Connect with us

LABARAI

Ramadan: Wakilin Birnin Bauchi Ya Taka Rawa Wajen Inganta Rayuwar Jama’a –Ago

Published

on

An bayyana cewar yunkuri da kuma irin jajircewar Dan Majalisar cikin Bauchi a Majalisar Dokoki Ta Jihar Bauchi wato Honorabul Yakubu Shehu (Wakilin Birnin Bauchi) a matsayin wani yunkurin da ke kawo gagarumar ci gaba wa talakawan jihar Bauchi.

Ibrahim Gambo Kobi wanda aka fi sani da Ibrahim Ago shine ya shaida hakan a lokacin da ke hira da manema labaru kan rabon kayyakin Azumi ga mabukata a jihar Bauchi.

Ibrahim ya ci gaba da bayyana cewar samuwar irinsu Honorabul Yakubu Shehu a cikin gwamnatin APC gagarumar ci gaba ne domin kyakkyawar manufarsu na tallafa wa talakawa.

Tun da fari ma, ya fara ne da bayyana irin kokarin da gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya yi wajen rabon kayyakin Azumi ga talakawan jihar, “Mai girma gwamnan jihar Bauchi ya yi kokari kan rabon kayyakin Azumi a wannan shekarar, domin yanzu haka ana kan rabon nan kuma ana ci gaba. A wannan shekarar hatta massalatan da basu cikin jerin jadawalin wadanda ake basu a shekarun baya a wannan shekarar an sanya su kuma sun samu kayyakin Azumi. Don haka gwamnati ta yi kokari, kuma ana raba kayyakin nan bisa adalci, domin kungoyoyi, massalatai da kuma bangarori duk gwamnati ta yi rabonta bisa cancanta, sai godiya,” In ji sa.

Ya ci gaba da bayanin cewar baya ga gwamnatin jihar, Dan Majalisar cikin gari Yakubu Shehu Abdullahi (Wakilin Birni Bauchi) shi ma ya taka rawa sosai wajen faranta wa masu bukata a cikin wannan watan mai alfarma, “Irin gudunmawar da yake bayar wa jama’an jihar Bauchi ya fi karfin dan majalisar yankinsa, shi dan majalisar dukka kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi domin babu wata karamar hukumar da alkairinsa bata ratsawa. Taimako ta massalaci ne, masu bukata na musamman idan ka je gidansa ka ga mabukatan da yake taimaka musu sai ka yaba masa. Da irinsu za su yi tururuwa a cikin gwamnatin APC da ba za ta taba jin wani korafi ba, domin suna gudanar da aiki bil-hakki domin talawansu,” Kamar yadda ya shaida.

Ibrahim Gambo Kobi ya ci gaba da bayanin cewar a rabon kayyakin Azumi da wannan dan majalisar ya yi sai dai Allah sambarka, domin ya tabuka abun a zo a gani, “Shi ma kansa ya yi rabon kayyakin Azumi wa mabukata kuma yana kai ma a halin yanzu. Shi fa tallafinsa a Azumi ne da ba Azumi ba taimakon talakawa yake yi. Domin burinsa na taimaka wa talakawa ne ma ya sanya ya kafa gidan yin shinkafa domin tallafa wa marasa shi. Don haka muna wannan bawan Allah ya gaji alheri,” In ji Ibrahim.

Da ya juya kan tsokaci dangane da halin da jam’iyyar APC take ciki a jihar Bauchi, Ibrahim Gambo ya bayyana cewar bayan zaben APC abun da ya wajaba a kan gwamnan jihar Bauchi shine ya jawo kowa da kowa jikinsa domin su samu nasarar dawo da gwamnati a 2019, yana mai bayanin cewar ba daidai ba ne gwamnati take rasa wasu daga cikin ‘ya’yanta a sakamakon wasu ababen son rai ko son zuciya na wasu.

“Zaben APC a jihar Bauchi ba za mu ce ba a yi ba, ba kuma za mu ce gwamnatin jihar ta kyauta ko bata kyauta ba. Amma abun da muke jawo hankalin gwamnatin jiha a kansu su ne, wadanda aka karbi kujerunsu aka baiwa wa wasu a bisa cewar da gwamnati ta yi na sun yi laifi, ya kamata gwamnati ta jawosu a ciki ta sauraresu ta dauki wani mukami ko wani abu ta basu domin su ma fa suna da magoya baya.

“Kada ya kasance gwamnati tana rasa mutanenta, domin idan gwamnati ta rasa mutum daya yau, gobe ta rasa to wata rana zata rasa kanta gaba daya. Mu bamu fatan gwamnatin da muke ciki ta fadi, fatanmu APC ta samu nasara a zaben 2019, don haka dole ne gwamna ya yi karatun ta nutsu ya jawo wadanda suka sauyasu,” In ji Ibrahim Ago.

Ya bayyana cewar ko a cikin rikita-rikitan da aka yi ta samun a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC, ya bayyana cewar Yakubu Shehu ya taka rawa wajen daidaita matsalolin da kuma masu matsalar domin nasarar APC.

Ya kara cewa, “Wasu ‘yan kama waje zauna ne, wadanda ko wahalar da aka sha wa APC babu su, sune suke neman cewa su yi ne da yawun gwamna. Alhali ina da imanin wasu abubuwan suna yi ne a bisa son ransu, don na sani gwamna ba zai taba amincewa da wata harkalla ta rashin gaskiya ba. Wasu ne masu bukata nasu na kashin kai suke yi domin ganin sun nasara a abun da suke so,”

Ya  bayyana cewar sam bai kamata wadanda suka yi hidima wa jam’iyyar a tun farko kuma a karshe a yasar da su ba, “Mu fatanmu duk wanda aka san an bata masa, walau dan APC ne ko ba dan APC ba a jawosa a tafi da shi domin mu burinmu a kawo gwamnati ne ba gwamnati ta sha kasa ba. Don haka ne muke kira ga gwamna da ya jawo irinsu Wakilin Birnin Bauchi kusa da shi domin tafiya da su a bisa harkar gudanar da mulki domin su mutane masu son ci gaban jihar Bauchi da talawan Bauchi,” Kamar yadda ya bayyana.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: