An Kashe Dala Biliyan 8.44 Wurin Shigo Da Sikari Nijeriya A Cikin Shekaru Uku — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Kashe Dala Biliyan 8.44 Wurin Shigo Da Sikari Nijeriya A Cikin Shekaru Uku

Published

on


 

Nijeriya ta kashe dala biliyan 8.44 don shigo da zallan sikari tan miliyan 16.49 a cikin shekaru ashirin da bakwai masu zuwa.

Bayanan da aka samo daga hukumar siga ta kasa (NSDC), ya nuna cewar, zallan sikarin da za a shigo dashi ya faru ne daga shekarar 1990 zuwa shekarar 2016.

Sikarin da aka shiga dashi ya haura dala miliyan a shekaru ashirn da bakwai da suka shige ya kai na dala miliyan 250.50, daga dala miliyan 265.66 a shekarar 1990 zuwa dala miliyan 516.16 a shekarar 2016. Dogon fashin bakin da aka yi ya nuna cewar, yawan sigan da aka shigo dashi,  ya haura na wancan lokacin.

Yawan gundarin  sigan da aka shigo dashin ya haura tan 955,803 a cikin shekaru ashirin da bakwai da suka shige daga tan 603,770 a shekarar 1990 zuwa tan miliyan 1.59 a shekarar 2016. An kuma lura cewar, sikarin da ake sha, ya kara karuwa a cikin karni biyu da rabi da suka gabata.

Daga shekarar 1990 zuwa shekarar 2016,inda kuma yawan sikarin da ake sha ya kai tan miliyan 16.68, kimanin tan 200,000 kasa da tan miliyan16.49 da aka shigo dashi a tsakanin lokacin.

kididdiga sun tabbatar da cewa, yawan shan sikarin ya karu ne saboda karuwar alummar Nijeriya,ba kamar yadda ake sarrafa sikarin ba ya sanya ake kara sarrafa shi da yawa. Shan sikari ya karu zuwa tan 914,325 a cikin shekaru ashirin da bakwaina tan 645,248 a shekarar  1990 da kuma tan miliyan 1.56 a shekarar 2016.

Bayanan sun nuna cewar, a shekaru ashirin da bakwai da sukawuce,Nijeriya ta samar da tan 579,766 na sikari, wanda ya kai kimanin tan miliyan 16, kasa da yawan jimmalar da ake sha duk a lokacin.

Yawan sikarin da ake sarrafawa a cikin gida a wannan lokacin yana yin kadawa, amma tan  25,000 da aka samar a gida a shekarar 2016, ya kai yawan tan 16,478, inda ya kai kasa da tan 41,478 da aka samar a shekarar 1990.

A bisa kashi biyu bisa dari na gudnumawar da masana’antar sikari takesamarwa a kasar nan, gwamnatin tarayya a shekarar 2008 ta bayar da umarci hukumar sarrafa sikari ta kasa (NSDC), data fitar da wani tsari don a samar da sigan da za a rika dogaro dashi a kasar.

Sakamakon kaddamar da shirn,NSDC ta kiyasta cewar, bukatar Nijeriya ta sikarin zai cike gurbin tan miliyan 1.7 a shekarar 2020. Don a watar da bukatar cikin gida na sikarin, mai makon wanda ake sarrafawa a kasar waje, akwai bukatar a kafa masana’antun sarrafa sikari guda ashirin da takwas, ta hanyar samar da kimanin aka 250,000 don numa rake nan da sama da shekaru goma masu zuwa.

A cewar hukumar, Yawan jarin da aka zuba zai fito ne daga ‘yan kasuwa masu zuba jari ta kuma samar da aiwatar da shirin a nazarin da ta yi a shekarar data gabata, inda hakan ya nuna cewar, bukatar Nijeriya na samar da wadataccen sikarin ya sha bamban.

 

Advertisement
Click to comment

labarai