Samar Da Kyakkyawan Tsaro Ya Sa Muke Goyon Bayan Buhari Da Masari -BOS — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Samar Da Kyakkyawan Tsaro Ya Sa Muke Goyon Bayan Buhari Da Masari -BOS

Published

on


 

Kungiyar da ke goyon bayan takarar shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari wato ‘’Buhari Support Organisation’’ ta ce samar da kyakyawan tsaro yasa take goyon bayan su sa ke tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.

Shugaban kungiyar Dakta Abba Abdullah ya bayyana a haka alokacin wani taron manema labarai da suka kira a katsina inda ya ce babu shakka shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Aminu Masari sun yi kokari wajan samar da tsaro a cikin shekaru uka da suka hau karagar mulki.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana a shekarar 2015 an samu matsalar tsaro musamman a Maiduguri inda ta kai ga hatta baban birnin tarayya Abuja suna barci da da ido a bude ne, amma cikin ikon Allah da zuwan gwamnati  Buhari sai gashi an sha karfin ayyukan ta’adanci na Boko Haram.

Alhaji Abba Abdullahi ya kara da cewa haka abin yake a jihar Katsina inda a shekarar 2015 kashe-kashen jama’a ya zama ruwan dare gama duniya inda aka samu rana daya an kashe mutane 150 a garin Maigora da ke cikin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

‘’Da zuwan Mai girma gwamna Aminu Bello Masari sai aka  bullo da wani tsari na yin afuwa da sansanshi ga barayin shanu wanda hakan ya taimaka wajan kawo karshen wannan mummunan aika-aika tare da kwace makamai daga hannun barayin shanun.’’ In ji shi.

Kungiyar ta ce idan aka koma akan batun samar da aikin yi yanzu karkashin jagoranshi Muhammadu Buhari ta samar da aikin yi ga matasa na N-Power wanda yanzu dubun dubatar matasa suka samu abin yi suka zama ma su dogaro da kai.

Acewarsu shi ma gwamna Masari ya yi namijin kokarin wajan ganin jama’ar da suka zabe shi sun more rumar dimokaradiya inda yanzu haka ya samar da hanyoyi a kusan dukkan kananan hukumomi 34 na jihar Katsina.

Sannan sun jinjinawa shugaban kasa Muahammadu Buhari saboda kin amicewa da ya yi da auran jinsi da kasashen yammacin duniya  suka matsa lamba sai an yi a Najeriya, sannan sun yi Allah wadai da yinkurin ‘yan majalisa na canza dokar zabe da suke kokarin yi wanda kotu ta taka masu birki.

‘kazalika kungiyar magoya bayan Buhari da Masari ta ce shugaban kasa a karkashin hukumar samar da ayyukan yi ta NDE ta samar da ayyukan yi ga matasa inda yanzu suka zama masu dogaro da kai, haka shi ma gwamna Masari ya tallafawa fiye da matasa 5,000 akan sana’o’I daban-daban domin dai kara samun nasara.

Akan haka ne, suka bayyanawa duniya cewa suna goyon bayan tafiyar Masari da Buhari a shekarar 2019 ba tare da wata targarda ba kuma suna neman jama’a da su yi sabon tunani suma su tallafi wannan tafiya cikin saurai kafin a bar su a baya.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai