Connect with us

WA'AZIN KIRISTA

Wa’azin Kirista: Akwai Shari’a

Published

on

Wurin Karatu: Ibraniyawa 9:27

“Da shi kef a a kudurta ma mutane su mutu so daya, bayan wannan kuma sharia” (Ibraniyawa 9:27)

 

Babu cikaken Kiristan duniya guda da baya yi imani da ranar tashin alkiyama ba! Dukan Kiristan duniya sun yi imani sharia a ranar tashin mattatu. Matuwa da tashin mattatu kuduri ne ko kadaran Allah ne ga kowane irin Bil Adama.

Abinda ya tabbatar da imani Kiristan duniya shine yardan sad a ranan tashin mattatu. Kiristan duniya ya yarda Alkwai bada lissafi a ranan tashi mattatu baicin bada lissafi kuma akwai sharia! Kirista na gaskiya yayi imani da cewa baiyan sharia, akwai salkaiya a ranan tashin mattattu.

Maganan mutuwa da tashin mattatu ga kowane Kirista watau wata irin tunatarwa ne na musamma daga Ubangiji Allah. Wannan tunatarwan domin kowane Kiristan duniya ya kara imani da tsoron Allah har Kirista ya rege nau’in zunubi ga cikaken tuba.

Tunatarwa ne in an ambaci ranar tashin mattatu amma kuma rana ne da ido zai raina fata ga marasa imani. Amma ga masu imani ranan farin ciki ne da karban sakamako daga wurin ubangiji Allah.

Wannan ranan tashin mattatu babu tuba sai dai bada lissafi ,shari’a da karban sakamako. A ranan babu wanda zai tsaya wa wani, watan babu lawyer, ko uba ko uwa da zau kari yayansu. A wannan ranan duk kowane bayeyen abu zasu bayana kuma Allah zai sharanta su duka.

A wannan ranan ne za a tantance masu imani da kafirai, za a tantance tsakanin masu bin adddini na gaskiya da marasa gaskiya. A ranan ne imanin ka ya cehce ka. A ranar fa kudinka ko Iliminka ba zai taba cece ka ba!

A ranan tashin mattatu ne san da gaskiya da rashin gaskiya abayane. Mallaman da Pastocin gaskiya da na karaya, duk Allah zai bayanasu a bayane. Babu boyeye sai dai bayanawa Bil Adama duka gaskiya kuma ranan ne karshen karya da ma karyata. Abinda muke nufi a nan shine, watu a ranan tashin mattatu akwai tonan tsilili.

A ranan tashi mattatu ranar karshen munafincin munafukai, karyan makaryata, zaluncin azzalumai, makircin masu makirci, Hassadan ma hassada, Ha’inacin masu ha’inci, kafircin kafirai, muguntan mugaye, da kowane irin nau’in laifufuka ko zunubi zata kare.

Matuka wannan ranar ta bayana, to tabbas duk masu imani za su sami cikaken yancinsu daga hannun azzahumai da masu mulkin danniya. Karshen rashin adalci ne da kuma karshen mulkin kamakarya da firananci. A ranan ne za a tabbatar wa mai gaskiya da aka zalunta za’a tabbatar ma shi da gaskiyarsa.

Masu sharian karyan zasu tarar da mai sharian gaskiya a ranan tashin mattatu. A ranan ba sai an tambayi mutum laifufu kansu kafin su yi Magana. Wannan ranar wata rana ne na ban mamaki, ranan juyayi ranan kuka, ranan farin ciki, ranan bakin ciki kai wannan ranan daidaita sawo ne!

Ranan, ranar adalci ne da yancin ga masu imani. A ranan ne, Ubangiji Allah zai kawo komai da ke aboye a bayane domin karya ta shude gaskiya kuma ta bayana. A ranan wasu zasu nemi hanayan tuba amma lokaci ta rigaya ta kure. A ranan ne masu neman santawa da juna zasu so suyi amma ba zai yiwu ba. Duk wadanan kokarin ba zata yiwu ba, domin ba a tuba a ranan tashin mattatu ko kiyama sai sharian Allah da hukucinsa.

Imaninka shine tsiranka a ranan tashin mattatu amma ga, marasa imani cikin Yesu Almasihu to ranar hunkunci da makomarsu shine Jahannama. Mafitan shine imani ga mutuwa da tashiwan Yesu Almasihu daga mattatu, da imani cewa ya mutu ne domin ya bada ransa domin duka wadanda suka yi imani da mutuwarsa da tashiwansa daga mattatu domin fansa zunuban mu. Littafin maitsarki na cewa:

“Akwai wata hanya wadda ta ked a alamar kirki ga mutum Amma matu katta tafarkun mutuwa ce! (Misalai 16:25)

To abin tambaya a nan wane irin hanya ne da kai ko ked a aka dauka? Wandansu addinin da suka dauka shine hanyar da suke tsamani hanya ce da ked a alamar kirki ga muhum amma matukatta tafarkun mutuwa ce. Allah ya rabamu da shigan addinin dab a zata kai mu ga ceto ba, amin. Allah ubangiji ya rabamu da kowane irin hanyan da muka dauka dab a zata kai mu ga tsira ba, amin. Yah Allah! Ka nuna mana hanyar da zata kaimu ga samin rain a har abada abadin amin.

Yah Allah ka yafe ma kura kurenmu da zunubanmu ka kuma yimana jinkai da rahamar ka.

Yah Allah, ka tabbatar mana da A’ljanarmu tawurin imaninmu ka kuma daidaita mana imaninmu domin mu cika da imani, amin thumma amin!

Shalom! Shalom!!
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: