Connect with us

SIYASA

Siyasa A Yau

Published

on

 

ALHAJI ABUBAKAR DAN USMAN jigo ne a jam’iyyar APC kuma Dan gaba-gaba wajen ganin ci gaban jam’iyyar. A hirarsa da wakilin mu MUHAMMAD AWWAL UMAR ya tabo batutuwa da nasarorin da gwamnatin Neja ta samu. Ga hirar kamar haka.

Da farko me za ka ce dangane da Korafin da jama’a ke yi cewar har yanzu ba su gani a Kasa ba dangane da dalilan da ya sa suka zabi wannan gwamnatin?

Kowa ya san yadda gwamnatin nan tazo kan karagar mulki da irin matsalolin da ta gada, in ko haka ne ba ya yiwu wa ka ba ta maki a cikin shekaru biyu, domin idan ka yi la’akari da jihar ba mu da hanyoyi na Kwarai, ba mu da asibitoci na Kwarai, makarantun mu sun lalace, ba wani da za ka Dauka ka nuna wa duniya kuma an aza harsashin gyara tun lokacin mulkin marigayi Abdullahi Kure, waDanda suka gaji kuren ba su mayar da hankali akai ba, shi maigirma gwamna da yazo ya iske basussuka wanda dole cikin Dan abin da yake shigo wa ake zaftare wannan bashi.

Da Alhaji Abubakar Sani Bello ya zo ya sha alwashin duk wani abu mai anfanin al’umma da aka fara aka watsar sai ya kammala, kuma gaya Dan abin da ke shigo wa can ake narkar da su ka ga dole sai an bi a hankali wanda duk zai yiwa gwamnatin adalci zai yabawa gwamnatin nan akan waDannan abubuwan da na zayyano ma ka gane.

 

Ba ka ganin cewar wannan bai isa ya zama hujja ba, duba da cewar ita romon dimukuraDiyya waDanda ake muka ya kamata su bayyana shi ba ita gwamnatin ba?

Kasan ita siyasa dole ne a yi adawa, amma ya kamata ita adawar nan ta zama ta ilimi da fahimta ka gane, saboda haka idan kana sakamakon yadda abubuwan ke tafiya za ka iya tantance komai tunda kaima Dan jihar ne kuma komai a fili yake. Idan ka duba kusan duka manyan garuruwan jihar nan in ban da ayyukan da maigirma Kure ya yi na samar da hanyoyi da gyaran makarantu, asibitoci, ba wani abu da aka sake kafawa sai bayan zuwan Abubakar Sani Bello, ka duba wasu daga cikin makarantun mu musamman ma na kimiyya da fasaha da na koyon aikin jinya kai da kan ka za ka yabawa gwamnatin nan, dubi yadda bangaren ilimi ya lalace ba Kwararrun malamai balle kuma kayan aiki, kan haka mai makon a kori mutane aiki kamar yadda wasu jahohin suka yi, sai aka KirKiro makarantun horar da malamai ta yadda nan ‘yan shekaru kaDan sai malamai sun zama abin alfahari, sassa uku na jihar nan ko ina an kafa wannan cibiya ka ga ba aikin rana Daya ba ne ai.

Amma akwai Korafin rashin aiki ga matasa wanda wannan ba Karamin barazana ba ne ai.

Haka ne, to ai ganin gwamnati ba ta iya baiwa kowa aiki yasa maigirma gwamna ya fifita harkar noma wanda an gayyato kamfanoni wanda suka yi haDin guiwa da ita gwamnatin kuma kashi saba’in na waDannan kamfanoni matasan mu ne ke tafiyar da su, nan cikin azumin nan mai kamawa farashin abinci zai sauKi saboda samuwar shinkafar da aka noma a jihar kuma za ta shiga kasuwa. Na biyu muna da cibiyoyin kowon sana’o’in hannu wanda a baya sun durKushe kuma maigirma gwamna bayan zuwansa sun farfaDo yanzu dubban matasa ne ke cin moriyar shirin, abin bai ma tsaya akan gwamnati ba hatta makusantan gwamna sun jajirce da abin hannun su suna bunKasa shirin.

Akwai masu ganin cewar bai kamata a yabawa ita gwamnatin ba domin ko wasu muhimman abubuwa da suke mallakin gwamnati ba su da nagartar yabo.

Ai ya sa makarantar horar da ma’aikata jinya ta Bida aka tabbatar hukumar lafiya ta gwamnatin tarayya ta amince da ita wanda duk shekarun da aka baro baya tamkar gata nan ne, sai ga ta Kontagora da aka samar yanzu, ko waDanda ke minna ta kimiyyar lafiya da ta horar ungwazoma aka tabbatar an Daga darajarsu. To ire-iren ayyukan da aka mayar da hankali ke nan martaba abin da yake haKKin gwamnati da inganta tsarin aikin gwamnatin.

Rashin aiki na daga cikin abin da yasa matasa faDawa bangar siyasa da shaye-shay, kuma ana zargin cewar ku ‘yan siyasa laifin ku ne.

 

Ina jaddawa matasa ‘yan uwana cewar APC tazo da nufin canji ne daga turbar da muka fito zuwa nagartacciyar turba, dan haka duk Dan siyasar da yace maku ku fito dan yin bangar siyasa to ya turo maku Dansa ya zama jagora, bai yiwuwa ‘ya’yansu na Ketare suna karatu mu kuma a gurbata mana rayuwa.

Ya zama wajibi mu natsu mu faDi wa junanmu gaskiya, mutum bai samun kamala ya yi kyakkyawan nazarin abin da zai taimaki rayuwar su sai ya inganta tunanin sa, da farko dai mu koma makaranta sannan mu nemi sana’a domin ita siyasa hanya ce ta haDuwar jama’a da tunanin yadda za a gina Kasa, ban ko tunanin mai shaye-shaye zai iya natsuwar da zai inganta rayuwarsa balle ya inganta na wani.

Gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello tazo da shirin da zai inganta rayuwar matasan, shi yasa aka KirKiro cibiyoyin koyon Sana’ar hannu ga wanda ya yi karatun da ma wanda bai yi ba, sai in ce a Neja ba a taba samun gwamnatin da ta sanya tubalin inganta rayuwar al’umma ba kamar wannan gwamnatin.

Wanne Karin haske za ka yi ma waDanda ke ganin kamar ba a yi komai ba.

Kamar yadda na fadi ne a baya, tun lokacin siyasa muke wajibi ne ayi adawa amma adawar nan ta zama ta gaskiya, domin gwamna a koda yaushe yana jin Korafe-Korafen jama’ a kuma akansu ake aiki. Dan haka duk wanda zai faDi wata magana indai gaskiya ce ai kamar tunatarwa ce ya yi.

Ba a hana adawa ba, kuma ai ita adawa ba Kiyayya ba ce, tuni ga mai mulki ina jaddada ma cewar na gamsu da muradun gwamnatin nan domin ta daKile kafafofin da ke yoyo ta yadda nan gaba al’umma zasu ga anfanin hakan, domin muradu ne da manufofi masu kyau.

 

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: