Connect with us

LABARAI

Mun Kwato Tiriliyoyin Naira Daga Barayi –Buhari

Published

on

 

Gwamnan jihar Bauchi Lauya Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana cewar kawo yanzu sun samu nasarar shigo da Tiraktoci guda Arba’in 40 cikin jihar, yake cewa, wannan adadin suna daga cikin Tiraktoci guda dari biyar ne da gwamnatinsa ta nufi samar wa manoma cikin rahosa mai sauki, wanda kuma tuni Buhari ya kaddamar a kwanakin baya domin bunkasa harkar noma a jihar ta Bauchi.

Gwamnan Abdullahi Abubakar ya bayyana haka ne a jiya, sa’ilin da ke jawabi a wajen kaddamar da shekarar noma ta 2018 hade da fara saida takin zamani ga manoma, wanda ya gudana a gidan gona da ke Bauchi.

Gwamnan yake cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da shirye-shirye masu kayatarwa wadanda za su tallafa wa manoman jihar, hade kuma da saukake musu samun yanayin noma da kiwo domin daukaka darajar tattalin arziki, samar da aikin yi, hade kuma da tafiya daidai da zamani a hidimar da ta shafi noma da kiwo.

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta saida takin zamanin ne a kan naira guda biyar da dari biyar ga dukkanin mai bukata, ya bayyana cewar wannan farashin na da matuwar rayuwasa, kuma sun yi hakan ne domin kyautata wa talakawa da manoman jihar.

Ta bakinsa “Idan ba a mance ba a lokacin da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kawo ziyara Bauchi ya kaddamar da wani shiri na musamman na samar wa manoman jihar Bauchi ‘Tiraktoci’ guda dari biyar ‘500’. Wanda tuni guda 40 a cikin 500 an riga an kawo su, an kuma sauke su cikin kwantena, sannan kuma an hadasu suna nan a tare a wannan wajen,” In ji Gwamna.

M.A ya bayyana cewar wannan shirin, hadin guiwa ne a tsakanin gwamnatin jihar da kuma gwamnatocin kananan hukumomi 20 na jihar ta Bauchi, hade kuma da kamfanin da suka kulla harjejeniyar samar da tiraktoci wa jihar.

Baya ga nan kuma, Gwamnan ya bayyana cewar akwai shiri na musamman da gwamnatinsa ta yi na tallafa wa masu kiwon shano, inda ya bayyana cewar mutane sama da dubu 3 za su ci gajiyar shirin, haka kuma tallafin kiwon awaki shi ma sun tanadar da bashi wa mutane sama da dubu biyu, kiwon kifi mutune 120 ne za su ci gajiyar shirin bashin noman kifi a jihar.

Haka kuma ya bayyana cewar “Za mu samar da kananun tiraktoci guda 150 da za mu raba wa manoma 150 wadanda za su fi amfani wa Arewacin Bauchi, sannan kuma Injin  girbin shinkafa mun samar da guda 100 da za raba wa kungiyoyi guda 100 da suka kunshi mutane 100. Sannan kuma an samar da injinan feshi guda 1,000 wanda za a baiwa matasa guda dubu, sannan kuma muna da shirin noman shinkafa na damina da za a baiwa mutane dubu shida da dari shida,” kamar yadda ya shaida a wajen taron.

Ya bayyana cewar, nomar shinkafa, gero, dawa, masara, da sauran shuke-shuke za su baiwa manoma bashin kudade domin tallafa musu kan nomar wadannan ababen.

Gwamna Abubakar ya kuma daura da cewa, dukkanin irin wadannan tallafin suna zuwa ne biyo bayan bashin da jihar Bauchi ta samu daga babban bankin kasa na tsabar kudi har naira biliyan biyar, “Biliyan takwas muka nema, muna sa ran nan bada jimawa ba sauran biliyan 3 din ma zai zo mana domin habaka noma a jihar Bauchi,” Kamar yadda ya shaida.

Gwamnan ya kuma shaida cewar a tsakanin gwamnatin jihar da kuma wata kamfani mai suna OCP Africa da ke a kasar Maroko wanda a duk duniya kamfanin yayi zarra wajen sarrafa takin zamani kamar yadda gwamnan ya shaida, ya bayyana cewar tuni suka yi aikin hadaka da kamfanin wanda yanzu haka zai zo jihar Bauchi domin kyautata kamfanin taki na jihar Bauchi da kuma tallafa wa manoma wajen bincikar irin takin da ya dace da gonakansu domin samar da yabaiya mai kyau a kowani lokaci.

Da yake tasa jawabi tun da fari ma, Kwamishinan Albarkatun Gona na jihar Bauchi Malam Yakubu Kirfi ya bayyana cewar tuni gwamnan jihar ya samar da muhimman kayyakin da suka shafi noma da kiwo wanda kai tsaye hakan zai taimaka gaya wa ci gaban manoman jihar Bauchi.

Kwamishinan ya bayyana wasu muhimman ababen da gwamnati mai ci ta samar domin kyautata wa manoma, ya bayyana cewar za su kuma ci gaba da yin duk mai iyuwa domin kyautata wa manoman jihar.

Tuni dai gwamnan jihar Abubakar ya kaddamar da fara saida takin zamanin a farashin naira dubu 5,500 ga kowani manomi a daminar bana ta 2018, sai dai sun bayyana cewar ba za su saida sama da buhu 10 ga mutum daya ba, kawo yanzu manoma da kamfanoni suna tururuwar samun cin gajiyar wannan farashin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: