An Cafke Wanda Ake Zargi Da Kashe Jami’in Ofishin Jakadancin Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

An Cafke Wanda Ake Zargi Da Kashe Jami’in Ofishin Jakadancin Nijeriya

Published

on


 

Gwamnatin Kasar Sudan ta bayyana kama wata mata da ake zargi da kisan wani jami’in ofishin jakadancin Nijeriya da ke Khartoum.

An sami Habibu Almu, a gidan sa da ke can Khartoum Shalkwatar Kasar ta Sudan, ranar Alhamis ta satin da ta gabata, a mace bayan an sossoke shi da makami, Almu, wanda mataimakin jami’in shige da fice na Nijeriya da ke aiki a can Sudan Din.

Cikin wata gajeruwar sanarwa, gwamnatin ta Sudan ta shelanta cewa, ‘yan sandan Sudan sun kama wanda ya aikata laifin, wata mata ce ‘yar Kasar waje ce ta aikata laifin.

“Ta kuma amsa cewa, ita ta kashe mamacin ta kuma kwashe wasu kayansa.

Sai dai hukumomin na Sudan ba su bayyana dalilan kisan ba, ko kuma matar ‘yar  wace Kasa ce.

Can baya dai, Ma’aikatar harkokin waje na Kasar ta Sudan ta ce, ta aika da ‘yan sanda gidan mamacin sun kuma kama mutane da dama suna bincikar su kan kisan.

Ministan harkokin waje na Nijeriya, Geoffrey Onyeama, ya tabbatar a ranar Lahadi cewa, gwamnatin ta Sudan ta sanar da su batun kama wanda ya aikata kisan.

Gwamnatin tarayya ta yi tir da kisan jami’in ofishin jakadancin, ta kuma yi alKawarin haDa kai da da gwamnatin ta Sudan wajen kama wanda ya aikata kisan.

Hukumar shige da fice ta Kasa ta bayyana kaDuwar ta kan kisan, ta Kara da cewa, babban kwanturolan hukumar, Muhammad Babandede, yana kan tattaunawa da ministan harkokin waje kan abin da ya faru Din.

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai