Duk Da An Haramta Zub Da Ciki, Annobar Na Karuwa A Nijeriya Da Ghana –Bincike — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Duk Da An Haramta Zub Da Ciki, Annobar Na Karuwa A Nijeriya Da Ghana –Bincike

Published

on


Lokacin dokokin zubar da ciki a Nijeriya suna wadanda ake ganin suke da tsaurara a duniya, kasar har ila yau ita ce ta daya daga cikin kasashe, wadanda ‘yan kasarsu ke neman maganin da  za asha domin zubar da ciki, kamar dai yadda wani bincike ya bayyana.

Kasasshen Ghana da Nijeriya sune kasashen biyu wadanda suke a gaba wajen neman wani maganin zubar da ciki, mai suna Misoprostol,  wanda maganin zubar da ciki ne kamar dai yadda rahotannin rediyon BBC suka bayyana.

Kamar yadda ita BBC ta bayyana alkalumman  kasashen wadanda suke neman maganin zubar da ciki ruwa a jallo, an samo bayanan ne daga Google.

Misprostol wani magani ne wanda yanzu shi aka fi amfani da shi, saboda  a samu damar zubar da ciki, shi maganin kamar yadda aka yi bayani akan shi, akwai samun kashi 95 na sa’ar zubar da jiki, wanda bai wuce kwana hamsin ba da shigar shi cikin.

‘’Yadda ake amfani da Misoprostol’’ ‘’Farashin  Misoprostol’’  ‘’A sayi Misoprostol’’ ‘’Yadda za ayi amfami da shi maganin’’ na cikin abubuwan da za a rika dubawa duk saboda a san yadda z a zubar da ciki, kamar dai yadda wannan binciken da ka yi ya nuna.

Shi sabon binciken da ka yi ya sa an nuna sahihancin hana amfani da hana zubar da ciki, a kasa kamar Nijeriya.

Daga cikin kasashe 25 da suke da sha’awar neman Misoprostol, goma sha daya suna nahiyar Afirka ne, sai kuma goma sha hudu suna Latin America.

Shi wannan binciken na BBC ya nuna cewar su kasashen dfa suke da tsattsauraran dokoki, wurin da aka bada damar acecei rayuwar ita matar da take da ciki, ko kuma a hana gaba daya, suna da dubawa wadda tafi hakan sau goma, akwai kuma dubawar tafi sau goma, na nuna sha’awa akan maganin zubar da ciki, ‘’Misopprostol’’ idan aka hada da kasashen da basu dauki wasu tsauraran matakai ba.

Idan ana sayen magani ta yanar gizo da kuma aikawa da shawarar al’amarin daya shafi lafiya, ta hanyar kungiyoyi daban daban na Whats App, mata suna kara amafani da fasahar zamani, su nemi samu wani ba’asi wanda  ke alaa da bangaren sharai’a.

Yayin da a kasar Ghana zubar da ciki doka ce, amma sai dai maganar fyade ta taso, maganar idan har cikin ya fara kankamwa, amma ita dokar zubar da ciki a Nijeriya tana da zauri, ana iya bada damar zubar da ciki a Nijeriya ne, idan aka yi la’akari da rayuwar ita matar da take da cikin tana cikin hadari.

Zubar da ciki wani abu ne wanda yake da rudadwa da kuma daure kai,a Nijeriya, amma akwai dokoki wadanda suka sha bam ban da juna, wannann kum ay danganta ne daga sashen da ake. A Arewacin Nijeriya dokar it ace ta Penal code, ita kuma ta Kudancin Nijeriya dokar ana kiranta Criminal code. Doka wadda take ita hanya da za a iya zubar da ciki a Nijeriya, ita ce ‘’Idan haihuwar zai iya sa ita mahaifiyar cikin matsala’’.

Sai kuma dokar zubar da ciki ta Criminal Code an  bayanin ta  cikin sassa 228, 229, 230, sashi na 228 ya bayyana cewar duk mutumin da ya taimaka aka zubar da ciki,(yadda ake kira al’amarin da ya shafi zubar da ciki) ga mace wadda ta aikata laifi na cin amanar kasa, zata yi shekara 14 a gidan fursuna. Sashi na 229 ya bayyana cewar duk matar data nemi ta zubar da ciki, ta aikata babban laifi, za kuma tayi shekaru bakwai  a gidan kurkuku.

Duk da yake an hana amma duk da hgaka bioncike wanda kasar Amurka ta gabatar, aka kuma yi a a cibiyar Guttmatacher, tare da taimakon Jami’ar Ibadan (UI) ya nuna cewar fiye ana zubar da ciki fiye da milyan 1. 25 ko wacce shekara  a Nijeriya.

Yawancin hanyoyin da ake bi ana yin su ne cikin sirri wadanda kuma ba kwararru bane suke yin hakan, sai dai masu kula da haihuwa na gargajiya  da kuma masu ayar da maganin gargajiya.

Hukumar bincike al’amaran magungunan Zamani (NIMR) ta bayyana yawan mutuwar da ake yi  a kokarin zubar da cikin da ake yi, ta hanyar da bata dace ba a Nijeriya, abin ya kai ga 34,000, wannan kuma ya bada gudunmawa akan mutuwar kashi 13  da kuma kashi  15 na matan da sukemutuwa lokacin haihuwa, da kuma kananan yara da suke mutuwa, wadanda basu kai shekaru biyar ba.

Gaba daya  a duniya mata 22,800 suna mutuwa ko wacce shekara saboda matsalar da aka samu dangane da zubar da ciki, wand aba ayi shi daidai ba, wato yadda ya dace, haka dai ita cibiyar Guttmacher ta bayyana  arahoton ta.

Idan aka zubar da ciki ba yadda ya dace ba, su jami’an lafiya suna iya bada shawarar ko dai a sake daukar matakin asbiti, na ko dai ayi tiyata, wannan kuma ya danganta ne akan irin halin da take cki.

Kamar dai yadda kwararru suka bayyana zubar da ciki  bai yi ba, lokacin da aka bari wanda bai san yadda ake yin shi al’amarin ba, ko kuma lokacin da ka yi shi, wurin da babu isassun kayayyakin yin hakan, amma duk da hakan a kasar Nijeriya laifi ne a yi maganar zubar da ciki ba, ba tare da na samo wasu magunguna ba kamar Misoprostol.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!