Connect with us

KASASHEN WAJE

Iran Ta Fara Tattaunawa Da Turai Kan Nukiliyarta

Published

on

 

Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Jabad Zarif, ya fara tattaunawa da wasu qusoshin Qungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels a jerin ziyarar da ya fara a ranar Asabar daga qasar China zuwa Rasha ta neman mafita da kuma dorewar yarjejeniyar nukiliyar da qasar ta cimma da qasashen Turai bayan ficewar Amurka daga cikinta.

Mr. Zarif ya fara ziyarar ne a ranar Assabar daga China, in da ya gabatar wa mahukumtan qasar qorafin fcewar Amurka daga yarajejeniyar nukiliyar 2015 tare da neman goyon bayan China wajen ci gaba da dorewarta, kafin ya zarce Moscow in da suka yi doguwar tattaunawa da takwaransa na Rasha, Sergei Labrob kafin zuwansa birnin Brussels ranar Talata.

Qasashen Turai sun lashi takobin ganin sun ci gaba da aiki da yarjejeniyar duk da ficewar Amuruka daga cikinta.

Da farko dai Iran ta lashi takobin watsi da yarjejeniyar idan Amurka ta fice daga cikinta, amma daga bisani ta sassauta matsayinta ganin qasashe 5 da suka cimma yarjejeniyar da ita a 2015 da suka hada da Britaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China sun nuna rashin jin dadinsu da ficewar Amurkar ba tare da wata hujja ba ya sa ta sassauto ita ma domin samun masalaha a lamarin

Za a iya cewa shugaban Amurka Donald Trump ya cika alkawarin da ya dauka na fitar da qasar daga cikin yarjejeniyar kamar yadda ya alkawalta a yaqin neman zabensa.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: