Babu shakka Nasiru El-Rufa’I ya nuna cewa fa ba Malam bane, ba kuma dan Malam bane, baya bukatar zama Malam saboda haka giyar mulki ta yi masa dadi yana sheke ayarsa yadda yake so kafin nan gaba ya ga yadda baya so, idan dai har ya cigaba da tafiyar da rayuwa da kuma dabi’arsa a haka.

Jama’a da dama sun yi Allah wadai da da jin kunyar cewa wannan shugaba ne amma ga irin tabargazar da yake aikatawa kuma yana son jama’a su yi ko yi da shi, ga abubuwa na bakin ciki da kullun sai an nuna mutanen Kaduna da su tare danganta su da mai wannan dabi’a a matsayin gwamnansu.

Baya jin kunyar ya yi rawa gaban koma wanene, idan kun tuna da wasan tashe da ake cewa ‘’kayi rawa kai Malam kayi rawa’’ sai dai ya ce ban yi ba. Ma’ana dai rawa ga malam ko shugaba ba wani abin kirki ba ce, shi kuwa gogan naka rawa na daya daga ckin kananan ayyukansa, da kuma fada ba daidai ba.

Yanzu kuma ya bude sabon shafi na tsinewa shuwagabanni a gaban bainar jama’a da sunan yana fada da su, wannan lamari ya jefa shakku ga mafi yawan jama’ a suna cewa to wai ko dai dai Malam ba Malam bane, muna iya cewa ta tabbata idan aka dauki wanda ake cewa Malam kuma yana amsawa aka hada da Nasiru El-Rufa’I za a tabbatar cewa malam ba Malam bane.

Abinda muke cewa shi ne, kana da zunubai da daman gaske da ka aikatawa mutanen Kaduna da kuma ‘yan Najeriya saboda haka ko dai ka bi hankali ka yi abinda hausawa ke cewa sauka lafiya wai ruwa ya ci biri ko kuma…

Anan zan tsaya, amma zan cigaba a sati mai zuwa kuma zan yi bayani dalla-dalla tare da kawo misalai da kuma dalila da ya sa Nasiru El-Rufa’I dole ya cire wannan riga ta mutunci da ya dauka ya sanya wanda ake da tabbacin ba da izni ya sanya ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!