George Simmel Da Falsafar Kudi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

George Simmel Da Falsafar Kudi

Published

on


Kaifin basira da tunanin George Simmel sun fito karara ne a nazarinsa na falsafar kudi ‘Philosophy of Money’, wanda a wasu lokutan a ke kira da ‘Sociology of Money’. Wannan kuma na daga cikin ayyukan da suka bayyana kimar Simmel a kan shiga fagen rubuce – rubuce kan mu’amalar tsakanin daidaikun mutane ‘Micro-Sociology’, a maimakon bayanin gabadaya al’umma ‘Macro-Sociology’.

Duk da a wannan nazariyyar ta Simmel, mafi muhimmanci shi ne yadda ya mayar da hankali a kan kudi; domin fahimtar irin hatsabibanci, da kuma yanayin yadda kudin ke iko da rayuwar al’umma ta yau da gobe. Masanin ya yi kokarin yin bayanin kima, wanda ya ce a na iya fahimtar kima ta yanayin mu’amalar mutane da kudi.

A wata fuskar, ina iya cewa ba wai Simmel ya damu ba ne da yin bayani kacokaf a kan kudi; a’a, sai dai damuwarsa ta fi rinjaya ga tasirin kudin ga rayuwarmu, da kuma yadda a ke mu’amala da kudi a duniya, har ya zama wani tsayayyen al’ada. Haka kuma ya kalli kudi ta fuskar cinikayya, hakkin mallaka, kyashi, rowa, almubazaranci, ‘yanci, yanayin rayuwa, da sauransu. Za mu iya kallon nazariyyar falsafar kudi a bangaren da ya yi bayanin yadda kudi ke taimakawa dan Adam wurin sanin rayuwa da daidaita rayuwa ta ingantacciyar hanya.

Falsafar kudi na da alaka makusanciya da wasu bangarorin ayyukan Karl Mard, duk da cewa a wasu wuraren an samu sabani tsakanin masani Simmel da Mard. Kamar dai Mard, a wannan nazarin Simmel ya zargi jari hujja da irin matsalolin da mayar da tattalin arziki da cinikayya ta siffar kudi ya haifar ga al’umma.

Ni ma a nan na yarda da batun Simmel, da ya ke cewa mutane su ne su ke samar da kima ta hanyar abubuwan da su ke samarwa ko kirkira. Sai su muhimmantar da wannan abubuwan da suka samar da kimar da ba kowa ke iya mallakarsu ba, ta yadda za a fara rige – rige a tsakani, kowa na son ya zama ya mallaki wannan abu mai kima.

Wannan dabi’a ce ta mutum, idan abu ya zama ya na yi mishi wahalan samu, kimar wannan abin ya fi girmama a wurinsa. Kenan za mu iya cewa mutum ne ya kirkiri kudi, ya basu kima mai girman gaske da daraja, sai kuma ya sa mallakar kudin shi ma ya zama wani gagarumin abu wanda sai an wahala a ke iya samu.

Ka kwatanta da kanka, kuma ka yi nazarin abubuwan da ke tare da kai, wasu abubuwan masu muhimanci ne, kuma masu amfani, amma sakamakon mu na iya samunsu cikin sauki, sai ya zama kimarsu ba ta taka kara ta karya ba a wurinmu. Saboda mu ne ke kimanta kiman ai.

Ba wannan kadai, akwai wata sabuwa a nan. Falsafar kudi ta zo da cewa abubuwan da tunaninmu ba zai iya cim musu ba, wanda komi kokarinmu ba zai yiwu mu samu ba, su ma ba za su zama masu kima ba a wurinmu. Su abubuwan da mu ke kimantawa su ne wadannan da a tunaninmu kullum mu na sa ran idan mun kokarta, mun yi hakuri da wahalhalu zai yiwu mu same su. Amma kuma ba zai yiwu mu same su a cikin ruwan sanyi ba, to wadannan su ne abubuwan da mu ke gani da kima.

Daga cikin abubuwan lura da a ke la’akari da su wurin gane abu mai kima har da tsawon lokacin da zai ci mana kafin mu same shi, karancinshi a cikin al’umma, wahalar mallakarshi, da kuma yiwuwar sai ka sadaukar da wasu abubuwan kafin ka same shi. wannan shi ne misalin kudi ga me nemanshi, kamar yadda ya zo a nazariyyar falsafar kudi.

Abin da na ke ta son bayyanawa a wanchan dogon bayanin shi ne, kudi ne ke shiga tsakaninmu da duk wasu abubuwan mallaka, na kayan masarufi, tattalin arziki, da sauransu. Idan mu ka samu kudin kuma, sai ya zama mu na iya mallakan wasu daga cikin wadanchan abubuwan, a maimakon mu samu natsuwa da iya wadanda mu ke iya mallaka, sai kuma mu shiga neman karin wasu kudin domin son mallakar wasu abubuwan fiye da wanda mu ke da su. A nan kenan, zan iya cewa ‘yan jari hujja sun kakaba mana kudi, ya zama wani abu me iko da rayuwrmu, kuma mai daidaita mu’amalar da za mu yi a tsakaninmu.

Duk al’ummar da kudi ya samu wanchan kimar da na ke kwatantawa, shi kenan, sai kuma abin da Allah ya yi, amma fa za a ga matsaloli. A irin wannan al’umma, kamar kasarmu Nijeriya da ta ke kwaikwayon yanayin rayuwa irin ta ‘yan jari hujja, KOMI na siyarwa ne.

A kasarmu, da kudi ka na iya siyan kyau, ka siyi gaskiya, ka siyi kaifin basira, kamar yadda za ka je kasuwa ka yi ciniki ka siyo albasa, turare, da sauransu. Wannan irin muguwar kimar da rayuwar mutum ke ba kudi ne ya sa komi da kudinshi, kuma komi a na iya cinikinsa a siye shi a kasuwa. Kudi sun sa ba mu iya bambancewa tsakanin hakikanin gaskiya da kuma hakikanin karya.

A takaicen takaitawa, kudi sun sa hatta mu’amalar da ke tsakaninmu ta tashi daga ta mutum da mutum. a maimakon mu yi mu’amala a tsakanin Musa da Ezekiel, mun koma yin mu’amalar tsakaninka da mai sharan gida, mai gadi, mai kabu – kabu, mai gyaran fulawa, mai shago, mai wanki da guga, mai dinki, shugaban ma’aikata, darakta, edita da sauransu. Saboda duk wadannan wasu matakai ne na kudi, wanda ke kasanmu a wurinmu ya ke samun kudi, wanda ke samanmu kuma a wurinshi mu ke samun kudi

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!