Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Abin Da Ya Dace Kan Kodin — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Abin Da Ya Dace Kan Kodin

Published

on


A wannan makon ne tashar talabijin ta BBC ta watsa wani shiri na musamman da ta yi akan batun shaye-shayen magungunan dake sanya maye a Nijeriya. Wannan shiri da BBC ta yin a bidiyo bai wuce minti goma ba zuwa 15, amma shirin ya tabowa mutane da dama inda yake yi musu kaikayi, musamman game da yadda ake asarar dubban matasa ta sanadiyar shaye-shayen magungunan da ke bugarwa ko su sanya maye.

A cikin shirin da gidan Talabijin na BBC ya gabatar, an nuno yadda shaye-shayen magungunan da kan sanya maye suke yi wa matasa illa, ta yadda suke yin sanadiyar Haukacewarsu, wanda akan yi asarar da dama ta sanadiyar hakan.

Bayan haka kuma, a cikin wannan shiri, an dauki bidiyon gurbatattun masu yin wadannan magungunan da sukan sanya maye, ta hanyar da su BBC suka nuna kwarewa, suka yi amfani da boyayyar kyamara mutanan da suke aikata wannan mugun aiki aka nuno su da bakinsu suna bayanin yadda suke hada wadannan magunguna domin haukatar da matasan.

Bayan da gidan talabijin na BBC ya yada wannan shirin kan irin yadda maganin Kodin na sirof suka yi wa matasan Nijeriya illa ta hanyar taimakawa wajen haukatar da dubunnan matasan Nijeriya. Gwamnatin Nijeriya ta magantu kan wannan al’amari, domin ba tare da wani bata lokaci ba, gwamnati ta dauki matakin day a dace kan baun magungunan da ake sha domin buguwa.

Ma’aikatar lafiya ta kasa karkashin Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya baiwa hukumar dake kula da ingancin kayayyaki ta kasa NAFDAC umarnin cewar lallai ta tabbatar ta dakatar da bayar da izni ko lasisin hada magnin kodin a Nijeriya tare kuma da kuma hana shigo da shi daga kasar waje ba tare da wani bata lokaci ba.

Alal hakika wannan mataki da ma’aikatar lafiya ta dauka ya dace domin an yi abin da ya dace a kuma lokaciin day a dace. Batun shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma magunguna masu sanya maye da ake sha fiye da kima abin yayi yawa kuma duk wasu masu kishi dole wannan a’amari ya dame su.

Batun shaye-shaye abu ne da tilas a tashi a taka masa birkin day a dace, domin wannan al’amari ya shafi kowa ta kusa ko ta nesa. Sannan kuma, bayan Gwamnati ta tabbatar an daina baiwa kamfanonin da suke yin irin wadannan magunguna izni, sannan ta tabbatar kuma an dauki hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu yana yin dillanci ko sayar da irin wadannan magunguna, haka kuma, batagari wadan da suke yinsa a gida, kamar yadda muka gani a wancan bidiyo da gidan talabijin na BBC suka haska, ya kamata a bibiye su kuma a dauki kwakkwaran mataki a kansu tare da yi musu hukunci mai tsanani.

Sannan kuma, Gwamnati ta dauki mataki na gaggawa wajen ganin an ceto rayuwar matasan da suka auku wannan al’amari na shaye-shaye, domin kamar yadda muka gani a wancan bidiyo hard a budurwa ‘yar shekaru 16 da ta tsinci kanta cikin wannan bala’i. To lallai ya kamata a taimakawa irin wadannan matasa wajen ganin ba a yi asararsu bat a hanyar tsare musu hankalinsu, wanda yana daga cikin ayyukan wajibi na hukuma.

A baya akwai cibiyoyi da ake tsugunar da masu matsala irin wannan inda ake basu kulawa ta musamman, tare da dawo da su cikin hayyacinsu da kuma saita musu tunanin, su dawo mutane kamar kowa a cire musu dukkan wani abu da zai sanya su marmari ko son irin wadannan kayan maye din. Dawo ko inganta irin wadannan cibiyoyi da ake da su zai taimaka kwarai da gaske wajen ganin ba’a yi asarar sub a a titi.

Bincike ya nuna irin wadannan cibiyoyi da ake tsugunar da irin wadannan mutane ana dawoda su cikin hayyacinsu tare da saita tunaninsu, wasu ko dai tun zamanin turawa aka yi su, basa samun wata kulawar da ta dace, ko kuma Gwamnatocin jihohi sun janye dan tallafin da suke bayarwa domin gudanar da wannan cibiya, ta yadda sau da dama sai ka tarar sabulun a irin wadannan cibiyoyi ya gagara, har sai an jira wani daga waje ya kawo.

Haka kuma, lokaci yayi da mutane zasu daina tunanin komai sai Gwamnati ta yi, ya kamata a samu masu arziki su gina irin wadannan cibiyoyi na kudi domin mutum ya biya kudi ya kai dansa domin dawo da shi cikin tunaninsa da hankalinsa, samun irin wadannan cibiyoyi masu zaman kansu zai taimaka kwarai da gaske wajen ganin an an ragewa Gwamnati nauyin cewar komai sai it ace zata yi.

Bayan haka, lallai harkar shaye-shayen nan, jama’a su sani Gwamnati kadai ba zata iya maganta tab a gaba daya, dole sai an taimakawa hukumomi musamman na ‘yan sanda da bayanai na irin mutanan da suka harkar kasuwancin wadannan miyagun kwayoyi da kuma inda ake yi, da inda ake hadawa, wannan hanya ce mai kyau da za a taimakawa da hukumomin tsaro dakile ci gaba da yaduwar kayan maye da shaye-shaye a tsakanin al’ummar wannan kasa.

Ayyuka na laifuffuka da suka hada da fashi da makami da fyade da sace-sace da garuwa da mutane domin neman kudin fansa, ummul aba’isin dinsu shi ne ta’amali da kayan shaye-shaye daa galibi masu aikata irin wadannan abubuwa suke yi, shi yasa kafin su yi sai sun bugu sun kwale sosai sannan suke iya yin barnar da ta danganci irin wadannan miyagun ayyukan da suka addabi wannan al’umma ta mu.

Bayanai sun tabbatar da cewar, hatta ‘yan kungiyar Boko Haram da suke ayyukan ta’addanci suma suna ta’amali da irin wadannan kayan shaye-shaye kafin su aiwatar da ayyukansu na ta’addanci ga al’umma. Kwanakin baya an taba kama wata kwantena cike da maganin kodin da benelin wadda aka ce jihar Adamawa aka nufa da maganin, amma kuma wasu bayanai suka tabbatar da cewar maganin karshen inda za a kaishi shi ne dajin Sambisa inda ‘ya ‘yan kungiyarr Boko Haramsuke da sansani, suke kuma shirya dukkan wasu hare harensu a can.

To wannan gwari gwari yana nuna mana yadda su kansu ‘yan kungiyar da suke karya da sunan addini ko jihadi suke ta’amali da muggan kwayoyi wajen baiwa yara kanana, su sha su bugu sannan a daura musu bama bamai su shiga cikin mutane suna tayar da su, zaka iy mamaki ace mutum da hankalinsa ace ya daura bom a jikinsa kuma ya shiga masallaci ya kashe Musulmi suna Sallah! Shin ta yaya hankali zai dauki wannan?

Mai hankali ya san ba yadda zaka sanya Bom a jikinka ka shiga Masallaci mutane suna Sallah ka tayar musu da Bom sannan ka yi tunanin jihadi kake yi, har ka yi zaton zaka shiga al’janna ta wannan hanya, indai ba aikin kwaya ko kayan maye ba, domin sune suke riyawa mutum sabanin abin da yake a zahiri, baki su mayar da shi fari, dare su mayar da shi rana, rami su mayar da shi tudu. Wannan kadan ne daga cikin irin yadda amfani da irin wadannan kayan shaye-shaye suke yi wa al’umma illa a kasarnan.

Daga karshe, lallai muna jinjina tare da yabawa matakin da hukumomi a Nijeriya suka dauka na hana bayar da lasisin yin irin wadannan magunguna, da kuma hana shigo da su zuwa wannan kasa gaba daya kaco kam, wannan abin a yaba ne kwarai da gaske, sannan, muna kuma fatan za a  dauki matakan da suka dace na tabbatarwa an hukunta dukkan wadan da aka samu da laifin yaduwar irin wadannan kayan may eta barauniyar hanya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!