Connect with us

KIWON LAFIYA

Kwai Ba Shi Da AlaKa Da Cutar Cardiobascular —Binceik

Published

on

 

Masu bincike a jami’ar Sydney suna da  wani Kuduri wanda zai raba gardamar ko kuma bayyana ainihin gaskiyar al’amari, na shawara wadda ta shafi abinci, dangane da cin shi Kwai. Saboda wani sabon binciken da aka yi ya nuna cewar cin Kwai da yake 12 ko wanne mako, bai taimakawa wajen yiyuwar kamuwa da cutar data shafi shafi wasu abubuwa na cikin Kirjhi, a mutanen da ake tsammanin sun kamu da cutar ciwon sikari, da kuma waDanda suke da cutar ciwon sikari ta2.

Sakamakon rahoton binciken da aka buga a mujallar Clinical Nutrition today, shi binciken am Kara faDaDa shi, akan wanda aka yi kafin  akai ga yin shi, wanda kuma aka samu sakamako wanda yai kama da wanda aka yi watanni uku da suka wuce.

Shi binciken an yi shi a KarKashin Dokta Nick Fuller daga jami’ar Boden sashen kula da Kiba, Harkar abinci, Motsa jiki, da kuma  matsalar dake tattare da cin abinci, a Charles Perkin Centre da kuma asibitin Royal Prince Alfred.

Farkon shi binciken su waDanda suka halarce shi manufarsu ita ce, su ci gaba da tsayawa akan nauyinsu, yayin da kuma al’amarin daya shafi (cin Kwai 12 ko wanne mako) na abinci, su mahalarta binciken sun ganao cewar, ba wani  bambanci da yiyuwar kamuwa da cutar da take nasaba da cardiobascular, bayan da suka yi wata uku.

Duk dai mahalarta taron sai kuma suka mayar da kalarsu zuwa al’amarin da ya shafi rage Kiba, zuwa wasu watanni uku, yayin da suka ci gaba da cin Kwai mai yawa ko kuma kaDan, abin da ya kai har wata shida, har ma zuwa watanni sha biyu, dukkan mahalarta shi taron su masu binciken suna lura dasu, sun kuma ci gaba da Dabi’arsu ta ko dai cin Kwai mai yawa ko kuma kaDan.

Gaba Daya dukkan su mahalartan da aka rarrabasu zuwa aji aji daban daban, basu nuna da akwai wata matsaala, dangane da ita cutar cardiobascular, sun kuma samu raguwar Kiba ko kuma nauyi, wannan kuma bai shafi wani al’amarin ko cin Kwai mai yawa ko kuma kaDan ba. Kamar dai yadda Dokta Fuller ya bayanna.

‘’Duk kuwa da yake ana basu shawarwari daban daban akan ko Kwai nawa ya kamata su riKa ci akan mutanen mutanen da ake sa ran suna da cutar ciwon sikari, da kuma waDanda suke da cutar ciwon sikari na 2. Bincike ya nuna bai kamata mutane su Dauki wani matakin ba akan al’amarin daya shafi shi cin Kwan ba, idan dai matuKar yana kan hanya maganar data shafi abinci.

‘’Abinci mai tsafta ko wanda ya kamata a wannan binciken da ka yi ya fi bada fifiko akan yin wani abu, ko Daukar mataki dangane da, Kiba (kamar butter ko manshanu) ko kuma (abocado olibe oil).

Shi binciken an Kara faDaDa shi akan wasu matsalolin da za a iya shiga, waDanda kuma ake ganin suna da alaKa da cardiobascular sun haDa da cholesterol, sikari cikin jini, hawan jini,, ba kuma wani bam banci tsakanin waDanda suke cin Kwai yawa, da kuma waDanda suke cin kaDan.

‘’Kwai su da kansu sun Kunshi cholesterol mai yawa, bugu da Kari kuma  mutanen da suke fama da cutar ciwon sikari na 2, su suna da babban mizani ko kuma abin ‘’Babu Kyau’’ lipoprotein (LDL)cholesterol, shi wannan binciken ya Kunshi shi cin wani wKai da yawa bai dawata alaKa da yawan mizanin cholesterol a cikin jinin mutanen da suke cin Kwan, kamar yadda Dokta Fuller ya bayyana.

Dokta Fuller ya Kara jaddada cewar sakamakon da suka samu bayan da suka kammala bincikensu, ya nuna muhimmancin da cin Kwai yake da shi, ga waDanda ake tsammanin suna da cutar ciwon sikari, da kuma waDanda suke da cutar ciwon sikari na 2.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: