Connect with us

KASASHEN WAJE

An Yi Jana’izar Falasdinawa 60 Da Isra’ila Ta Kashe

Published

on

 

Dubban Al’ummar Musulmi ne suka gudanar da jana’izar mutane 60 ciki har da jaririya ‘yar watanni 8 da haihuwa da sojin Isra’ila suka hallaka jiya yayin zanga-zangar da Falasdinawan suka yi don nuna adawa da matakin Amurka na mayar da Qudus babban birnin Isra’ila.

Yayin zanga-zangar ta jiya wadda Falasdinawan ke ci gaba da gunarwa, Sojin na Isra’ila sun yi amfani da makaman gurneti da kuma bindigogi da kuma hayaqi mai sanya hawaye wajen tarwatsa su tare da hallaka wasu.

Rahotanni sun ce mutane da dama ne suka fita daga hayyacinsu sakamakon hayaqi mai sanya hawayen da Isra’ilan ta yini tana harbawa yankin na Gaza.

Kawo yanzu dai akwai kusan mutane 300 da suka samu mummunan rauni a zanga-zangar ta jiya, ciki har da qananan yara da shekarunsu ya gaza 12.

Tuni dai qasashen duniya suka yi Allah wadai da matakin yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke wani zaman gaggawa kan batun.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce, kunnen shegun da Trump ya yi wajen bude ofishin jakadancin qasarsa a birnin na Qudus ya sanya ya rasa ikon fada ajin da kuma martabar da ya ke da ita wajen shiga tsakani don sasanta rikicin gabas ta tsakiya.

Bayan mayar da birnin na Qudus babban birnin Isra’ila hakan na nufin cewa yanzu yankin na Gaza baya da wani iko da birnin a dai dai lokacin da Isra’ilan ke ci gaba da mamaye yankin na su.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: