An Cafke Wasu Hastsabiban ’Yan Yahoo Shida A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIMIYYA

An Cafke Wasu Hastsabiban ’Yan Yahoo Shida A Nijeriya

Published

on


Jami’an hukumar EFCC sanar da cafke wasu ;yan damfara ta kafar sadarwa intanet wadanda akafi sani da suna Yahoo yahoo booys a yankin Kubwa cikin babbar birnin tarayya Abuja. Sanarwar da jami’in watsa labaran hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren, ya bayar, ya ce, wadanda ake zargib sun hada da Ihoeghian Aghasomwan da Precious Osarumen da Enabulele Osazee Frank da Osahon Scott da Efe Ehieorobo da kuma Peter James.

Samamen da sashin yaki da ‘yan damfara na hukumar ta gudanar ranar 11 ga watan Mayu 2018 ya biyo bayan rahotanin sirri ne da aka samu na kasancewar ‘yan damfarar da harkokin da suke yi a unguwar.

Binciken ya kai ga tantance mutanen da inda suke, daga nan ne suke gudanar da aiyukan damfarar inda suke cutar da jama’a daga cii da wajen kasar nan ta hanyar amfani da kafar sadarwa na intanetr.

Kayayyakin da aka kama daga wadanda aka kama sun hada da mota daya kirar Toyota Camry 2009 da Laptop guda 10 da paspon ECOWAS guda 4 da kuma waya tafi da gidanka guda 17 da flash dribe 2 sauran kayan sun  hada da HP printer.

An kuma gano jakar tafiya da tikitin jirgi dake nuna an yi tafiya ranar 19 ga watan Maris 2018 da kuma ke nuna an shigo Abuja ne daga inda aka taso., da kuma wasu takardu masu mahimmanci da suka shafi hukumar kwastam, dana ma’aikatan harkokin waje na kasar Sin masu lamba kamar haka : 00548 da TDK da ME103178131.

Sanarwar ta kuma ce, dukkan kayayyakin da aka kwace a hannunsu zasu fuskanci binciken kwakwaf, daga nan ne za a gurfanar dasu a gaban kotu domin yanke musu hukuncin daya dace.

 

Advertisement
Click to comment

labarai