Connect with us

LABARAI

Gwamna Bagudu Ya Yi Kira Ga Gaggauta Kammala Hanyar Kontagora Zuwa Yauri

Published

on

 

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya bukaci ministan ayyukan, wutar lamtarki da kuma gidaje Babatunde Raji fashola domin gaggauta kammala hanyar Kontagora-Yauri a Jihar Kebbi, saboda irin amfanin hanyar ga mutanen johihin kebbi da legas.

Gwamna ya yi kira ne a yayin da ke jawabinsa na maraba ga ministan da ya kawo ziyarar aiki na kwana Daya a jihar a jiya a Birnin-kebbi a Daukin taron na masaukin shugaban Kasa da ke Birnin-kebbi.

Har ila yau, ya bayyana damuwa kan yadda ba a kammala wata hanya mai mahimmanci a kasar ba dangane da tattalin arzikin Najeriya. Ya ce a cikin kowace rana fiye da ɗari biyu waƙa da aka ɗora da kayan abinci a cikin Legas da sauran jihohi a kudu da yammacin wannan kasa. Ya kara nuna cewa rayuka da dama sun rasa saboda rashin talauci na hanyar.

Haka kuma Gwamna Bagudu yace” idon akeyi la’akari da irin gudunmawar da jihar Kebbi ke bayarwa ga ci gaban Kasar nan ta hanyar mayar da hankali ga farfado da tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar noman shinkafa da kuma alkama , inda jihar ta zama zakara kan harakar noman shinkafa da kuma alkama a Najeriya daga cikin ayyukan noma. Wanda ya taimaka wurin ganin cewa Kasar nan tafita daga yinwar abinci da kuma talauci”.

Hakazalika Sanata Bagudu ya gode wa gwamnatin tarayya da kuma Minista na ayyuka don bada tabbacin kammala aikin hanyoyin gwamnatin taraiya da ke a cikin jihar ta kebbi nan bada jimawa ba. Domin yace hanyar ta fara ne tun daga jahohin sakkwato , Kebbi da kuma Neja har zuwa Jihar Legas inda jihar Kebbi ta yi wata yarjejeniya a tsakanin jahohin biyu kan harakar samar da shinkafa ga jihar ta legas da kuma sauran wasu kasuwanci kamar gina kasuwar kifi a jihar ta kebbi dama sauransu.

Da yake jawabi tun farko, ministan ayyukka da gidaje Babatunde Raji Fashola ya bayyana makasudin ziyarar da ya kawo jihar kebbi shine domin da ma’aikatarsa da kuma gwamnatin taraiya ta kawo gudunmuwar ta ga jihar kebbi hanyar gyaran hanyoyin gwamnatin taraiya musamman hanyar kontagora – Yauri domin irin muhimmancin ta baga jahohin arewa ba kawai har da gwamnatin taraiya.

Ministan ya ci gaba da cewa “ bayan tabbatar da kammala aikin hanyar kontagora-Yauri da kuma kammala gidajen ma’aikatan gwamnatin taraiya da ke aiki a cikin jihar ta kebbi da gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke ginawa a cikin jihar ta kebbi”.

Ministan ya bayyana cewa, kasafin kudin bana na ma’aikatar ayyukka ta taraiya ta sanya aikin gyaran hanyoyi gwamnatin taraiya da ke a cikin jihar ta kebbi shine yasa na ke a jihar ta kebbi domin kara bayyana wa gwamnatin jihar da kuma jama’ar Kebbi”. Bugu kari yace “ gwamnatin taraiya na alfahari da gwamna Bagudu kan irin KoKarin da kuma gudunmuwar da yake bayar wa ga ci gaban Kasar nan”. Saboda sun yadda da cewa cikaken Dan kishin Kasa ne.

Har ilayau Babatunde Fashola ya kuma gode wa gwamnatin jihar Kebbi da kuma dukan mutanen jihar da irin tallafawa da kuma taimakawa ga nasarar da aka samu a gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari a cikin shekaru uku.

Haka kuma Ministan yace “ zai ziyararci hanyar Yauri-Kontagora da Liman kamba feka iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Benin Jamhuriyar da ke da a jihar Kebbi domin samar da ingantatun hanyoyi a Kasar nan da kuma samar da walwala da jindadi ga jama’ar Kasar nan “.

Daga karshe gwamna Bagudu ya godewa gwamnatin taraiya da kuma Ministan ayyukka na Kasa kan irin kula wa da aka nuna kan hanyoyin gwamnatin taraiya da ke cikin jihar ta kebbi.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: