Connect with us

KASUWANCI

NCAA Ta Dakatar Da Ayykan Kamfanin Jirgin Saman First Nation

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa,(NCAA) ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin na First Nation Airways har sai yadda ta yuwu.

A sanarwar da kakakin hukumar Sam Adurogboye ya fitar ya ce, an dakatar da ayyukan kamfanin ne saboda gudanar da ayyukan sa ba tare da an bashi izini ba.

Sam Adurogboye ya ci gaba da cewa,  wasikar dakatarwar, tana dauke da lamba kamar haka, NCAA/DG/CSLA/RM/1-06/18/2304 mai kuma dauke da kwanan wata na ranar 11 ga watan Mayun 2018 wanda kuma Darakta Janar na hukumar Muhtar Usman ya rattabawa hannu.

Kakakin ya kara da cewar, wasikar ta dakatarwar an kuma aikewa da kamfanin, inda suka nuna cewar sun samu wasikar.

Adurogboye ya bayyana cewar, dakatarwar anyi tane saboda ci gaban da kamfanin ya yi nayi wa dokokin hukumar karan tsaye.

Wasikar ta bayyana cewar, bayan da takardun kamfanin suka daina aiki, kamfanin baida wasu ingantattun jirage a kalla guda biyu don gudanar da ayyukan sa kamar yadda dokar ta bukata mai lamba, 9.1.1.6 (b) da biyu a cikin baka (2) na hukumar ta shekarar 2015.

Ya sanar da cewar, takardar shedar gudanar da aiki na kamfanin a lokacin sabunta ta, ta sabawa ka’idar yin jigila ta duniya.

A cewar kakakin, kamfanin ya kuma ci gaba da gudanar da ayyukan sa harda bayar da sanarwar yin jigila da sayar da tukiti a filayen sauka da tashin jirage na kasa da kasa dake jihar Legas da kuma Abuja.

Ya bayyana cewar, a baya hukumar ta sanar da kamfanin cewar tana gudanar da bincike akan karya dokokin hukumar da kamafnin ya yi.

A cewar sa, hukumar ta aikewa da kamfanin wasika a ranar 31 ga watan Agustan 2017, wadda ta umarci kamfanin da ya dakatar da haramtacciyar ayyukan sa in kuma yaki, dakatarwa ce zata biyu baya.

A cewar sa, a bisa binciken da aka gudanar, hukumar ta gano cewar, kamfanin ya yi buris da wannan gargadin, inda ya ci gaba da gudanar da ayyukan sa wadanda a ka’ida, sun sabawa dokar bayar da lasisi.

Ya yi nuni da cewar, laifin ya sabawa dokar hukumar ta 9.1.1.4 (d) a cikin baka ta Nijeriya ta shekarar 2015.

Adurogboye ya ce, hukumar don ta tabbatar da ana bin wannan dokar sau da kafa, ta sashe 35(2) a cikin baka da(3) a cikin baka da (a) a cikin da (4) a cikin baka na dokar shekarar 2006, kamafanin bai chanchi ya ci gaba da gudanar da aikin sa ba.

Kakakin ya ce, a saboda haka, an dakatar da kamfanin har sai yadda ta yuwu, inda dakatarwar ta fara aiki a ranar 11 ga watan Mayun 2018.

Ya ce, ana kuma bukatar masu gudanar da kamfanin dasu dawo da lasisin su ga Daraktan na ayyuka da horaswa a cikin kwana bakwai da zarar sun samu wasikar.

Adurogboye ya ce, in har kamfanin ya nuna halin dattako da niyya wajen bin dokokin hukumar, hukumar zata iya sake sabunta ayyukan kamfanin da kuma maido masu da lasisin su don suci gaba da gudanar da ayyukan su.

Ya kara jadda kudurin hukumar akan bin doka da oda na jiragen, inda ya ce, hukumar bazata yi kasa a gwaiwa ba, wajen jadda da dokokin don masu jiragen sama su dinga bin su sau da kafa.

Dakatarwar da aka yiwa kamfanin, ya kuma kara tabarbarar da ayyukan sa.

A cewar Manajin Darakat kamfanin, Kayode Odukoya a yanzu haka kamfanin hukumar EFCC ana zargin tana bincikar kamfanin akan wata badakala.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: