Maulidin Cibiyar Kainuwa Ya Yi Armashi A Kano — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Maulidin Cibiyar Kainuwa Ya Yi Armashi A Kano

Published

on


 

Maulidin da Cibiyar inganta Rayuwar Mata da Kananan Yara wato Kainuwa Women And Children Foundation da ke KarKashin shugabancin Hajiya Fatima Dala mai ba Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje shawara akan walwala da jin daDin Kananan Yara ta Kano ta shirya Maulidin a karo na Tara yayi armashi fiye da yadda aka gabatar a baya.

Taron Maulidin Manzan Rahama wanda akayi a Dakin Taro na Gidan tunawa da Malam Aminu Kano ya samu halartar dubban mutane wanda suka haDa da Maza da Mata masoya Manzan Allah (S.A.W) domin sauraron karatuttu ka da suka Kunshi Tarihin Manzan Rahama da kuma waKoKin na yaban Manzan Allah da Alayan sa da Sahabban sa da sauran bayin Allah na gari a wannan Maulidi wanda Gidan Mubayya da ke Gwammaja ya cika ya batse da dan dazon al’umma a wannan Maulidi.

Haka kuma wannan Maulidi ya samu halartar Malamai Shugabanni Yan Kasuwa Yan Siyasa ya da sauran al’umma daga sassa daban daban na Jahar Kano da Kasa baki Daya ciki kuwa harda Shugaban Majalisar Dokoki na Jahar Kano Rt. Hon. Abdullahi Yusuf Ata.

Ita kuwa shugabar cibiyar Kainuwa Women And Children Foundation Hajiya Fatima Dala ta bayyana wannan Cibiya an kafa ta da Mata kamar 200 amma yanzu akwai Menbobin wannan cibiya sama da 20,000 kuma wannan Maulidi kulli sai samin bunKasa da cigaba ya ke yi kuma dama haka harkar da ta shafi Manzan Allah haka take kullum sai dai bunKasa ba baya ba kuma wannan lokaci wannan rana – rana ce da farin ciki na Masoya Manzan Allah baya iya misaltuwa ko bayyanawa irin yadda yake ga masoyac

 

Advertisement
Click to comment

labarai