Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Amince A Kafa Kananan Matatun Mai 13 –BARU

Published

on

Gwamatin Tarayya ta bayar da lisis guda sha uku don kafa kananan matatun mai a kasar nan.

Jimlar kamfamfaboni talatin da biyar ne suka nuna sha’awar su na kafa matatun mai a kasar nan, inda hakan ya nuna cewar, kasa da kadan ne suka samu amincewar gina matatun man daga sashen albarkatun mai.

Babban Daraktan rukunonin kamfanin matatar mai na kasa NNPCThis Maikanti Baru ne ya sanar da hakan a cikin sanarwar da kamfanin ya fitar.

Baru ya bayyana hakan ne a taron fasaha na shekarar  2018 tare da bayar da lambar yabo a masana’antar mai da kuma liyafar cin abinci da aka gudanar a kasar Amurka, inda ya halarci taron a matsayin babban bako na musamman kuma shima aka karrama shi da lambar yabo.

Kafa kananan matatun mai wani tsari ne na gwamntin shugaban kasa Muhammadu Buhari don shawo kan hakilon yankin Neja Delta,inda danyen man Nijeriya yake.

Gwamnatin tana son yin amfani da kananan matatun mai ne don dakile sarrafa danyen mai ta haramtacciyar hanya da samar da ayyukan yi don arzurta ‘yan yankin na Neja Delta.

Baru ya bayar da tabbacin hakan a jawabin sa a wurin taron cewar, kamfanin da ma’aikatar albarkatun mai sunyi hadaka don baiwa kafa kananan matatun man kwarin gwaiwa don kafa su a yankin na Neja Delta don samar da ayyukan yi.

Ya ci gaba da cewa, mafarkin mayar da Nijeriya na mai fitar da danyen mai da yawa, a cikin ‘yan watanni zai zamo gaskiya.

Ya bayyana zage damtse don a tabbatar da hakan a cikin watan Disambar 2019 da gwamnatin tarayya ta ware don kawo karshen shigo da mai cikin kasar nan.

Yace, shekarar 2019 da aka ware karamin ministan mai Ibe Kachikwu, wanda ya danganta hakan a matayin cewar itace hanyar ta din-din-din da zata kawo karshen karancin  mai da ake fuskanta a kasar nan.

Baru ya sanar da kokarin da kamfanin yake yi wajen yiwa matatun mai hudu da ake dasu a kasar nan kwaskwarima, wadanda suka hada da; ta Warri da fatakwal data Kaduna.

Yace, akan tsarin da ake kan ci gaba da yi da ainahin kamfanonin da suka yi su don a kalla su dawo suna aikin da zai kai kashi tsasa’in kafin 2019 da aka yanke har yanzu maganar na nan yadda take.

Babban Daraktan ya kara da cewa, hanyoyin da kamfanin da za su yi aikin ta hanyar yin kwangila, an kammala hakan a cikin nasara.

Yace, kamfanonin za su gudanar da ayyuka da ban-da-ban za’a sanar dasu nan gaba.

A cewar sa, wannan sabon tsarin zai kasance ne ba tare da dogaron jiran  gwamnatin tarayya ta bayar da kudi ba.

Ya bayyana cewar don gudanar da aikin a cikin sauki da kuma aiwatarwa muna kuma canza gudanar da tsarin aikin na matatun yadda za su samar da mai cikin sauki. Baru ya sanar da cewa, Nijeriya itace ke akan gaba a nahiyar  Afrika, wajen fitar da mai.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!