Connect with us

LABARAI

Abuja Ta Kwace Wa Legas Kambin Hada-Hadar Kudaden Waje

Published

on

Babban Birnin Tarayyar Abuja yana

kara samun tagomashi, a yayin da
yake kara samun shigowar kudaden
wajen, wanda aka fara hakan a
tsakiyar shekarar 2017.
A rahoton da hukumar kididdiga
ta kasa (NBS) ta fitar ta ce, a farkon
shekarar 2018, Nijeriya ta samu
shigar dala bilyan 3.54.
Wannan ya nuna cewar an
samu karin kashi 32.24 bisa dari
daga cikin adadin da hukumar ta
bayyana a baya ya kai dala biliyan
2.68.
Duk a wancan lokacin, shigo da
kudi cikin jihar Legas ya karu da
kashi 4.59 daga cikin dala biliyan
2.55 a zango na karshe zuwa dala
biliyan 2.67 a shekarar 2018,inda
kuma shigo da kudi cikin jihar
Akwa Ibom ya kai dala miliyan
43.62, inda hakan ya nuna ya sauka
da kashi 65.05 bisa dari daga cikin

jimlar da NBS ta fitar a zangin
karshe na dala miyan 124.85.
Ma’ana jihohin Ogun da Bauchi
da Kano sun samu shigar kudaden
kasar waje da yawa a zangon
shekara na farko, inda ko wacce jiha ta samu kashi 182.06 bisa dari
da kashi 370.59 bisa dari da kuma
kashi 154.84 a cikin zango-zango.
A cikin rahoton da hukumar
NBS ta fitar na kudaden da aka
shigo dasu a zangon shekarar
farko a cikin watanni ukun
shekarar 2018, ya kai dala miliyan
6,303.63, inda hakan yake nuna
an samu karin kashi 594 bisa
a cikin shekara daya daga dala
miliyan 908.3 a cikin zango daya
na shekarar 2017.
A cikin farkon zangon shekarar
2018, NBC taga yadda ake shigo
kudaden cikin kasar tun daga
karin da aka samu a cikin zan
zangon na biyu a shekarar 2017.
Fashin baki akan kudaden da

suka shigo dasu daga kasar waje
ya nuna cewar, kasar Birtaniya
tana ci gaba da taka rawar ta
wajen zuba jari a Nijeriya a zangon
shekarar 2018,inda aka zuba jarin
dala biliyan 2.25 a kasar nan.
Shigowar wadannan kudaden ya
kai kashi 35.73 bisa dari na jimlar
kudaden da suka shiga a cikin
zangon daya na shekarar 2018,
har ila yau, ya kai kashi 39.89
bisa dari da ya karu a zangon baya,
inda kuma sama da kashi 644.55
ya karu a shekarar data gabata.
Tun shekarar 2010, Birtaniya
ta tura kude masu yawa a cikin
tsakiyar shekarar 2015.
Bugu da kari akwai akwai
kudaden da ake shigo dasu daga
kasar Amurka, inda suka kai
biliyan 1.26 a zango na farko na
shekarar 2018 ko kashi 19.99
bisa dari na jimlar kudiden da ake
shigowa dasu kasar nan. kasar

Amurka tana daya daga kasar dake
zuba jari a Nijeriya, inda itace ke
a kan gaba ko ta biyu wajen zuba
jari a Nijeriya.
Sauran masu zuba jarin biyu a
cikin zangon farko na shekarar
2018 sune kasar Afirka ta Kudu
da Ghana, wanda suka samu dala
miliyan 493.22 da kuma dala
miliyan 380.14 na kudin da suke
shigowa Nijeriya a farkon zango.
Wadannan kasashen biyu jarin
da suke zubawa ya kai kashi 7.82
bisa dari da kuma kashi 6.03 bisa
dari na jimlar da ake shigowa dasu
a zango na daya na shekarar 2018.
Kudin da ake shigowa dasu daga
kasar Afirka ta Kudu ya karu da
kashi 79.29 bisa dari a zangon
baya zuwa kashi 673.19 bisa dari
a zangon farko na shekarar 2017.
A zango na farko na shekarar
2018, shine karo na farko da tun
a shekarar 2013 Ghana ta zuba

jari jari a Nijeriya, inda hakan
ya sanya Ghana ta zamo ta
hudu wajen shigo da kudi a cikin
Nijeriya a cikin zangon farko na
shekarar 2018.
A cewar hukumar NBS, karin
shigowar kudi a zango na daya na
shekarar 2018, mafi yawanci zuba
jari ne, wanda ya habaka daga dala
miliyan 3,477.53 a zangon baya
zuwa dala miliyan 4,565.09 da aka
samu akan kashi 72.42 bisa dari
na kudin da aka shigo dasu a cikin
zangon.
Kudaden da suka shigo an raba
su akan zuba jari gida uku, akwai na zuba jarin kasar waje da ake yi
kai tsaye da zuba jari na kashin
kai da kuma sauran zuba jari.
Zuba jarin kasashen waje na kai
tsaye da sauran zuba jari ya kai
kashi 3.91 bisa dari da kuma kashi
23.67 bisa dari na jimlar kudaden
da aka shigo dasu cikin Nijeriya.
Shigowar kudade na shiya a
zangon farko ya karu da kashi
3.05 bisa dari daga dala biliyan
3.68 da aka ruwaito a cikin zango
na hudu na shekarar 2017 zuwa
dala biliyan 3.79 a cikin zango na
daya na shekarar 2018.
Wannan ya sanya an samu kari
tun daga zangon farko na shekarar
2017, inda aka kara samu a cikin
zango daya na shekarar 2018, a
zaman zango na biyar.
Kashin hannayen jari da aka
zuba, ya karu daga kashi 68.37
bisa dari a zangon da ya gabata
zuwa kashi 60.17 bisa dari na
zangon farkon shekarar 2018.
A zangon farko na shekarar
2018, hada-hadar banki itace ke a
kan gaba wajen shigowar kudaden
kasar waje, inda hakan ya sanya
aka samu masu zuba jari da yawa.
A zangon na farko jarin da aka zuba na kasar waje ya kai biliyan
1.18, inda hakan ya kai kashi 18.7
bisa dari na jimlar kudin da aka
shigo dashi.

Zuba jarin da aka yi a bangaren
sadarwa shine na biyu wajen zuba
jari, inda aka samu zuba jarin da
ya kai dala miliyan 485.41.
Wannan ya biyo bayan dala
miliyan 328.15 na kayan da
masana’anta ta sarrafa inda ya kai
dala miliyan 144.09 akan aikin
noma inda aikin yake da dala
miliyan 130.90.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: