Connect with us

MAKALAR YAU

2018 ‘Yankasuwa Ga Ramadan Fa Ya Zo

Published

on

idrisdaudawaaliyu@gmail.com

Shekara kwana ce sannu sannu kuma bata hana zuwa sai dai a dan dade ba a je wurin da za a je ba, kwanci tashi sai ga shi cikin ikon Allah madaukakin Sarki mai kowa mai komai, ya sa mun ga watan Ramadan saboda gamu cikin shi, mun ma fara yin Azumin. Mutane da yawa sun samu damar yin Azumin shekarar data wuce, wasu ma sun samu labarin ganin wannan watan na shekarar da muke ciki, sai dai kuma Allah bai yarda , da sai sun yi Azumin ita wannan shekarar ba. Allah madaukakin Sarki shi ke da wannan ikon, shine kuma mai yin yadda yaso. Samun kasancewa cikin watan Ramadan babban fa’ida ce, kuma duk musulmi yana mai fatar Allah ya sa Azumin ko wacce shekara ya same shi, sai dai idan lokacin tafiya gidan gaskiya ya yi, bugu da kari kuma Azumi yana daga cikin shika shikan musulunci na uku daga cikin biyar. A watan Ramadan ne aka saukar da Alkur’ani mai girma wanda shine jagaba da ake amfani da shi, duk kuma dokokin rayuwar musulmai, suna ciki, yadda musulmain ya kamata su tafiyar da rayuwarsu, sai kuma Hadisan Manzon Allah Annabi Muhammadu Sallallahu alaihis wasallam, har ila yau cikin watan akwai daren Lailatul Kadari wanda yafi watannin dubu, duk musulmai suna fatar haduwar su ta samun haduwa da shi daren, wanda ake sa ran shi tsakanin ranakun 23, 25, 27, da kuma 29, Allah yasa mu dace amin.

Duk cikin wannan wata ana bukatar ko wanne musulmi yayi kokari ya samu damar yin wasu abubuwa na alkhairi wadanda, zasu kara kusantar da shi da samun rahamar Allah saboda ai dama wata ne na gafartawa, yafewa, rahamawa, da kuma jin kai .Wannan ba wani abin mamaki ba ne idan  aka ga yadda musulmai suke ta dauki ba dadi, domin ganin cewar basu bata lokacinsu ba, a wannan wata wanda sake ganin shi, sai wanda Allah ya nufarmawa. Lokaci ne bana kasala ba, sai dai idan da akwai wani babban dalili wanda yasa hakan. Wata dama ce wadda musulmai suka samu ta taimakawa junansu, ta hanyoyi masu yawa, in ba wannan akwai waccan, in ba dama akwai hagu, in ba gaba akwai baya, in ba gabas akwai yamma, sai dai idan mutum bai da niyyar taimakawa, wanda ba sai da wani babban abu ba, saboda ai kowa ya san cewar karamin goro ya fi babban dutse. Duk dai komai kuni kunin mutum bai rasa yin abin da zai sa ya  samu rahamar wannan wata mai alfarma ba.

Allahu akbar Allahu akbar walillahil hamdu wallahu akbar, subhanalillah walhamdu lillahi wala’ilaha illallahu wallahu akbar walahaula walakota illabillahil azim. Allahu akabar wani abin da zai daure ma mutane kai shine idan suka tuna idan lokacin yin bukukuwan abokan zamanmu ya kusa. ‘Yankasuwa masu irin  yin bikin nasu sai kaga sun fara rage farashin kayayyakin da su kasan, lallai ko shakka babu ‘yanuwan nasu na amfani dasu lokacin bukukuwan nasu, wani lokaci da zarar an shiga watan Nuwamba ko dai tsakiyarshi, ko kuma karshen shi, mutum zai ji suna ta labarin Bonanza ! Bonanza!! Bonanza!!! ta kafafen yad labarai inda wai lokaci zasu cire ko kashi 10, 20, 30, 40, kai wani lokacin ma suna cire kashi hamsain gaha cikin kashi dari na babban garabasar da suke yi, saboda mabiyan addinin da suma suke yi, ba domin komai ba sai saboda so da kaaunar junansu da suke yi wanda ko dai ba komai tasa sun rage masu farashin kayayyakin amfanin yau da kullun, sun nuna cewar sun san da ‘yanuwansu. Mu kuwa ‘yanuwan namu da zarar sun ga watan Ramadan ya kama, ko kuma kafin hakan, wato ina nufin ‘yanuwanmu musulmai ‘yan kasuwa, wasu daga cikinsu kara kudin farashin kayayyakin da suke sayarwa suke yi, wasu abubuwan da suka san dole ne sai an neme su lokacin Azumi, su kara masu kudi abin ma har wani lokacin shi al’amarin na wasu daga cikinsu, sai ya rika daure ma mutum kai, ya fara tunanin anya kuwa ’yanwannan namu suna son mu, kamar yadda yaga wasu su wadancan suke yi ma nasu , suna ta tarairayarsu, suyi nan dasu , suyi can dasu, suna tambayar su ko zamu taimaka maku ne? kamar ma zasu basu kyauta ne, idan har lokacin yayi. Idan mutum ya je kasuwa wani lokaci yana rasa ma, shin ina zai fara zuwa ne, inda yake tsammanin ko da akwai  wani dan sanyi sanyi, wato ko farashin kayayyakin da yake tsammanin ko sun yi kasa, amma ba kuma kasa kasan ta sosan da kowa ke tsammanin ba. Wanda ko wadanda suka dade da kayayyaki sun yi watanni tare da su, tare da wanda ko wadanda suka sawo nasu, ba wani abin mamaki bane, su sa farashin nasu ya kasance daya, saboda kuwa su dai, idan ma ka tambayesu, me yasa haka ne dangane da tashin farashin kayayyaki? amsar wasu daga cikin su ita ce, wallahi suma basu so hakan ba. Koda yake dai komai runtsi akwai wadanda idan kaji farashin nasu, sai ka ji ya sha bamban da na wadancan, masu nuna kamar kudade sun fi ‘yanuwa, saboda su suna son ‘yanuwansu, amma kuma anfi su yawa, ba yadda zasu yi, domin wani lokacin ma ana mayar dasu saniyar ware, badon komai ba, saboda sun nuna alamar suna tausayawa ‘yanuwansu musamman ma talakawa masu karamin karfi.

Idan mutum ya fara lekawa bangaren masu sayar da hatsi, zuwa masu sayar da kayayyakin miya, sayar da Atamfofi ko kuma nace da sauran kayayyakin kyale kyale na mata, haka abin zai tafi har zuwa Teloli, saboda shi al’amarin sai dai ace na wani yafi na wani wasu daga cikin suma suna kara kudin dinki, suna la’akari da sai dole an zo an same su . Kamar dai yadda wani mai waka marigayi Alhaji Sani Sabulu Kanoma ya fada a wakarshi, mai taken ‘’Harkar duniya babu dadi ba a shirin barin hakanan, kullun tafiya take, inda yace ya san Mamar sa da Baban sa, ana kwana a tashi Muhammadu ban gansu ba, duk wada naddade akwana tashi Muhammdau watarana  za a wayi gari ba a tare damu . Haka kuwa al’amarin yake watarana sai labari, amma ya dace idan mutane sun tuna da mutum bayan ya rasu, su rika cewar Allah Sarki ashe wane mutumin kirkinnan ya mutu Allah ya jikai nai, ba wai a rika cewar kai mun dai huta yau mun rabu alakakai. Duk wani zumudi da Unguwar zoma zata yi, ai  sai  ta bari tukunna sai an haihu, daganan idan da damar yanke cibin sai ta yanke, to amma ina son ta tuna cewar akwai lokacin da ake haihuwar wani jaririn da yankar cibiya, saboda ai komai sai da yardar Allah madaukakin Sarki yake kasancewa. Wasu ‘yankasuwa da suke karin farashin kayayyaki saboda suna ganin hakan shi  ne zai  sa su zarce ‘yanuwansu, sun manta ai ba anan take kadai ba, da aka danne Budari ta ka. Al’amarin na Allah ai tun ran gini ranar zane ne, saboda duk kowa kafin a haife shi an riga an rubuta ma shi, dukkan abubuwan da zasu kasance da shi a rayuwar shi, don hakan abin mukaddari ne ko kuma na ce ‘’Kaddara ta riga fata’’. Ba nuna wayo bane zai sa ku zarje  su ‘yanuwan naku, da kuke ganin suna saukakawa dangane da farashin kayayyakin har wani lokaci ma ku yi kokarin daukar matakin da bai kamata akan su hanyar da suke son bi. Kuma kan nu kun san, cewar ba dole bane sai sun bi hanyar taku, domin akwai bambanci tsakanin ku da kuma su. Kungiyar ‘yan kasuwa tun daga tarayya zuwa kananan, manya da kuma kananan  lokaci ya yi, wanda kuma da kanku ya dace, ku yi ma kanku fada, ba sai an yi maku ba. Kamar dai yadda na yi bayani saukakawa ‘yanuwa musulmai hakan shi zai sa Allah yasa albarka a al’amuran naku, ku tuna fa wannan wata ne da ake son  kowa ya dadadawa danuwan sa rai, ba a bata masu ba, wajen karin farashin da bai zama dole ba, saboda bai yin maganin kishirwar da ta dade tana damuwar, masu irin wannan dabi’a, su kuma tuna irinsu ai ba tun yau suka fara yin haka ba. Kamata ya yi suyi ko kuma kuyi tunannin shin g
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: